IDONA.
"Labarin da yayi na Uku a Gasar ƙagaggun labarai
ta Mujallar Zauren Marubuta".
© Bamai A. Dabuwa Kkm
07037852514.
"Kaka."
"Iye."
"An ce a zamaninku kuna shan su taba da wiwi
amma da wayo..."
"In ji wa?" tsohon ya katse shi a fusace.
"E mana, ya ma sunan abun? Uuuumm! Yauwa
lofe. Wai a shi kuke hadawa kuna zuka. Kai ma
ka sha?"
"A'a. Ni ban sha ba."
"Me ya sa?"
"Saboda idona."
"Idonka kuma?"
"E."
"Ban gane ba, ta ina suka hadu?"
"Saboda shaye-shaye na rage karfin gani da
daddare."
"Hmmm!"
Shiru ne ya mamaye su na tsawon mintuna, kafin
daga bisani yaron ya kuma nisawa da wata
tambayar.
"Kaka."
"Miye?"
"Me ya fi komai sauri a jikin mutum?"
"Ido."
"Ba zuciya ba?"
"Ba zuciya ba!"
"Hujja fa?"
"Me ya sa idan abu ya faru da gaggawa muke
cewa cikin kiftawar ido don kambama saurin?"
"Eh kam. To menene a jikin mutum wanda ba ya
girma tare da karuwar girman jikinsa?"
"Ido."
"Ido dai?"
"Shi fa, domin shi ne tun haihuwarka na nan
yadda suke sabanin su hanci da kunne."
"Kaka."
"Kai! Ka dame ni fa."
"To a iska zan yi ta jelen kawo ma abinci
kullum?"
"Yaro ka daina, babanka ya kawo."
"Kaka."
"Ya aka yi?"
"An ce ka kware sosai a soyayya da sace zuciyar
mata lokacinka. Menene sirrin ka ban?"
"Idona."
"Shi ma?"
"Eh. Kana so ka ji?"
"Sosai ma."
"Tsaya na ci abincin to."
"Wato Kaka, zan so ka tsawaita rayuwa kamar
shekaru dari."
"Hmm! Na gode, ya aka yi ka san na ki jinin
mutuwa?"
"Ban sani ba."
"To me ya sa ma min wannan fatan?"
"So nake ka kai matsayin da hakoranka duk za
su zube, na kawo maka cin-cin ka ci. Babana ya
ba ni labarin yadda kakansa ke tauna goro ba
hakori, na ci dariya."
"Babanka ne ya ba ka labarin Babana?"
"Eh."
"Hmm! Idan kana so mace ta kware ma a
soyayya, abu na farko shi ne kallo."
"Kallo!? Ba za ta ce min maye ba?"
"Ba kallo irin na kurilla ba. Ina nufin ka sa idonka
a cikin nata. Ajinka nawa ma?"
"Ina S. S 2."
"Science ko Art?"
"Science."
"OK. Akwai sinadarin da yake sarka soyayya
tsakanin mutum da mutum a gangar jiki. Sunansa
Phenylethylamine yana samuwa a dalilin haduwar
idanun juna."
"Phen... Me!? Tab, ban taba ko ji ba."
"Yau ka ji. Amma ka sani kamar yadda wannan
sinadari ke haifar da shauki haka ne ma yake yi
wa tsoro. Idan ba ka iya hannunka ba ka kalli
wata zai iya zama kamar misalin haduwar idon
Zaki da Akuya ne."
"Ta yaya zan iya hannuna?"
"Da idonka."
"Ai kuma ka ce za su iya haifar da tsoro a
tsakani ma."
"Eh! Akwai kallon so ai."
"Ya kallon so yake?"
"Ka ga wannan digon bakin na cikin ido?"
"Eh."
"A duk lokacin da ka ga mutum ya kalli abu da
dukkanninsu, ina nufin idan suka gwale yayin
kallon abu to mutumin ya ga abun da yake so ne
ko shauki."
"Haka ne!?"
"Haka ne. Wanda ya san hannunsa yana fara
kallon abun da ya fi so ne a jikin wacce yake son
kafin ya nemi su hada ido."
"Na fahimta, amma ta ya zan gane ta afka?"
"Ba ka da fahimta."
"Da gaske ban gane ba Kaka."
"To ka lura da yanayin digon bakin idanuwanta
yayin da kuka hada idon."
Sunkuyar da kansa kasa ya yi yana jinjina
maganganun, kafin daga bisani ya dago a karaye
da cewa:
"Kaka ni matsoraci ne, ba zan iya hada ido da
mace har na fahimci haka ba ko na sa mata
sona ta kallo ido da ido!"
"Akwai wata hanyar ai."
"Yauwa! Wacce ce?"
"Idonk."
"Kuma dai?"
