📖✏️
ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION.
Kamala Minna.
Kamalminna217@gmail.com
MAKASHINKA.
Da sunan Allah Mai Rahama mai jiƙai..gidiya ga Allah madaukakin sarki ma raya da kashe wa Rabbi ya karo wasila da fadila ga fiyayyan halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihin wasallam.
1-1-2020.
01.
Numfashi ta sauke, tana mai daga idanuwanta sama zuwa inda agogo ya buga karfe biyar dai-dai na yamma Remote din dake hannunta tashi juyawa zuciyar na wata irin bugawa a hankali.
'Ko dai yau bai zai gabatar da shirin bane, anya kuwa kalau yake, gashi har Biyar ta buga, shirin da suke farawa wani lokacin tun kafin Biyar tayi ma za a nuna sanarwa, amma yau ba alamun haka me yasa?'.
Zantukan da take ta faman kokawa da su kenan da zuciyarta.
Sake daga kanta tayi, ta dubi Agogon Biyar har da minti uku.
Runtse idanu tayi a jikin take ji ba zata iya jurewa ba, ba zata iya daukar wannan yanayin ba zuciyarta zata yi ciwo, ciwo mai girma da ta jima tana dakon sa.
'Don Allah ku taimaka ku sanya ko da na minti daya ne, ku taimaka mani ko fuskarsa ce na gani'.
Zantukan da take tayi kenan tana gyaɗa kai, idanuwanta kan Tv din da yake ta faman motsi.
jikin ta ji yayi sanyi lokaci guda, kanta ya fara sarawa runtse idanu tayi tana ambaton 'Hasbunallahu wani'imal wakil' kafun ta buɗe su ta sake duban Tv har izuwa wannna lokacin ba canji ba alamun ma shirin za a sako shi.
Ajje Remote din dake hannunta tayi tana mai tallaɓe haɓarta da duk hannayenta idanuwanta kuri kan Tv ba ta san lokacin da taji hawaye sun fara taruwa cikin idanuwanta ba sai da taji saukar su gefen yatsunta ba ta damu ba don ta san fiye da haka ma zai iya faruwa dalilin rashin tabbatar abin da take muradi a yanzu.
Ta tabbata in har ba a gabatar da shirin nan ba to tabbas komai zai iya faruwa da ita.
"Safeenah".
Da sauri ta dawo daga duniyar tunanin da ta afka tana mai dago idanuwanta da suka gama jikewa da hawaye kafun ta miƙe cikin hanzari tana mai rungume Mami gami da sakin kuka.
"Mami sun ki saka shirin ban san me yasa ba, kin ga ni..."
Ta tsagaita da maganar cikin sarkewar harshe dan yatsanta ta shiga nuna tvn dashi kafun ta sake sakin kuka maras sauti.
"Don Allah Mami ki kira su ki ce, in saboda da ni ne suka ki saka shirin ko nayi musu laifi suyi hakuri wallahi ba zan iya jure rashin ganinsa ba, zuciyata..".
Ta kamo hannun Mami da tayi sakato tana kallon 'yarta ta cikin wani irin yanayi na tsananin damuwa da tausayi.
Safeenah ta kai hannun Mami saitin zuciyarta.
"Kin ji Mami zuciya bugawa take yi ji nake kamar zata keto daga mazauninta ta fito waje da gaske nake ba zan iya jure rashin ganin shirin nan ba Mami shine farin cikina walwalata...".
Sarkewar da harshenta ya yi hakan ya sanyata saurin matse jikinta sosai a na Mami numfashinta take jin yana barazanar daukewa runtse idanu tayi wasu zafafan hawaye masu tsananin kaifi kamar za su keta mata fuska suka shiga kwaranyowa.
Ita kanta Mami hawaye take yi hannunta guda ta kai bayan Safeenah ta na shafawa a hankali kafun cikin sanyin murya da kwantar da hankali ta shiga faɗi.
"Feenah ki yi hakuri ba su ki saka shirin naki ba don wani abu ba, sannna ba suki sakawa don ko kin yi musu laifi ba, ba laifin da kika yi musu a ina ma kika ga ma'aikatan gidan Tvn balle har kiyi musu laifi...".
Da sauri ta katse Mami ta hanyar dago kanta ta sauke mata idanuwanta da suka kaɗa sukayi jajir.
