🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍
*WASA DA SO* 🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍
_{ Ganganci }_
*TRUE LIFE LOVE STORY*. _(Labarin Soyayyar Gaske)_
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story And Edited By:*
*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_.
*Writing by:*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_.
*Facebook Aisha Mohammed Sani*.
*
BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*.
_Duk kan godiya ta tabbata ga ubangiji madaukaki sarki. Gaskiya ina matukar farin ciki da fara sabon novel dina fatana Allah yasa ya ilmantar da al'uma tare da nishdantarwa, ina rokon Allah ya yafemin kurakuren da zan yi wayanda bansani ba. Alkhairan da ke ciki kuma ya isa ga al'umma su amfana tare da alfahari damu_.
*KAMAR YADDA KUKA GANI TUN FARKO WANNAN LABARIN BA KIRKIRARRE BA NE YAFARU DA GASKE NE SAI YAN WASU ABUBUWAN DA AKA GYARA DOMIN TAFIYARDA SHI A TSARI*.
*HAPPY NEW YEAR /HAPPY BIRTH DAY TO MY SIS LYK NO OTHER FATIMA ZAHRA(MRS UMAR)*
_May this new year bring many opportunities your way, To explore_ _every joy of life & turning all your dreams into reality & all your efforts into great_ _achievements._😍😍😍
*PAGE* 2
------------------------------------------------------------------------------------------
Ba inda Adam ya nufa sai gida, ya na shiga su Mama da Aunty na falo .
Ya yi Sallama tare da kwallawa Hamida kira ,"SWEEETYYYYYYYY."
Mama Da Aunty Kawai Murmushi Su ka yi domin sunsan halin Adam da Hamida na tsokanar juna kamar Tom And Jerry sunan da Mubarak ke kiransu dashi kenan.
Hamida ta fito ta na, "Kai Adam wai miye haka ne ? ka kiyayeni fa tom."
Adam ya yi murmushi , "Ke dalla ki bini ahankali zan daga miki aji ki shirya gobe za mu je wurin wani bikin abokina."
Hamida ta yatsina fuska sanan ta ce, "Kai kasanni ba tsararka bace yasin sai dai ni indaga ma ka eheee."
Adam ya ce, "Eh naji dai aje agani za aga tsakanin nida ke waye ya fi aji."
Mama ta ce, "Ohhh nikam wayannan yara ku na bani mamaki kullum burinku bai wuce shirme ku na jin dadi kuwa?."
Adam ya ce, "Mama ki bari kawai ta rainani ne so nake ta je ta ga yadda yan mata suke roshin akai na ko ta ragemin raini."
Hamida ta tintsire da dariya , "Yooo daman yan karya irinka ba dole suyi roshin akan ka ba, ka ga nikam girki nake bara naje naduba,banda lokacin ka."ta juyo abinta tafara tafiya.
Adam ya ce, "Yauwa sweetiee nidai akawomin daki domin kinsan banyi breakfast ba dazu kin dan tabamin zuciya,."
Ko kallonsa bata yi ba ta nufi kitchen ta na murmushi abunta.
Aunty ta kalli Mama, "kwaji dashi dai."
Kowa ya taru afalo dai-dai lokacin da Hamida ta gama girkin rana,Ko wa na gida domin yau weekend ne har dasu Baba Da Abbah.
Hamida da Ta fara fito da abinci domin jerawa adainin Adam ya tashi ya na, "Haba sweetie bazaki ce nazo in tayaki ba kinata aiki ke kadai,kinsan fa banson ki na wahalar da kan ki irin haka."
Ko kula shi bata yi ba yatashi ya bita kitchen din yana, "Ke nifa a gidana ba za ki na girki ba wallahi yar aike zan nemo ke kome ba da masu yi inda hali har brush ma zan samo wanda zai miki."
Hamida abun ya matukar bata dariya hakan yasa ta ce, "Kai kam Yaya Messi wallahi matar ka ta shiga uku ita kam da karyar banza wato har me brush zaka nema ma ta! in baka nemo ma ta ba ai ka kara ma ta kishiya ko.?"
Adam ya ce, "Allah ko? kinsan fa inason ki shiyasa na ke raga miki ,kinga bani kayan abincin nan yau bazaki zuba kowa abinci ba aike ba baiwar su bace ni zan zuba."
Hamida ta ce, "Toh Babangida ko ince Adamu dodon mata ."
Dariya kawai ya yi ya ce, "Yarinya zo muje kiga yadda ake savin din mutane domin kar mu kai ki gidan miji muji kunya shiyasa da nasa na taimaka miki na aura."
Hamida ta ce, "Wallahi inna biyema sai su Aunty sun zo sunkarbi abincinsu kan kabar zubar nan."
Suka fita tare su nata dariya.
Cewar Aunty, "Ku kam inaga sai yunwa ta dankarar da mu sannan zaku kawo mana abincin."
Adam ya ce, "Aunty ai in fada miki yar nan bata iya kome ba nifa na tsaya gyara ma ta girkin fa ,kuma yau ni zanyi savin din kowa ku tsaya kallo."
Abba ya gyara zama tare da ce wa, "Yauwa Adamuna dan Albarka fara samin nikam."
Adamu banda iya yi ba abinda ya ke wajen zuba abinci har style yakewa abinci sukam banda dariya ba abinda su ke masa.
Ya ce, "Abba wallahi bara na yi kudi ka ga yan aiki goma zan samowa gidannan domin Hamida aure zan ma ta."
Mama ta ce, "Kuutt ah lallai Adamu kai ma ka aurar da kanka mana bare ita."
Adam ya tebe baki, "Abba kaji wai nine Adamu ko,ni wallahi adaina hadani da sunan yan kauye."
Babah ta ce, "Toh me za ace maka inba Adamun ba naga shi aka rada ma."
Abba ya ce, "A a fa kar inkara ji ancewa messi na Adamu."
Adam ya ce, "Yauwa Abbana kai da Auntyne kadai ku ke sona agidannan."
Haka dai suka ci abinci cikin nishadi banda tsokanarsu ba abinda Adam ya ke.
Washe gari
Adam natashi ya nufi kitchen domin ya san Hamida na chan .
0 Comments