(Hausa Novel) Wace ce Ni? By Aminah Abubakar, Page 1-5

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
                  _*WACE CE NI?*_πŸ™†πŸ»
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺



*_ZAMANI WRITERS ASSOCIATION_*πŸ–Š
_________________________________
_We are here to educate, motivate, and  entertain our readers_
__________________________________


                    *By*
🌺 *Aminah Abubakar*🌺
      🌺(Ι±Ι›Ι›Ι³Ι‘uwΙ‘Κ†)🌺


 ~*Dedicated to*~
Maman Aysar Yola




*Page 1⏩5*




Wata mata ce ta fito daga wani daki dake kama dana mahaukata ta na huci ta ce

"Ke Sabriyya dan kaza kazan ubanki me kikeyi a wajen nan? na rantse da Allah idan baki tashi kinzo kin tattara wanke wanken nan ba saina sumar dake a wajen shegiya maras hali kawai, kin tashi ko kuwa?" A hankali yarinyar dake zaunen ta mike tana faman tare hawayen dake shirin gangaro mata ta nufi mawankin don gabatar da aikin daya zamar mata farilla.


Wanke wanken takeyi lokaci zuwa lokaci tana sharce hawayen dake zuba a idanun ta, ji tayi an dafa kafadar ta a sanyaye ta juya ganin wacce ta dafa tan ne yasa ta dan saki murmushi sannan ta dan saci kallon kofar dakin Inna Jummai gudun kada ta hango su tazo ta kaddamar mata da rashin mutunci. Cike da tausayi Rahma take kallon ta ta ce "Kiyi hakuri da halin Inna don Allah kada kisa a ranki komai yayi farko yana da karshe.Sabriyya duk da cewar mahaifiya tace inna amma sam bana jin dadin abinda take yi miki.amma ki kara hakuri kada ki rike ta a zuciyar ki kinji Sabriyya?" Ta karasa maganar cikin sanyin murya da d'an hawaye dake makale a idanun ta.


Bata damu da goge kwallar dake faman gangaro mata ba kuma bata daina wanke wanken ba ta ce "Kakki damu Rahmu ai dama aikin gida dole ne ga mace ni hakan ma dadi yake min. sai dai sam bana jin dadin irin zagin da Inna kemin koda ace iyaye na mahaukata ne ko kuma ta hanyar banza suka same ni dole ina sonsu Rahma bazan taba jin dadi ba idan aka zaga min su ba. Amma sam Inna ta kasa gane hakan." Ta karasa maganar tana cusa kanta tsakanin cinyoyin ta.


Sosai take bama Rahma tausayi sai dai babu yadda ta'iya da Inna Jummai sam bata saurara ma yarinyar ko tausayin ta a matsayin ta na marainiya bata yi. Tana tsaka da wannan tunanin ne sukaji salatin Inna Jummai da fitowar ta daga bayan gida kenan da buta a hannu. ta ce  "Wai uwar me kikeyi ne a gurin nan Rahama bana son iskanci fa kinzo kin tasa ta a gaba hudubar me kike mata? Kin bace daga wajen ne ko sai nazo na doddoke ki awajen."


Da sauri Rahama ta tashi tana faman baiwa mahaifiyar tata hakuri saboda sanin hali. tasan ba karamin aikinta bane tazo ta buge tan. Dakin kwanan su ta wuce kai tsaye, ta labe tana leken Sabriyyan dake wanke wanken. har ta gama tsab ta tattara wajen ta share shi tass ta kuma jawo ruwa a rijiya ta shiga wanka, bayan fitowar tane taga baban nasu ya dawo yana zaune akan tabarma. D'an duqawa tayi cike da ladabi ta mishi sannu da zuwa sosai ya sake fuska ya amsa mata fuskar shi cike da annuri. Wani uban harara Inna Jummai ke binta dashi. Ita kuwa bata ma sani ba ta wuce daki abinta.