"Mami to me yasa za suki sakawa, in ba wani abu nayi musu ba, ji har Text na tura musu suka karanta na kowa amma ban da nawa".
'Yaa Rabbi'.
Mami ta faɗi cikin zuciyarta da wani irin yanayi na tsananin tausayin Safeenah kallonta take yi tana mai gyaɗa mata kai don ta rasa ma me za ta ce da ita da zai sanyata gane cewa ba saboda ita suka ki saka shirin ba, ta san ko ya za ta karanta mata uzuri ba zata dauka ba.
"Feenah ki kwantar da hankali, ba abin da zai hana su gabatar da shirin sai dai in 'yar matsala aka samu ko ta sharrin kayan bature (Na'ura) ko kuma dai jiki da jini...".
Da sauri Safeenah ta shiga girgiza kai hawaye na sake wadatuwa a kumatun ta maganar Mami ta karshe sun yi matukar dukan zuciyarta bata so zuciyarta ta gasgasta tafi kaunar ace sharrin na'ura ne kar ace mata Yaa Deen ne babu lafiya ba za ta iya jurewa ba zuciyarta zata iya faɗawa ko wani irin yanayi.
Cikin rawar laɓɓan ta sake buɗe idanuwanta tana duban Mami.
"Mami kar ki ce min Yaa Deen ne ba shi da lafiya?".
Wani irin kallo Mami take mata mai cike da tuhuma da bukatar karin haske kan maganar ta ta.
"Me kike nufi Feenah?".
Ta faɗi tana tsareta da idanu sosai kafun ta ja wata ajiyar zuciya ta na mai da idanuwanta zuwa sashin Tv.
"....Muna neman afuwarku masu kallonmu, a bisa rashin kawo muku shirin 'SIRRIN ZUCI' akan lokaci. Haka ya faru ne bisa 'yar matsala da aka samu, bangaren na'ura dafatan za kuyi mana afuwa. Sannan muna masu sanar da ku a ko wani lokaci za ku iya kasancewa damu in komai ya daidai....kafun zuwa shirin ku nishaɗantu da wannan.."
Numfashi Mami ta sauke kafun ta dubi Safeenah da tayi kasake tana sauraron sanarwar da ake yi.
"Yanzu hankalin ki sai ya kwanta ko ba Yaa Deen din bane ba shi da lafiya, sannan kuma shirin nan za a gabatar dashi...sai ki koma ki zauna kar ki faɗi".
Murmushi Safeenah tayi mai tafe da guntayen hawayen da suka maƙale mata a hankali ta ja kafarta mai lafiya hannunta guda saman maras lafiya ta koma ta zauna tana mai ajje numfashi mai kwari.
Zuciyar ta sake buɗewa da farin ciki wanda har ya kasa tsayawa cikin zuciya ya bayya a fuskarta karara.
Mami cigaba tayi da kallonta na wani lokaci kafun ta gyaɗa kai ciki zancen zucin da take fata Allah yasa ba abin da take aiyana mata bane game da Safeenah.
Domin ita kadai ta san yadda take tausayin 'yar ta ta, ba za ta so hakan ta kasance ba za ta fi kowa jin ciwo don ta san ba abu bane da zai haifar da ɗa mai ido ba..
Da wannan tunanin ta juya domin kowa dakinta.
Ita kuwa Safeenah Idanuwanta na kan Tv sosai zuciyarta ke doki da murna yau zata ga Yaa Deen dinta.
'Allah Sarki Yaa Deen zan so na kawo maka ziyara cikin shirin nan naka'.
Abin da ta faɗi kenan a zuciyarta tana kaɗa kai farin ciki na sake ƙawa a fuskarta.
"Masu sauraron mu muna neman afuwarku ba za mu samu damar gabatar muku da shirin 'SIRRIN ZUCI' ba a wannan rana ba bi sa rashin samuwar yadda muke so muna neman afuwarku ku tare mu ranar Laraba da misalin karfe biyar na yamma domin jin mu da shirin'.
Wata irin dokawa zuciyar Safeenah tayi, idanuwan kafe a Tv ji take yi kamar ta shako wuyar mai sanarwar ta hadashi da bango don takaici.
Laɓɓanta ta tura baki tana cizawa kafun ta miƙe da ƙyar hannun dafe da kafarta mara lafiya ta shiga tafiya a hankali.
