[Rubutun Hikaya] "TALALA" By Jazuli Ya'u Hashim

..................TALALA............... Mai kamar Sake............................ .....Written by : Jazuli Ya'u Hashim...... ......“Ai wato Hajiya, ina fad'a miki idan kayan nan suka samu isowa cikin qasar nan, a daidai wannan lokacin, za mu samu gwagwa6ar riba mai yawa, wadda ba mu ta6a samun irinta ba”. Inji Alhaji Nasiru Damisa, wanda yake zaune a qayataccen katafaren d'akin hutawar gidansa, cikin tsananin farin ciki yake sanar da matarsa Hajiya Saudatu hakan wadda take zaune a kusa dashi a kan kujera. “ Ai da ma tunda naga bakinka yaqi rufuwa, na san cewa dawalakin goro a miya, domin kuwa dalilin farin cikinka, ruwa baya tsami banza”. Qir… wayar Alhaji Nasir ta fara yin gunji a cikin aljihunsa, yasa hannu ya fito da ita waje, Musa Bala sunan da ya bayyana kenan akan fuskar wayar, alhaji Nasiru ya d'aga wayar yana murmushi ya kara a kunne “ Hello Pilot Musa!” “ Alhaji Musa saidai fa ka yi haquri, domin Jirgin da ya d'auko kayanka, gaba d'aya ya nutse a cikin teku”. Maganar da Pilot Musa ya sanar da Alhaji Nasir kenan. Cikin tsananin sauri alhaji Nasir da Matarsa suka miqe tsaye a fusace “ Jirgi ya nutse a cikin teku! Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un”. Alhaji Nasir yace hakan lokacin da gumi ya jiqa masa jiki jirgif, ya cire hular dake kansa yana fifita da ita, gaba d'aya hankalinsu ya yi matuqar tashi, a daidai lokacin ne ‘ya’yansa mata guda biyu masu qananan shekaru, suka shigo cikin falon daga waje, suna sanye cikin kayan makarantar Nursery. Yaran suka tsaya cirko-cirko a falon suka bi iyayensu da kallo cike da fargaba da kuma mamakin abinda ya faru. Nan take Alhaji Nasir ya yanke jiki ya fad'i qasa tim a tsakiyar falon, matarsa da ‘ya’yansa suka yi kansa a guje suna kuka. “ Abba dan Allah ka tashi kada ka tafi ka barmu”.Babbar tace haka cikin muryar kuka tana jijjigashi, Hajiya Saudat da Surayya suma kukan suke suna jijjiga jikinsa suna ta iface-iface. Matashin likitan da shekarunsa ba su wuce ashirin da biyar a duniya ba, ya bud'e qofar d'akin jinyar ya shigo ciki daga waje, da sauri ya qarasa inda marar lafiyar yake kwance akan gadon,. “ Wannan ai Baba Nasir ne, Docto me yake damunsa?”. Datta Lawal ya juya ya kalli Aliyu Haidar matashin likitan da ya masa tambayar, “ Haidar da ma ka san shi ne?”. “kwarai kuwa docta, amma me yake damunsa”?. Haidar ya Tambaya “ ya had'u da mummunan cutar nan ta mutuwar 6arin jiki”. Inji datta Lawal, Haidar ya matsa kusa da Marar lafiyan ya qura masa idanu. SHEKARU GOMA BAYA. “ To Alhaji Allah ya kiyaye hanya” Umman mu Karimatu tace da Abbanmu Alhaji Auwal haka, lokacin da suke tsaye a jikin motarsa dake harabar gidanmu, suna yiwa juna bankwana “ Allahumma amin Uwar ‘ya’yana” yace hakan yana murmushi, sannan ya miqa hannu ta miqo masa ‘yar qaramar jakarsa dake riqe a hannunta, ya bud'e motarsa ya shiga ya tashe ta, mai gadi ya bud'e masa get ya fita sannan ya ja get d'in ya rufe, Umman mu tana inda take tsaye tana bin motar da kallo har saida ta fita, sannan ta juya ta koma cikin falo. Qarfe biyar na Yamma aka kira waya aka sanar da Umman mu cewa “mijinta wato Abbanmu ya yi had'ari a hanyar sa ta zuwa garin Abuja kuma Allah ya kar6i ransa” Haidar dake zaune akan kujerar bayan tebur yace haka yana bawa datta Lawal labari, cikin muryar tausayi Haidar ya cigaba “ A lokacin da Mahaifinmu ya rasu ina aji uku a wata makarantar sakandire ta kud'i, da yake Abbanmu ya d'ora rai a kaina, na ganin na samu kyakykyawan karatu, yayyuna guda biyu Mata, anti Hassana da anti Nafi kowaccensu tana gidan mijinta. Bayan rasuwar mahaifinmu ba dad'ewa, sai komai ya ta6ar6are mana, talauci ya sako mu a gaba abincin da za mu ci ma, da qyar muke samu. A wannan lokacin ne muka bujirowa da Mahaifiyarmu wata tambaya, game da inda dukiyar Mahaifinmu take, a lokacin ne Umman ta mu ta sanar da mu cewa, dukkanin wata dukiya ta Mahaifinmu, tana Hannun babban Amininsa Alhaji Nasir Damisa, sun had'a dukiyarsu suna kasuwanci tare, kafin mahaifinmu ya rasu ya sanar da ita hakan. Lokacin da mahaifiyarmu ta je masa da zancen gadonmu, ya nuna shi sam bai san da wannan maganar ba, har kotu Ummanmu ta kai qararsa amma da yake akwai kud'i a hannunsa ba mu samu nasara ba, haka muka cigaba da rayuwa cikin quncin talauci, wanda sakamakon hakan ne yasa dole na bar makarantar kud'i na koma ta gwamnati, ni da ban san duk wata wahala da gwagwarmayar rayuwa ba, a wannan lokacin dole ta sa na shiga fafutukar neman na kaina, na yi aikin qarfi iri-iri a rayuwata har Allah ya kawo ni wannan matsayin”. “ Wai da ma Haidar wannan ne mutumin da ka ce ya cinye muku gadon ku” in ji datta Lawal “ Qwarai kuwa shi ne” Haidar ya amsa masa, datta Lawal ya yi shiru yana yin wani tunani, sannan ya nisa yace “ In Allah yaso ya yarda lokaci ya yi da dukiyarku za ta dawo hannunku” Haidar ya zaro ido ya bishi da kallo cike da mamaki. Bayan Alhaji Nasir ya dawo cikin hayyacinsa, Haidar ya bayyana a gabansa tare da tilin tambayoyi, wanda Alhaji Nasir di'n yaqi amsa masa, da yake sun shigo da lauya da ‘yan sanda cikin maganar, hakan tasa dole aka yiwa Alhaji Nasir wasu allurai da ake kira Narcotic test. Allurai ne da ake yiwa wanda ake tuhuma da laifi su idan ya yi taurin kai, nan take Alhaji Nasir ya fito fili ya fad'i gaskiya, ba su bar wajan ba har saida Alhaji Nasir ya yi Transfer d'in dukkan kud'ad'en su haidar na gado a account d'in Haidar d'in. Duk lokacin da Alhaji Nasir ya tuna cewa dukkan dukiyarsa ta nutse a cikin teku, sauran kud'insa na banki kuma ya turawa Haidar su, sannan ya had'u da ciwon mutuwar 6arin jiki, sai zuciyarsa ta buga sosai, a dalilin hakan ne har zuciyarsa ta fashe ya mutu............................ ..............Alhamdulillah..............

Post a Comment

0 Comments