https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹
💦 *AAIRAH* 💦
🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹
*{ ROMANTIC LOVE STORY}*
*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION*
_*WE ARE HERE TO EDUCATED, MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READER'S*_
```DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN K'AI, SARKIN DA BA WANI BAYAN SA! TSIRA DA AMINCI SU K'ARA TABBATA GA ANNABI MUHAMMAD ( S.A.W ).```
``` YA ALLAH INA ROK'ON KA! KAMAR YADDA NA FARA LITTAFIN NAN LAFIYA ALLAH YASA NA GAMA LAFIYA AMEEN```».
©®
•°♥ _*HAFSAT IBRAHIM UMAR*_
✨ *1* ✨
Da misalin 9:30 na safiyar ranar laraba, na hango wata yarinya wadda bazata gaza shekara goma ba, tana tafe tana kuka ga kayan makarantar dake jikinta sky blue da dark blue sunyi bakikkirin kamar kayan kanikanci.
K'afarta sanye take da takalmi silifas amma ya sud'e a kuma tsinke an d'add'aure shi da yankin k'yalle, hannunta rike da bak'ar leda! Da alama littattafan tane a ciki.
Bishiyar data saba zuwa nan ta k'arasa, bayan bishiyar ta lek'a ko zataga abincin da aka saba ajiye mata yana nan? Ilai kuwa ta ganshi a cikin bak'ar leda a nad'e ga Kuma jarkar lemo da ruwa a gefe.
Zaman durshan tayi jikinta na kyarma ta d'auko abincin ta bud'e, dankali da plaintain ne sai kuma sharb'eb'iyar wainar kwai a gefe, d'ayan ta k'ara d'aukowa ta bud'e! shi kuma sakwarace da miyar a gushi taji ganda da naman kaji, ta rasa wanne zataci? Daga baya ta yanke shawarar cin sakwarar anjima taci dankalin.
Ai kuwa batayi wata-wata ba ta fara danna sakwarar hannu baka hannu kwarya, tanayi tana kalle-kalle saboda unguwar tayi tsit, bakajin komai sai kukan tsuntsaye.
Wata mata naga ta fito daga wani gefen gida inda take a rakub'e, gurin da yarinyar take ta nufa tana k'are mata kallo saboda yadda taga tana cin abincin hakan sai ya k'ara bata tausayi.
Saboda yadda cikinta yake mata kuka yasa bataji takun taba sai maganarta taji a kanta tana mata sallama.
A firgice ta d'ago zata ruga a guje, matar tayi sauri ta dank'ota saboda taga yadda ta firgita.
Idanunta ne suka ciko da hawaye
" Yi hakuri! Babu abinda zan miki, nice wadda nake ajiye miki abinci anan tsawon shekara guda kenan, ki kwantar da hankalin ki magana zamuyi kinji?".
Shiru tayi tana kallon matar wadda take sanye da kaya lemon green komai da komai fuskarta sai shek'i take ga dukkan alamu yar gayuce.
A hankali ta dunga sauke ajiyar zuciya harta koma ta zauna, Kuma har lokacin bata daina kallon matar ba.
Ganin yarinyar ta zauna yasa itama taja wani dutse dake gefen bishiyar ta zauna tana kallonta, Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace da yarinyar.
" Sunana Hjy Rahma Abdulfatah! Ni cikakkiyar lawyer ce me kare hakkin d'an adam daga nan Nigeria har k'asashen waje. Sannan mijina Ambassador ne a America, da d'ana guda d'aya ARBAN! Soja ne amma ba'a k'asar nan yake aiki ba, ga gidana can anan nake da zama".
D'aga kanta tayi tana kallon gurin da take nuna mata inda yake da d'an nisa daga inda suke, juyowa tayi taci gaba da kallonta saboda jin datayi tana son ci gaba da magana.
" Amm! Ya sunan ki? Kuma ina ne gidan ku? Me isa kullum idan zaki tafi makaranta kike kuka ?"
Shiru tayi ta kasa cewa komai sai hawaye da suke zuba daga idanunta, sai da ta shafe kusan minti 30 sannan ta d'ago ta k'arewa matar kallo dan tun ganin farko da tayi mata taji ta kwanta mata arai.
A hankali ta bud'e bakinta ta fara magana " Sunana AAIRAH MAHMUD ME FATA "
Da sauri hjy ta kureta da idanu, domin gani take k'arya ne ace yar me fatace haka, amma ganin tsantsar kamar da sukayi da me fata yasa ta had'iye abinda take son fad'a.