Zuciyarta na sake matsewa duk wani farinciki da murna da ta fara duk ya kau haka kawai take jin jikinta ya yi mata sanyi sosai a haka har ta karasa dakinta ta zube bakin gadonta tana daura kanta kan gadon nata ta shiga mai da numfashi a hankali.
'Yaa Deen me yasa haka, me yasa suka hanaka gabatar da shirinka.Sosai nake jin farinciki sosai nake jin nishaɗi a duk lokacin da na ganka kana gabatar da shirin 'Sirri Zuci' amma sai dai yau akasin haka...don Allah kar ka yarda ranar Laraba su sake yi maka haka zuciyata ba za ta jure ba'.
Zantukan da ta dinga yi kenan ita da zuciyarta, don komai ji take yi ba ya yi mata dadi, domin kuwa sosai ta kwallafa rai game da shirin nan na yau musamman abubuwan da Yaa Deen yace zai sanar game da wasikar da ya karanta waccan karon.
Gandoki sosai take yi don har mafarkin abin ta yi amma an yanke mata duk wani tanaji da tayi wa shirin.
Buɗe idanuwanta tayi a hankali tana mai jin wani iri a jikinta mikewa tayi dakyar tana jan jikinta har zuwa saman gadon tayi lamo kamar mai kokarin yin barci amma ba haka bane kawai tunanin Yaa Deen take yi.
***
"Safeenah In fada miki yau muka hadu da Yaa Deen...".
Safeenah da tayi lamo cikin kujera kamar 'yar mage tun dazu da sauri ta zabura ta mike zaune tana duban Zafeera idanuwanta a warware.
"Da gaske kike Zafeera don Allah kun yi magana kin sanar dashi ni masoyiyar shirin sa ne 'Sirrin Zuci' me ya ce miki Allah ya sa kin faɗa masa yadda nake son shirin...".
Tunda ta fara magana jikinta ke rawa ko numfashi taki bari ta ja sai da taji harshen ta ya sarke tari ya turnuke ta idanuwanta suka kawo kwalla
Mami dake zaune gefe ta shiga bin ta da kallo da wani irin kalolin abubuwa wanda bata san ya zata fassara su ba zuciyarta take ji tana sake sarkewa da tausayin 'yar ta ta bata taba ganin yarinya irin Safeenah ba bata taba ganin zallar kauna ga wani abu wacce ta tsakani da Allah irin ta Safeenah ba...
Runtse idanu tayi kafun ta buɗe su tana sake duban Safeenah wacce ta dafe kirjinta idanuwanta sun kaɗa sun yi jajir.
"Feenah mana!".
Zafeera ta faɗi tana girgiza mata kai kafun ta mike ta isa wajanta ta zauna gami da riko hannunta ta damke cikin nata.
"Feenah ki dinga rangwanta wa kan ki, da gaske ban faɗi maki don ki tashi hankalin ki ba na faɗi miki ko za kiyi farin ciki amma sai akasin haka..".
Murmushi Safeenah tayi tana mai goge fuskarta ta dubi Zafeera.
"Da gaske farin ciki nake Zafeera don Allah bani labarin Yaa Deen".
Girgiza kai take yi tana jin yadda tausayim 'yar uwarta ta ke samun masauki azuciyarta ina ma ace kaunar da take nuna wa Yaa Deen shima ya kauna ce ta haka ya faranta mata kamar yadda a kullum take masa fatan alheri a kullum bata da labari sai na shi in har kana so ka ga fara'ar Safeenah to ka kawo mata labarin Yaa Deen ko labarin Shirin 'Sirrin Zuci'.
Girgiza ta da Safeenah take yi shi ya katse mata tunanin da take da sauri ta dauke kai tana goge kwallar da ta cika mata idanu bata so Safeenah ta gani don ita kadai ta san irin kalar tausayin da take mata game da Yaa Deen in ta tuna yanayin da ta ga ya nuna mata da ta masa magana abin ya taba mata zuciya bata tunanin Safeenah zata samu kwatankwanci haka a wajansa a yadda take din nan.
"Zafeera Don Allah fada mani ya ku ka yi da Yaa Deen?".
Dubanta take yi tausayinta na danne mata harshe bata san mi zata ce mata ba, bata san mai ya kamata tace mata ba game da Yaa Deen. Shin ta faɗa mata gaskiya ne ko ya ya, in ta faɗa mata gaskiya da matsala, amma bata so ta yi mata karya sam.