"Eh. Bari ka ji." Dattijon ya ce da shi kafin daga
bisani ya dora.
"Ban sani ba ko ka taba lura da wani abu
dangane da tasirin ido."
"Me?"
"Cewa idan da wani zai kura ma ido ta baya za
ka ji a jikinka ko ka tsargu ana kallonka."
"Eh kam, yana faruwa.
"Yauwa. To yadda ake yi idan kana jin tsoro ko
kunyar hada ido da ita shi ne satar kallonta."
"Satar kallo?"
"Eh. Ina nufin a duk lokacin da hankalinta ba ya
wajenka to ka kura mata ido kawai."
"Idan ta tsargu ta juyo fa?"
"Za ta juyo kam."
"Ai ka ji. Ni da nake da tsoro ya zan yi idan ta
juyo?"
"Ka dauke kanka daga gareta da sauri."
"Kwafsi kenan. Ina hikimar hakan?"
"Hmm! Hanyoyin shigar soyayyar matsorata da
masu kunya guda uku ne."
"Ina jinka."
"Na farko shi ne satar kallon wacce ake so, gaza
dauke ido yayin da aka hangota daga nesa. Sai
kuma kauda kai yayin da ta kama ana kallonta.
Idan wadannan abubuwan suka faru tsakaninku,
to so ya gitta kenan. Kuma hakan zai haifar
mata da waccan sinadarin kwatankwacin na saka
idonka a nata. Sai dai..."
"Sai dai me kuma?"
"Idan ka hadu da wacce ta san hannunta ko ta
kware a yaudara to ta yi ta rufta ka kenan alhalin
ba son naka take ba. Ina nufin wacce ta san
sirrikan ido."
"Akwai matsala kenan."
"Idan da gara ta hadu ba!"
"Ana gane su ne to?"
"Sosai ma."
"Ta yaya?"
"Da ido."
"Komai wai da ido ake yi ne?"
"Yaro za ka iya binne damuwarka ta hanyar
murmushi, amma duk wayonka sai ido sun
fallasa."
"Ina jinka to."
"Kasan me?"
"A'a. Me?"
"Zan fada maka wasu sirrikan ido da kallo a
cukurkude kila, ya rage naka ka fahimta."
"To Kaka, ina sauraro."
"A komai idan kana son gano gaskiya ko karyar
mutane to ka fara sa su a daidain yanayinsu."
"Ban gane wannan ba aradu."
"Ina nufin ka fara sawa su ji sakayau nutsuwa da
sakin jiki."
"Na gane, amma ta yaya zan sa su ji hakan?"
"Misali: Idan kana son fahimtar gaskiyar matarka
ko budurwa musamman wacce kake zargin ta
san hannunta a karya. Ka fara dauko wata hirar
ku tattauna kalar hirar da babu wani dalili na
karya ko 6oye wani abu akai. Kamar akan yanayi
ko wani film da kuka kalla. Da zarar ta saki jiki
ta fara magana a lokacin ka zubawa yanayinta
ido, kuma ka haddace su. Domin za ta
kuskurewa yanayin ranar da ka tuhumeta akan
abun da take ma karyar duk wayo da sanin
hannunta."
"Hmmmmm!"
"Daga karshe, tsaya ka ji wannan."
"To. "
"Makaryata sun fi masu gaskiya yawan hada ido
da mutum. Amma masu gaskiyar sun fi jurar
haduwar idon yayin da aka fuskance su."
Shiru yaron ya yi yana kallonsa, wannan ya ba
shi damar ci gaba.
"Idan kana magana da mutum ko ka ga ya daga
kai yana kallon sama, hoton abun da kake fada
yake wassafawa. Ko wani abu yake son tunowa
idan shi ne mai maganar."
"Haka ne?"
"Eh. Idan kuma kana magana da mutum ko da
zarar kun hada ido ya dukar da kansa wannan
yana girmama ka ne ko ya aikata laifin da ake
tuhumarsa."
"Na san wannan."
"Idan mace ta kalle ka sannan ta daga kanta
sama kuma ta kalli wani waje tana nufin "mu je
can"."
"Idan ka hangi mutum kansa a duke sannan ya
kalli bangaren hagu to magana yake da kansa."
"Da gaske?"
"Da gaske. Idan kuma ka ga kwayar idon mutum
na juyawa gefe da gefe, ba shi da gaskiya ko ta
carke."
"Hhhh! Tsuru-tsuru kenan."
"Idan mutum ya dauke idonsa daga gareka da
daga kai sama yana kallon hancinsa, yana nufin
ya wuce da ajinka."
A daidai nan ya yi shiru yana numfasawa kadan-
kadan.
"Kaka."
"Kai! Tashi ka tafi mai surutun tsiya."
Karshe.
0 Comments