π π π π π
*BAMISRIYA TA*
π π π π π π π
π¨π»π»π©π»π»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
WΙ ΙΚΙ Ι¦ΙΚΙ tΡ³ ΙΙucΙtΙ, MΡ³tiΡ΅ΙtΙ ΙΙ³Ι ΙΙ³tΙΚtΙiΙ³ Ρ³uΚ ΚΙΙΙΙΚΰΈ£.
___________________________________
©2019
*πDATE*
*Page 2*
*STORY BY*
_DEEN_π
*TYPING BY*
_Abubakar Saleh Al-Quyraemey_π
```@Facebook Abubakar Saleh AlQuyraemey```
~Sadaukarwa Ga Zamani Writer's Association Allah Ya Kara Hade Kanmu Ameen Ya Hayyu Ya Qayyumu.~
Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
..............Wato a yayin da wannan baiwar allah bamisiriya tace "ΞΉ¢Ρ zΞ± Π½Ξ± gΞ±Π½" Ahhh. Jinayi tamkar zuciyata ta tsaya, komai ma ya tsaya cak, kamar daga nesa sai naji ta Ζara cewa "ΞΉ¢Ρ zΞ± Π½Ξ± gΞ±Π½" sai kuma naji na dawo daidai,hakan a larabcin Masar yana nufin kana bukatar wani abu ne? nan da nan sai nayi firgigit nace da ita "ΞΉ ΟΞ± ΞΉ ΞΉΡ ¢ΟΟΞΉ" ma'ana ina bukatar shayin copi. Nan take sai tayi maza taje wajen wannan na'ura ta matso min shayin copi ta mikamin,sannan ta kawo min sugar koda zan Ζara.
Na dubi fari wannan sugar sai naga yana mani kamamceceniya da farin idanun wannan yarinya, yayin da launin ja na jikin wannan copin na ga yana min kamanceceniya da labban wannan yarinya, duk da cewar kuwa ba jambaki ta saba haka labban nata suke min indillahi.
Sai kwakwalwata ta debe tunani na da kuma nutsuwa ta izuwa shawagi mai tsayi na jinjinawa izuwa ikon Allah da hikimarsa da fasaharsa, wajen Ζera wata halitta mai gigita sauran halitunsa, firgigit na dawo hayyacina kasan cewar kaΙan daga cikin ruwan copin nan ya zuba mani a gwiywata, domin na rike inata tunani har copin ya Ιan tangaΙe daga hannuna.
Sai na zauna inata kallon ta bance komai ba ita kuma tana can gefe taci gaba da karatunta, can tana cikin karatun sai ta dago sai muka hada ido sai nayi sauri na kauda kaina haka mukayi har wajen sau biyu can tace dani "Ξ±ΠΈΡΞ± ΠΌΞΉΠΈ ΡΠΈ" [ma'ana daga ina kake?] ban amsaba sbd bantaΙa tunanin dani take ba, sai ta Ιaga murya tace min "ΠΌΞΉΠΈ ΞΉΠΈ Ξ±ΠΈΡΞ± ΡΞ± ΠΊΞ±fΡΞ±ΞΉΠΈ" to a nanne na fahimci cewa dani take, sai naji cikina ya dauka kululuuuuuuu.
Cikin sauri nace Nigeria cikin murmushi tace "Ξ±H Π½Ξ±ΡΞ±ΠΈ ΠΈΞ±Ρ" [ma'ana mutanen kirki] wannan ta´ada ce ta mutanen masar yayin da suka tambayeka ka fada masu sunn kasar ka sai suce ma "Ξ± Π½Ξ±ΡΞ±ΠΈ ΠΈΞ±Ρ" "Ξ± Π½Ξ±ΡΞ±ΠΈ ΠΈΞ±Ρ" abunda ya dunga dawo min kenn a cikin kwakwalwata.
Yayin da takoma taci gaba da karatunta nikuma wannan kalmar wato "Ξ± Π½Ξ±ΡΞ±ΠΈ ΠΈΞ±Ρ" ta dinga dwo mani a cikin kwakwalwata raina yana mani dadi, sannan zuciyata tace dani "Da wnn damafa aka baka" nan take kuwa sai na fara shan shayina harna shanye cikin natsuwa da jin dadi ina gamawa sai na Ιago hannuna na duba agoggon dake a hannuna naga 7:50am, to wannan ce damata, ta minti goma gareni domin na samu nayi tasiri a tunanin wannn yarinya na samu nasara a gare ta. Duk wannan surutai ina yinsu ne a cikin zuciyata.