Baba yana hankalce da irin kallon da take bin yarinyar dashi yayi gyaran murya ya ce "Ayya ayya Jummalo ashe ba zaki sassauta ma zuciyar ki akan yarinyar nan ba. shin wai me ta tare miki? bafa ayima yaro abu ya manta wallahi" tsaki ta buga tana hararan shi ta ce "To idan ka gaji da ganin hakan ka nemo yadda iyayen ta suke mana ka damka musu abinsu. ni nagaji kuma wallahi matukar yarinyar nan tana gidan ba dai Rahma ta samu miji ba, yarinya kamar wata aljana sai uban kyau da farin jini kamar bala'i mtswww ni dai wallahi kasan nayi." Jin haukan nata yayi yawa yasa baice da'ita komai ba ya cigaba da abinda yake yi.


Wani yaron da bazai wuce shekaru takwas bane ya shigo ya ce "Assalamu alaikum wai ana kiran Sabriyya a waje." Kamar dama zaman jira Inna Jummai keyi tayi caraf ta amshe da cewa "Kace bata nan." Baba dake zaune a wajen ya ce "Kai yaro kace tana zuwa ko." Yaron ya ce "to Baba" ya fita yana tsalle tsallen shi, a fakaice Inna Jummai ta zabga mishi wani uban harara. Sarai ya ganta saboda shi din ba mai son tashin hankali bane yasa ya kau da kai. Kira ya shiga kwalla mata, tana daga cikin dakin ta amsa shi sannan ta fito cikin nutsuwa ta duke nan gaban shi ta ce "Baba gani" cike da kulawa ya dube ta ya ce "Kina da bako a waje maza tashi kije ko."


Ba don ranta yaso ba sai don bata son mishi musu yasa ta amsa mishi da "to" sannan ta tashi zata bar wajen "Iskancin banza da hofi ayi dai mu gani." Inna Jummai ta fada. Da ido Baba ya mata alama akan tayi wucewar ta tabar wajen haka kuwa ta wuce ta koma dakin su ta samu Rahma. Jin yadda sukayi da kuma ganin halin da ta shiga yasa Rahma ta dafa kafadar ta ta ce "Kiyi hakuri da halin Inna don Allah." Da sauri ta juyo ta fuskance ta ta ce "Nooo Rahmu ba wannan ke damu na ba wallahi ni bana son zuwa hiran nan ne yanzu haka Umar ne kuma kin san ba wai son shi nakeyi ba." Jinjina kai Rahman tayi ta ce "Gaskiya ne wannan, amma ko don Baba ki daure ki fita kada Inna tayi mishi dariya. shi kuma Umar kada ki kuskura ki nuna mishi kiyayyar ki a fili kin san shi ba hankali ne dashi ba komai zai iya faruwa." Gyada mata kai tayi alamar taji sannan ta goge guntun hawayen daya gangaro mata ta dauki mayafin ta.


A Sanyaye ta fito kofar gidan ta same shi zaune yana zaman jiran ta a hankali tayi mishi sallama da sassanyar muryar ta mai kama dana rigima amma a zahiri kuma ba hakan bane halittar muryar tata ce haka. Washe baki Umar yayi a madadin ya amsa sallamar kawai sai ya ce "Ahh hajiya Sabariya an fito?" da kyar ta danne bacin ranta ta ce "Eh ina yini?"


 "Lafiya lau. ya gari ya gararin gari ya neman gari acikin gari? Oh ashe muke neman gari ku kam sai dai diban ruwa a cikin gari hhhhh." Ya baiwa kanshi amsa wannan wani gaisuwa ne na mahaukata a zuciyar ta ta furta hakan, wani tukukin bacin rai ne ya tokare mata wuya amma ta danne saboda tsoron halin sa tayi murmushi ta ce "Zan shiga ciki Inna Jummai ta sani aiki inaso in kammala sai anjimah" a hasale ya mike tsaye yana mata wani banzan kallo ya ce

 "Keee nine zaki nunawa zaki shiga ciki kiyi aiki don ba mutunci ne dake ba? Ke kin san waye ni da har zan tako kofar gidan ku kizo kina nuna min bakida lokaci?"