Duban Mami Zafeera tayi tana mata alamu da idanu da sauri Mami ta dauke kai don bata san me ya kamata tace ba don ita kanta a gaban idanunta komai ya faru shiyasa tausayin Safeenah ke kara narkar mata da zuciya fargaba da tsoro sun kara wadatuwa.
"Shikenan...Zafee tun da ba zaki faɗa mani ba, na hakura na sani dama ba ki son farin cikina game da Yaa Deen kin kasa fahimta ta game dashi...".
Safeenah ta mike tana jan kafarta zuwa inda Mami take zaune zama tayi sosai kafun ta kamo hannun Mami idanuwanta cike da kwalla.
"Mamina kin ga Zafee ta ki faɗa min sakon Yaa Deen ko, dama na sani bata so na da farin cikin da nake nuna wa game dashi Mamina ke kan ki kin sani farin cikin da nake samu ta hanyar Yaa Deen game da shirin sa na 'Sirrin Zuci'".
Numfashi ta sauke tana sake riko hannun Mami sosai. Mami ji tayi zuciyar tayi wata irin dokawa ihu sosai take ji a cikin kanta game da Safeenah ihun tashin hankalin da za su shiga a duk lokacin da Safeenah ta hadu da Yaa Deen yana nuna mata halin da ya nuna wa Zafeera bata jin zuciyarta za ta iya jure wa bata jin za su samu kwanciyar hankali gabadayar su domin kuwa kwanciyar hankalin Safeenah shine na su tashin hankalinta duk tare za su raba shi.
"Mami..".
Safeenah ta faɗi tana mai jan numfashi kafun ta dora d faɗin,
"Na san kin ga komai Mami na san a gabanki komai ya faru faɗa mani me Yaa Deen yace?".
Wata irin dokawa zuciyar Mami tayi amma bata bari hakan ya fito a zahirin fuskarta ba illa murmushi da ta saki da bai kai zuci ba ta riko Safeenah sosai ta haɗe ta da jikinta ta rungume.
"Safeenah bana wajan lokacin sai da na fito daga cikin Bank din Zafeera ke faɗa min yanzu suka hadu da...".
A hankali ta zare jikinta daga jikin Mami tana mikewa ba tare da ta ce da ita komai ba ta ja kafar ta ta nufi dakin ta.
Zafeera da jikinta ya gama yin sanyi ta dubi Mami tana faman gyaɗa kai cikin yanayi na tausayawa Safeenah.
"Amma Mami...".
Da sauri ta daga mata hannu tana mata nuni da Safeenah da bata karasa shigewa dakin ta ba, Sai da ta ga ta turo kofar da dan karfi sannna Mami tayi ajiyar zuciya tana sake duban Zafeera.
"Abin da nake ta gudu kenan Zafeera, ban so ki ka sanar da ita ba don na tabbatar da ma hakan sai ta faru duk yadda kike zaton Safeenah game da wannan mutumin ya ya zarce wallahi ni kadai na san halin da nake ganinta a ciki da yadda take kasancewa a duk lokacin da aka ce miki shirin mutumin lokacin sa ya gabato abinci wannan sai nayi daƙyar take cin sa".
Tasowa tayi daga inda take zaune ta iso wajan Mami ta zauna tana mai bin hanyar da Safeenah ta bi da idanu.
"Da gaske Mami ban san haka zai kasance ba na san dai Safeenah na farinciki sosai game dashi amma ban yi zaton abin ya kai har haka ba".
Yaƙe Mami tayi don ita kada ta san halin da take tsintar kanta game da Safeenah.
"Ban san ta ya ya zan dakatar da al'amarin nan ba, don Allah na gani bana son Shakuwar nan ta Safeenah game da mutumin da ba ta taba ganinsa a zahiri ba iyakarta dashi a tv kin ga kenan da matsala...ba ma wannna ba Zafeera ki dubi Safeenah kina tunanin zai mata duba na kirki a duk lokacin da suka hadu a zahiri?".
Shiru Zafeera tayi gami da zabga tagumi tana nazarin maganganun Mami wanda lokaci guda ta hango abin da Mami take yiwa fargaba.
Sai dai kuma ita a zuciyar bata so hakan ya yi tasiri duk da ta san dole wani abu zai faru.
"Uhmm".
Abinda ta iya kokarin faɗi kenan tana mai gyara zamanta kafun ta dubi Mami sosai.