Nan take cikin gaggawa na Ιauki wannan copin naje na kaimata, duk da cewa bisa tsari ba kaimata copin ake ba mutum bari yake a gurin in yaso daga baya sai tazo ta Ιauka taje ta wanke, to amman dai nakai mata ita kuma ta karΙa, nan taje ta fara wankewa a inda take wanke wa, bayan ta gama ta dawo ta zauna, sai na tsaya ban tafi ba sai na ce "βΞ±Ο
ΡΞ± ΠΌΞ±Ρ ΡΟ¢Ο
ΡΡ ΠΌΡ" da jin haka sai ta buga wani uban murmushi kyanta ya kara fitowa, sai naji zuciyata ta narke, ita kuma a Ιangaren ta larabcin dana yi shine ya bata dariya kasancewar dagaji kasan dan koyo ne musamman yanda nayi Ζafar ungulu da kan zabo na faro da larabci na kare da turanci sai ta bude baki tace "fΞ±∂∂Ξ±β" Yayin da takarashe maganar ta da wani murmushi mai narkar da zuciyar masoyi.
Na bude baki zanyi magana kenn sai ga jirgin mu nan ya iso, kuma yanda abun yake in har muka rasa wannan jirgin to dole sai mun jira jirgin karfe *10:00am*.
Kawai sai naji abokina Hizbullah ya kwalo mani kira "kai wai tun dazu meye kake yi ne haka❓jirgi yazo kazo mu fece", kash!!!!.
Ni banma san sun dade da dawowa ba ashe suna zaune sunata hirarsu kamar yanda suka saba.
Nan take naji kamar an watsa mani ruwan zafi irin tafashashshen nan, naji ina ma ana iya tariye lokaci dana tariye wannan lokacin, naji ina ma nace wa abokanai na sutafi su barni, nasan wata rigimar ce zata taso kasancewar nina matsa masu cewa lallai ayi wannan fita, kawai sai maganar tata ta juyo mani da akalar hankalina izuwa gareta yayin data cemani
"Ξ±ΞΉ ΟΞ± fΞ±∂∂Ξ±β Ξ±ΠΈΞ± ΞΉΡΡΞ± ΠΌΞ±'Ξ±β"
[Ma'ana inajin ka], a daidai wannan lokacin ne sai naji bani da wani abokin gaba daya wuce barin wannan wuri, domin bana son na tafi na barta a wannan lokacin, kwatsam sai naji a zuciyata tamkar na tsaida tsawon shekara *100 years* a wannan waje.
Banyi aune ba sai naji hawaye suna zuba a idanuna, yayin da ita kuma tayi tsaye tana jiran meye zai fito daga bakina, banyi auneba sai naga yanayin damuwa ya bayyama a fuskarta, kasancewar taga na shiga wani yanayi mai huda zuciya, na buda baki zanyi magana amman maganar taki fitowa, gashi abokanaina sai azalzalata suke.
"Kai hamago idan bata da changi kabari idan mun dawo kazo ka karba haba" acewa Hizbullah.
Yayin da kamala yace "shifa daman ya iya bata wa mutane lokaci wannan hamagon".
Bansan mai ya shiga jikina ba naji na juya naci gaba da tafiya amman zuciyata tana cemani tabbas inda rabo wata rana jamu sake haΙuwa, tayuwu ma idan mun dawo da daddare muhaΙu da ita a wajen.
Na shiga jirgin na zauna, jirgi ya fara tafiya sai na Ιago idanuna na kalleta domin nayimata kallon karshe amman ga mamakina, duk wani annuri na fuskarta ya dusashe, kamar ba ita bace dazu take mini dariya ba. Sai naga kamar a mafarki wani abu a fuskarta makamancin abunda yake juba a fuskata hawayene yake zuba daga idanunta ko meyasa ?
Muje zuwa..........
*Abubakar Saleh Quyraemey*
```{Young Writer}```
0 Comments