Bamisriya Ta Page 1

BAMISRIYA TA Da akwai wani lokaci, ni da abokai na da yake an bamu hutu a makaranta, muka yanke shawarar mu tafi yawon shakatawa, izuwa Askandariya wace aka fi Sani da Alakzandiriya a asar Masar. . Saboda haka, muka nufi tashar jirgi kasa ta Ramsis a nan Alahira wato masar kenn, muna isa ba tare da bata lokaci ba suka je muka siyi tikitai sann muka nemi guri muka zauna muna dakon jirgin da zai dauke mu da karfe *8:00 am.* . Kasancewar munyi sammako saboda muna son muje a ranar, kana mu dawo Alhira a ranar. . Ko karin kumallo ma bamuyi ba, yayin da muka tsaya muna dakon jirgin ne, muka yanke shawarar ya kamata munemi wani abu mu saka a bakin salatin mu. . "Toh, jama'a wai madadin mutsaya muna jiran isowar wannan jirgin, mai zai haba munemi wani abu musaka a bakunan mu mana?" ya cigaba da cewa "Ni ciki na sai fadin eyyyane yakefa ko baku gane bane" a cewar daya daga cikin abokanai na mai suna Yusif Sani. . Ba karamar dariya maganar tashi ta bani ba, nace ni matsalata dakai baka jurar yunwa wlh. Nan Kamala ya sako baki shima yace "To ina gwanin ta a jurar yunwa dallah mu nemi abinda xamuci kaji ko shedanma baya jurar yunwa wlh" nan dai mukasa dariya gaba dayan mu. . Hizbullah da tun dazu yayi kasake yana jinmu shima ya kada baki yace "Kai kamala a ina kuka taba fira da shedan din yace maka baya jurar yunwa, waya fada maka shedan na cin abinci, wai kai waya fada maka shedan na cin abinci ma? nan dai suka kaure da gardama nikuwa nayi shiru ina sauraron su. Kasancewar naji jikina yayi mani wani iri tamkar bani da lafiya. . Toh muna cikin wannan raha ne sai kawai na daga kaina, ina daga kannawa ne, mai zan gani? sai kawai idanuna suka ci karo dawata Bamisiriya, Budurwa mai matukar kyan gaske. . Nan take zuciyata tace hmmmm, na kare mata kallo yayin dana ganta tana zaune tana karanta wani littafi, nace inama a ce nine wannan littafin data rike tana karantawa ina kara mata ilimi ina bata nishadi. . Na fara nisa ciki chakwalkwalin mafarkin zaune na kenan, sai kawai naji kamala ya ture mani kafada yace "Kai dallah Malam a nata yi maka magana ko tunanin ma me kake oho?". . Nan da nan Yusif yataso mashi yace " Kai dallah malam ka rabu dashi haba kasan abunda yake damunsa ne". . Nan kamala yace ”Kai malam wlh sai ya raba mana wannan musun da mukeyi", nidai bance komai ba sai binsu sa ido da nake. . Sai kamala yace dani "Kanaji ba", nace ehh inaji yace "Da dadin dakake ji bayan cikin ka yayi muguwar kullewa kagane? kullewa iya kullewa, kawai ka samu ka saki tusa fuuuurrrrrrr" nan mukasa dariya. Ya ci gaba da cewa "Ko kuma irin fitsari ya matsoka, na fitar hankali kawai ka shige bandaki a guje kana zuwa kawai sai ka saki fitsari shhhhhaaaaaa. Kaga ne wai a cikin biyun nan wanne ne idan kana yinsa zaka samu sa'ida idan kana yinsa zakaji nishadi hankalin ka ya kwanta" hakika wannan tambaya ba karamin bamu dariya tayi ba, saboda haka muka kece da dariya, sai da mukayi mai isar mu sannan muka yi shiru. . Hizbullahi yace "Kai fa ka mai da abun nan musu, tambayata kayi na fada maka ra'ayina, kuma kazo kace musu muke wai wanda ka fada shine dai-dai wanda nafada ba daidai ba ne, ai ba musu muke ba ra'ayina ka tambaye ni na fada maka". . Hankali na kwata-kwata baya tare dasu yayin da na juya na cigaba da kallon wannan Bamisiriya zuciyata ta ci gaba da bugawa kamar takawar kofaton dokin sarki yayin daya fito yawon shakatawa. . Wannan Bamisiriya tana zaune ko daga kanta bata yi bare ma ta kalli wani, ni kuma na kura mata na mujiya sai kallonta nake ina tunani a zuciya ta, nake tunani ko itama Iskandariyar zata je itama ko ina ne zata ne itama bansani ba? . Nan take, na afka duniyar tunani nagani kusa da ita muna fira sai bata dariya nake, a cikin jirginan tana ta kyalkyalewa. Kawai sai tunani na ya katse yayin da naga wani yazo yana mata magana, kuma ya dauki kudi ya bata, sai na kara maida hankalina sosai a gunsu, sai naga ta tashi ta tafi ta nufi wata na'ura, na'urar kuma ta sa'ida shayin sayarwa ce. . Take na gane ashe wannan yarinya Bamisiriya mai siyar da shayi ce, a lokacin kuma sai naji ta kara aji takara burgeni kasancewarta yarinya budurwa mai kyau kuma Bamisiriya amman tana siyar da shayi a tashar jirgin kasa. . Abokaina ma sun manta da maganar abinci sunata faman gardamar su, kawai sai sukaji nace musu nifa kawai shayi zan shaaa, cike da matukar mamaki suka juyo suna kallona, amman ba wanda yace dani kala, sai abokina Hizbullah yay karfin hali yace "Shayi kuma? shayi zai kosar dakai ne malam in zaka nemi giredin abinci kanema kawai ka sankama kagane koh? ba abinda shayi zai ma", nace malam ni kawai shayi zan sha period. Ra'ayi riga, sai kawai suka tashi suka barni a gurin, na mike tsaye da niyar in je wajenta sai kawai naji gabana ya fadi, kafafuna sunyi sanyi, naji kamar an daddaure ni gashi ban dade da zuwa ba larabcina bai nuna ba suma gashi suma basu iya turanci ba, bare hausa amman lamirina baya bani in je ko kar naje? nan take sai na ga duhu kawai sai na ganni a gabanta ban san ya akayi naje wajenta ba kuma ban iya tunawa ba lokacin da nake zuwa wajenta ba. . Gani a gabanta inata kallon ta na kasa. magana kawai sai ta dago takalleni sai tace "ice za ha ga" . . . Muje zuwa.......... . . . . Abubakar Saleh Quyraemey . {Young Writer} Ku ajiye comments

Post a Comment

0 Comments