"Maganar gaskiya Mami nima kaina ina fargabar abin da zai je ya zo mutumin nan ba kirki gare shi ba kina kallon yadda ya amshe ni a wulakance kamar ya ga kash...".
"Zafeera amma dai ba Yaa Deen ba ko?".
Wata irin razana ce ta ziyarce su Zafeera don ba su taba zaton Safeenah zata fito a daidai wannna lokacin ba jikin Zafeera har rawa yake yi ta dubi Mami da tayi mutuwar zaune sai faman ajje numfashi take kafun ta yi kokarin kwato kanta ta dawo kan doka da oda ta dubi Safeenah da ta jingina kafarta mara lafiyar da jikin kujera ta harɗe hannayenta a kirji ta zuba musu idanu.
"Feenah me ya kawo batun Yaa Deen kuma, ai tunda ki ka shiga daki ba mu sake zancen sa ba don ni kaina raina bai min dadi ba na rashin faɗa miki abinda ya faru da Zafeera bata yi ba ki yi hakuri Safeenah kar ki yi fushi In Allah ya yarda wata rana da kaina zan kai ki wajan sa ku gaisa".
Ta karashe cikin dakewa don ita kadai ta san abin da take ji kasar zuciyarta tsoranta daya Allah yasa Safeenah ba ta fahimci da Yaa Deen din suke ba kokarin kalato murmushi tayi ta daura a fuskarta tana kallon Safeenah din wacce tayi musu kuri da idanu kamar mai son nazartar wani abu lokaci guda kuma ta gyaɗa kai ta juya ta nufi dakinta.
"Mami ke ki ka min Alkawari, ni kuma zan tura masa da sako gobe na bukaci son ganawa dashi in har ya aminci sai ki kai ni tunda kin daukar min alkawari".
Ta karashe tana tura kofa tana shigewa cikin dakin ba tare da ta jira cewar Mami din ba.
"Na yarda".
Mami ta faɗi cikin daga murya don kara tabbatar mata sannan ta kau da shakkun da ta gani cikin idanun Safeenah.
Mikewa Zafeera tayi tana faman gyaɗa kai don ta rasa ma mi za ta ce al'amarin Safeenah ya fara danne tunaninta a cikin yan mintina duk yadda takai da zaton Safeenah game da Yaa Deen ta zarce haka.
'Wannnan wata irin shakuwa ce, wannan wata irin kauna ce ta baɗi ni Safeenah ke yiwa mutumin nan, mutumin da bata zaton zai dube ta da idanun arzuki'.
Zantukan da suke ta faman yi mata ihu a kwakwalwa da zuciya kenan har ta isa kofar da zata sa da ta da kicin.
"Zafeera!!".
Mami ta furta cikin yanayin tashin hankali da sauri Zafeera ta saki Handle din dake tsakanin yatsunta ta juyo da sauri tana duban Mami da take ta faman yi mata nuni da dakin Safeenah.
Don gabadaya jin kafafuwanta tayi sun rike ta kasa motsawa zuciyarta sai faman bugu take yi cikin sauri-sauri.
Da hanzari Zafeera ta iso tana duban Mami bakinta sai rawa yake yi so take yi ta tambayeta meke faruwa amma ta kasa.
Sautin numfashin da take jiyo ya tabbatar mata da kome Mami ke nufi da hanzari ta nufi dakin Safeenah har tana kokarin faɗuwa....
Wassalmau alaikum waramatulllahi ta'ala wabarakatuhu..Yan uwa dangin juna barkanmu da wannan lokacu da fatan mun tabbata cikin aminci da nagarta da lafiya cikin wannna sabuwar shekara ta 2020..Rabbi ya tsare mu ya tsare mana rayuwa da zuciyoyinmu Rabbi ya yafe mana laifukanmi na fili da na boye...Rabbi ya albarkace mu da rayuwarmu.
Yadda muka ga sabuwar shekarar nan lafiya Rabbi ya bamu ikon ganin karshenta lafiya.
Gamu tafe da sabuwar tafiya ina bukatar ji daga gareku gyara tsokaci shawara su ne abin bukata kofa a buɗe take
Happy New Happy to all.my lovely fan's😍😍
Son so Fisabilillah.
#Ana tare
#Makashinka
#Z.W.A
#Kamala Minna
#2020
0 Comments