🌺🌺🌺
*_SANADIN HIV!_*🙆🏻
🌺🌺🌺
~_A Short & Fiction Story_~
*By*
*Jamaal Datti*
Wattpad@Jhermaal0809
~_Dedicated to my sis *Ummul~Khairi*_~
*5💖6*
*Not Edited*
_Bismillahir-rahmanir-raheem_
*_Beauty tips: Natural Toothpaste_*
_ina maza da mata? Uwargida da amarya, kai yaro da babba ku fito gafa dama ta samu! Shin kin kasance daga cikin masu yawan brush kullum da safe da dare amma har ilah yau Baki rabu da bashin bashin baki ba? Ko kuma bakin ki yai ta shi daga can karshen bakin! To fah in kaima ka kasance haka ga hanya mafi sauki dazaku haɗa natural toothpaste nan cikin karancin kudi dako naira hamsin bazaku ka sheba. Gishiri cokali biyu, ɗanyar citta 'yar karama, sai rabin lemun tsami. Ki fere cittarki ki jajjagata a turmi ko kuma ki niƙeta a grater, firstly zaki saka gishirinki a ɗan mazubi sai ki matse ruwan rabin lemun tsaminki a ciki ki jujjuyashi sa'annan kisa ka niƙaƙƙiyar cittar ki a ciki a sai ki hade su guri guda da kwaɓaɓɓen gishirin nan, sai ki dinga sawa akan brush dinki kina wanke baki dashi bake ba tashin baki musammam in kika hada da cin aswaki👌🏼_
Islam da hanzari ta matsa daga jikinshi tace "pls kar kasoma ɓatamin kwalliyata daka barni da abinda ke damun zuciyata kuma ka.....
Da sauri Fu'ad ya tari numfashinta yana me cewa "babynah meke damunki?" Hadi dasa yatsansa manuniya na hannun dama ya ɗago habarta ya tsira mata idanu kamar me son karanto damuwarta daga cikin ƙwayar idanunta.
Kawar dkai gefe Islam tayi sannan ta bude bakinta cikin raunin murya tace "baby ina ji a jikina wani abu mummuna na tunkaro rayuwata tun kwanakin baya amma na safiyar yau yafi cimin tuwo a kwarya domin zuciyata kamar ana mun luguden daka sbd fargaba!!!
Fu'ad ko cikin dariya da mayar da saka maganarta cikin mizanin wasa yace ko dai har kin fara fargabar first night ɗin mune? To kwantar da hankalinki kamar kin kashe dan sarki domin ni Fu'ad na ɗaukar maki alƙawari bazan yi mawa amaryata Islam komai ba a daren farkon mu.
Cikin muryar shagwaba Islam tace "baby ba wannan bane, abun is so weird that I cant point a finger at it! Inaso kai min Alƙawari komai rintsi ko mai wuya kana tare dani, duk abunda zan riska zaka tsaya mu yaƙeshi tare dani dakai har muyi galaba a kanshi!?.
Haba babynah babu wani abu mummuna dake tunkaroki illah alkhairi a rayuwarki, kawai tension ɗin rabuwa da familyn kine. Idan ma wani abun ne inah ƙara jaddada maki nayi alƙawari duk wuya duk rintsi ni ɗin nakine har abadan abada, okay? ya ƙarashe mata cikin rausayar da kai alamun ta gane?
Dukkansu ajiyar zuciya suka safke, nan kuma shiru ya kara ratsawa a tsakaninsu.
A ɓangaren Fu'ad kalamanta duk sunsa jikinshi yin sanyi, ɗaurewa kawai yai tare da nuna cikakkiyar jarumta ta mazan ƙwarai bai bayyana a fuskar shi ba.
Amarya Islam kuwa takurewa tayi a jikin murfin mortar ba abin da take nanatawa a ranta face انا للله و انا اليه راجعون, domin itace kawai mafita a gareta da kuma addu'ar koma mene ne ke tunkaro rayuwarta Allah ya bata ikon juriya da kuma rinjayi, indeed she trust her instincts.
Fu'ad ya bude baki kenan da niyayyar ƙara rarrashinta da kuma ban baki sai ya jiyo karar ham daga abokinsa Abubakar (shine wanda ya tuƙosu zuwa wajen dinner ɗin) na dannan musu ba ƙaƙƙautawa, ashe sun daɗe da isowa gurin amma basu farga ba.
Daidaita nutsuwarta Amarya Islam tayi domin kada kwalliyarta ta ɓaci, Fu'ad ne ya fara fitowa ya zaga yo gefenta ya buɗe mata, ziro zararan yatsunta tayi wanda ya ƙawatu da zanen fulawa/dayis/lalle zallar ja ba mix din baki hakan ya kara fito da kyawun hannun, hannunshi ta rike kana cikin tafin hannunta kana ta ziro ƙafarta dake sanye cikin high heel daya zauna zam_zam da taimakon belts dinsu sannan ta fito _hmmm cancaɗi, sarauniyar mata kenan_.
Jerowa sukai kan wani lallausan red carpet dake shimfiɗe tun daga parked motarsu har izuwa bakin hall ɗin, Fu'ad shima sanye yake cikin armani white suits and sauran accessories ɗin maza duk blak ya saka like his princess amarya Islam. Flower gals ne a gaba da bayansu duk sun sha kyau sai watsa jajayen flowers suke masu fitar da ni'imtaccen ƙamshi. Hmmmm
Nan fah dj ya sakar musu haɗaɗɗen sauti domin farincikin ango da amarya m.c kuma sai koɗasu yakeyi, mutanen gurin kuma in banda tafi rafff-rafff ba abinda akeji domin couple to be ɗin sunyi kyau Masha-Allah!
JamaalDatti👌🏼
0 Comments