" Gidan mu shine gida na uku idan kin fita daga layin nan, sannan kullum da yunwa nake kwana haka idan zani makaranta ma nake ta fiya da yunwa, idan ciki na ya kulle shine nake kuka saboda babu wanda zai bani abinci sai dai naje naci na karnukan gidan mu idan an basu, to shine da Aunty's suka gano inacin abincin kare shine suka saka muk'ulli suka k'ulle d'akin sai dai na tafi makaranta haka banci komai ba, wataran ma sai nayi kwana biyu banci abinci ba" ta k'arashe maganar tana rushewa da kuka.
Hawaye ne ya cika idanun hjy Rahma tasa hannu ta share sannan tace " To! Ina abban ki da ummin ki?"
" Ummina! Nanny tace min wai ta mutu, shi kuma Abiy kullum baya gida yana k'asar waje ni banama ganin shi sai dai inji ance yazo koya fita".
"Okay! Yanzu ita Nanny taking tana nan?"
" Eh tana nan "
" Tom! Ki kwantar da hankalin ki, zanzo gidan ku gobe insha Allah, karki damu kinji?"
A hankali ta gyad'a mata kanta.
Wani abu ta mik'a mata mai kama da cube na zobe.
" Ki rik'e da kyau kinji? Indai kikaji ance abiyn ki yazo to ki dannan nan gurin zan zo gurin shi mu tattauna kinji?"
Kallan abin take, ita Kuma tana nuna mata inda zata danna, daga baya ta mik'e tana mata bye-bye.
Bayan ta tafi Aairah ta kalli abincin gabanta taga ashema ta cinye, kawai sai ta d'auki d'ayan ta saka a leda ta nufi hanyar makaranta ranta fes.
★★★★★★★★★★★★★
Tunda hjy Rahma ta koma gida take tunanin yarinyar! Domin ga dukkan alamu yarinyar tana cikin tasku na rayuwa, a wannan age d'in na Aairah bai kamata ace tana facing wannan halin ba, kamata yayi tana jikin mahaifiyarta tana kwasar roman tarbiya.
Tunawa tayi da ranar data fara ganinta a jikin wannan bishiyar ta kwanta tanata bacci ga hawaye duk ya bushe a idanunta kashi duk tayi wani iri, ga dukkan alamu yunwa take ji! Daman unguwa zata fita ita kad'ai a mota ganin mutum a kwance yasa tayi parking, ganin halin da yarinyar take ciki yasa ta koma gida tasa aka zuba mata abinci a take away tazo ta ajiye mata tayi kuma rubutu a jikin takadda ta ajiye mata, tun daga wannan ranar take sawa ana kawo mata abinci ana ajiye mata.
Wayarta ta d'auko a cikin jaka ta Kira mijinta nan take bashi labarin Aairah da kuma shawarar data yanke akanta, farin ciki ne ya mamaye zuciyarsa dan haka lokaci guda yayi na'am da shawararta, jin ranta tayi wasai saboda har ga Allah ranta ya kwanta da Aairah.
★★★★★★★★★★★
Tana kwance da yamma lik'is a d'an d'akin da aka ware mata wanda yake bayan katafaren gidan.
Ihun yaran gidan taji suna Abiy oyoyo, fitowa tayi sad'af-sad'af ta rakub'e a jikin ginin gidan tana lek'en abiyn nata, sai da taga ya shiga cikin gidan yasa ta koma d'akinta ta zauna tare dayin ta gumi, lokaci k'ank'ani hawaye ya wanke mata fuska tasa tafin hanunta tana gogewa.
Tunawa tayi da wannan abin da hajiya ta bata, k'arasawa tayi gurin tulin kayanta da suke zube a k'asa ta d'aga wani zanin atamfa ledarta ta d'auko cube d'in.
Danna inda hjy ta nuna mata tayi ta maida abin cikin kayanta ta b'oye.
Fitowarta kenan daga wanka taji k'arar speaker din dake gefen makunnin fitalar d'akin tayi k'ara, hakan yasa ta tuna Aairah ta bawa madannin, Cikin azama ta fara shiri dan isa gidan nasu.
Sai data idar da sallar magriba sannan ta d'auki muk'ullin mota ta fito.
Hon tayi a katafaren get d'in gidan, wani basamuden gard ne ya bud'e kofa ya fito yana tambayarta gurin wa tazo.
Nan ta shaida masa gun Alhaji tazo, waya ya ciro a aljihunsa ya Kira Alhaji yana shaida masa bak'uwar da yayi.
Bud'e mata get d'in yayi yace ta shiga, babu musu ta cinna motarta ciki.
0 Comments