A tsorace take kallon shi yadda yake maganar yana mokada gefen baki irin na cikakkun yan daba din nan. Cike da tsananin tsoro ta ce "Kayi hakuri Umar banida mafita ne daya wuce hakan." Fusata ya kuma yi ya daka mata tsawa "Ke dalla yimin shiru don ma za'a rufa miki asiri a aure kin? bacin nima wa zai yarda ko hanya ku hada maras asali. to wannan kyawu da suffar taki ta daina rudin ki tsintacciyar mage kawai. bace min da gani kona babballaki naga gatan ki a duniyar nan Saura kuma idan anjima nazo kada ki fito wallahi har cikin gidan zan shigo na fiddoki."


Da sauri ta ce "Kayi hakuri zan fito." Baibi ta kanta ba yayi wucewar sa ya barta a wajen. A sadade ta zauna akan dakalin kofar gidan tana wani irin kuka mai tsuma zuciyar duk mai sauraro. a kasar zuciyar ta take magana "Ayya Allah am ka zama gata na, ya ubangiji ka kawo min tallafi cikin gaggawa. hakika zuciya ta baza ta iya cigaba da daukan irin wannan wulakancin ba da kaskancin ba, azabar tayi min yawa." wani bangaren zuciyar ta ne ya kara tuno mata kalaman Umar "Tsintacciyar mage" dago kanta tayi ta kafe idanun ta waje guda tana nazarin maganar, kanta take tambaya.


"Shin wai wacece ni da kowa ya tashi bashida gori akaina sai tsintacciyar mage? Tabbas ya zama dole na nemi sani akan rayuwa ta don a yanzu kam zuciya ta ta gaza jurewa." fuskar nan tata tayi jajur sha'aninka da farar mace. Tana cikin wannan tunanin kuwa saiga Baba ya fito zashi majalisa tana ganin shi ta mike zumbur tana kallon shi ido cikin ido. can kuma sai hawaye ya kuma ballewa daga idanun ta ba tare da ta'iya cewa komai ba. sosai hankalin Baban ya tashi ya rikice yana tambayar ta


"Meke damun ki Sabriyya? Me Umarun yayi miki? Fada min mana bana son kukan nan"  hannun mahaifin nasu ta rike cikin gunjin kuka ta ce "Baba ka daure a wannan karon ka sanar dani wacece ni? Shin wai wacece ni Baba? cin mutuncin mutanen garin nan yayi min yawa Baba daga masu cemin shegiya sai masu kira na tsintacciyar mage. Me na tare musu ne Baba? Ni kadai nasan me nake ji a zuciya ta ka taimaka ka sanar dani asali na ko zan samu sassauci" Ta karasa maganar da wani sheshsheka mai cike da tashin hankali. Abin gwanin ban tausayi jawo hannun ta Baban yayi suka koma ciki don har mutane sun fara taruwa a wajen saboda irin kukan da takeyi din bana wasa bane.


Hankalin Baban a tashe ya wuce da'ita dakin shi ya zaunar da'ita sannan shima ya zauna yana faman sharce uban gumin dake yanko mishi. Sheshshekan takeyi har lokacin bata daina ba kofin ruwan dake gefen sa ya dauko ya bude hadi da mika mata "Ungo amshi kisha zuciyar ki tayi sanyi, bana son kukan nan kinji ko." Babu musu ta karba ta kafa kai tasha sosai sannan ta daga kai, hannu yasa ya amshi sauran ruwan ya aje a gefe. Babu laifi kuwa ta danji sanyi a zuciyar ta.


"Ki nutsu ki saurare ni Sabriyya. ke ba kowa bace face cikakkiyar yarinya mai asali wacce aka sameki ta hanyar aure. Duk wanda ya sake fada miki wannan kalmar wallahil azeem sai nayi sharia dashi ko dan gidan uban waye. share hawayen ki ki daina kuka, su kuma iyayen ki Allah ya bayyana mana su. Har abada bazan gushe ba wajen nema miki iyayen ki farin cikin rayuwar ki, amma ki kara hakuri kinji koh? shi kuma Umaru zanje har wajen mahaifin shi yaja masa kunne tun kafin abu ya baci mana." Sosai taji dadin hakan a ranta tayi mishi godiya da kulawar tashi sannan ta fita don shirin makaranta.




~Muje Zuwa...~








_*Meenauwal ce*_✍🏻

Post a Comment

0 Comments