[Hausa Novel] Bamisriya Ta Page 3 By Abubakar Saleh Alquyraemey


💞 💞 💞 💞 💞 💞 💞 💞
          *BAMISIRIYA TA*
           💞 💞 💞 💞 💞 💞 💞

👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
__________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
__________________________________

©2019

*🆙DATE*


*Page 3*


*STORY BY*

      _DEEN_💘


*TYPING BY*

      _Abubakar Saleh Al-Quyraemey_💘

 ```@Facebook Abubakar Saleh AlQuyraemey```


~Sadaukarwa Ga Zamani Writer's Association Allah Ya Kara Hade Kanmu Ameen Ya Hayyu Ya Qayyumu.~



*_Better is not something you wish, it is something you become._*

   


بسم الله الرحمن الرحيم


```Bazan manta ba ina fadamaku cewa kamar a mafarki sai naga wani abu a fuskarta makamancin abunda yake zuba daga fuskata hawayene yake zuba daga idanunta ko meyasa
```


Inata tunanin me  yasa wannan kyakykyawar yarinya take zubar da hawaye haka, a kaina ne ko itama ta kamu da soyayyata ne? soyayyar da ake cewa soyayyar ganin farko wanda kana ganin mutum nan take zakaji stamping sansa ya rattafu a zuciyarka, kodai itama irin wannan son ne ya rattafu a zuciyar ta.

"Ya Salam"

Nan take na tashi a firgice ina son na fita amman kash! sai na lura jirgin yayi nisa da tafiya, gashi kuma idan hr ya fara tafiya to baya tsayawa har sai yaje madakatarsa {m'ana yaje tashar sa}…

Nayita ɗaɗɗaga kai ina son na ganta, can na tsinkayonta tana tsaye tana kallon jirgin yayin da yake tafiya, kawai sai naga ta girgiza kanta ta koma wurin zamanta ta zauna a keɓance tayi tagumi. Nan take naji zuciyata kamar zata yi bindiga ta fashe na ce "Akan me na yarda na bar wannan waje bayan duk irin alamun data nuna mani, Mai yasa zan bar wannan waje!?"…

"Subhanallah kaga wasu yan tsirarun mintuna zasu canza mani kaddarar rayuwa, yarinyar nan ban taɓa ganin ta ba, ban ma san sunan ta ba komeye ma sunan ta".Duk waɗannan surutan a zuciyata nake yin su. To ganin bani da amsoshin su yasa na a danasu a ƙarkashin zuciyata.

Bayan tafiyar sa'a biyu mun samu mun isa Alexandria, tun da muka isa ban samu cewa komai ba, yayin da abokaina suka cigaba da musayayyaya kamar yanda suka saba.

"kai kasan Allah duk rashin san gaskiyarka dole ka yarda cewa naman zabuwa yafi na kaza dadi wlh" a cewar Hizbullah.

"Mene ya kawo dole abu ne fa na ra'ayi, kowa da abunda yake da ra'ayi, sannan da yanda yake jin ɗanɗano a bakin sa ni dandanon kaza yafi mani na zabuwa dadi simple" a cewar kamala yana dariya sbd yanda yaga Hizbullah ya yi kamar an jiƙa buri a ruwa.

Suka ci gaba da gardamar su, ni dai sam bata tasu nake yi ba ina ta tunanin abunda yake mafi A'ala a wannan lokaci a rayuwata.

Gamu dai a Alexandria amman ni gaba daya tunani na yana tashar jirgin ƙasa ta Ramsis.

Muka fita daga cikin jirgin, muka shiga gari muka je gurin cin abinci, muka ci abincin muka je bakin ruwa muka dauki hotuna, muka je wajajen shakatawa da gidajen tarihi, amman kwata-kwata bazan iya tuna abubuwan da mukayi ba sbd zuciyata da tunanina tana tashar jirgin kasa ta Ramsis.

Abokaina suma jikinsu yayi masu wani iri basu gane mani ba sai suka tambayeni.

"Kai hamago. Tun ɗazu kayi wani zugum kamar anyi maka mutuwa me yake damu nka eeyyeehh?" a cewar Hizbullah

Sai kamala ya ce "Nima nakasa gane mashi wlh yadai da fatan komai lpa?" Sai na ce masu "komai lpa kawai kaina ne yake mani ciw amman daga haka babu abinda ke damuna".

Kamala yace "kaga ina da maganin ciwon kai, zo kaga kawo kan ka" ya kai hannunsa yana ƙokarin tallafo mani kai. Ganin haka yasa Hixbullah ya ce dashi "kaga malam sakar masa kai mana kana ta wani jawo masa kai wai me ma zaka yi masa?" nan kamala ya buɗi baki ya ce "Gware zan masa, Allah idan nayi masa sai ya watstsake fa" Duka dariya muka saka masa, ni dai dariyar da na keyi ana iya kiranta da yaƙe sbd bata wuce iya baki na ba lol. Haka dai Hixbullah ya hanashi yi Mani wannan gwaren da yaketa ikirarin zaiyi mani.

A haka muka gama yawace-yawacen shakatawarmu.Sannan muka koma tashar jirgin Ƙasa domin shiga jirgin Ƙarfe *8:00pm* domin mu isa Cairo da karfe *10:00pm* kasan cewar 2hrs ne tsakanin su.

A haka wannan jirgi yaketa sheƙa gudu kamar zai tashi sama amman ni ji nake kamar a tsaikance muke tamkar na hau bayan kunkuru. Bayan munyi tafiya ta kamar kimanin minti *45mins* sai jirgin ya nemi waje ya tsaya kasancewar jirgin yana tsayawa a kowace tasha dake hanyarsa. To mun ɗauka irin wannan tsayuwarce, to ashe ba haka bane sai suke sanar damu ce wa "na cikin wannan jirgi suyi hakuri kasancewar sun sami labarin cewa ana rikici a can Cairo, sbd wasu daga cikin yan ƙasa sunyi tawaye ga shugaban kasar Husunni Mubarak. A dalilin haka wannan jirgi bazai karasa Cairo ba a wannan dare ba.

An Sanar damu cewa "Sai dai mu kwana a wani gari mai suna Tanta Wanda yake tsakanin Alexandria da Cairo", nan take naji wani hijabin bakin ciki ya lullubeni tamkar bantaҍa farin ciki ba tunda nake a rayuwata ba, haka zalika na shiga wani matukar tashin hankali kasancewar an fara tawaye a wannan ƙasa, wannan yarinya ko wane hali take ciki bansani ba?.

"Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un……"

Abinda na din ga maimaitawa kenn sbd na samu kai na a ganiyar tashin hankali da firgici. Nan take zuciyata ta tunatar da ni cewa wasu damarmaki sukan zo wa mutum sau ɗaya tak a rayuwarsa, da zarar ya bari ta kuɓuce masa to shikenn yarasa ta, yanzu wannan irin wadannan damarmakin ne nayi arba da ita kuma narasa ta, wayyo Allah!!!.

Naji wani ɗaci ya lulluɓe mani zuciyata, sai na saduda, mai yuwuwa irin wannan abunne dazaka haɗu da mutum sau ɗaya tak a rayuwarka, wanda zakaji kana tambayar kan ka mai yasa tun a farkon rayuwar ka baku haɗuba.

Amman kuma kafin ka farka saika nemishi karasa, baka sake ganin sa har abada.





*Muje zuwa .......*




*✒Abubakar Saleh Al~Quyraemey*

 ```{Young Writer}```

Post a Comment

0 Comments