[Hausa Novel] Sanadin HIV Page 3-4 By Jamaal Datti

🌺🌺🌺

*_SANADIN HIV!_*πŸ™†πŸ»

                    🌺🌺🌺

~_A short and Fiction Story_~







*By*

*Jamaal Datti*






Wattpad@Jhermaal0809





_Dedicated to my sis *~Ummul~Khairi~*_





*3πŸ’–4*





*Not Edited*






Haka dai su kaita janta cikin wasa da dariya,  itako Amaryar tak ba tace musu Ba sai dai ta saki wani  shu'umin sanyayyen murmushi mai kashe duk wani mai kallonta.




8:00pm daidai tsantsara²n motoci su kazo domin tafiya Dinner da aka shirya ta bangaren dangin ango dana amaryar, shima dai angon akwai masu gidan rana a tare dashi.



Kawayen amarya aka fara kwashewa kamar dai yadda akeyi, shakikan kawayen ta ne kawai aka bari zasu taho tare wato SK da Fatima dama dai sune na kut da kut din, ita Fatima a unguwar Nasarawa suke da zama halinta abin a yaba ne cox bata shiga shirgin daba nata ba sai dai fa akwai dan banzan surutu, ita haka take.



ita kuma Maimuna wato SK (silent killer)  a unguwar sharada suke da zama, iyayenta ba masu shahararren kudi bane sai dai rufin asirin Allah daidai gwargwado amma ita ta daura ma kanta kwadayi da dogon buri, in dai bakin zauna da ita sosai ba to pah kallan shiru² ake mata, amma fa ta bangare guda akwaita da kadifiri harda shedana duk ta gwanance. Kawarsu kuma ta boye musu mijinta ne  saboda yau take so ta musu  surprise, wannan Kenan.



Kara gyara kwalliyar fuskarta make-up artist din tayi, sannan tai mata nadi da head dinta, sanye take cikin wata bridal readymade gown wacce daga tsakiyanta ta tattare sosai, bayan kuma ya bude sosai tare da tsawo sosai har yana jan kasa, saman rigar a dame yake sosai sosai that showed her attractive figure, kalar rigar white ce, takalmin data saka high heels ne mai belt shima black ne, sai wata fashion jewelry mai adon black stones, kai duk wani accessories daya danganci kyale-kyalen mata black ta sanya irin su bungles, zobuna etc.   Hakan  ba karamin kyau tai ba a gown din.


Harabar gidan suka fito, Fatima sai iya shege take mata tare da tsokanarta itako wani abin ma ba jin take ba saboda  tensions din dake  dankare  cikin  zuciyarta .



Wata Benz suka  nufa  new  model da aka  kawata ta  furanni masu kyau   daga  ganinta  kunsan   event   za aje. Cikin motar  ango  *Fu'ad*  hakimce a  ciki  domin  tafiya  da  amaryasa  gurin  dinner . Sk  ce  ta  bude  mata  murfin  motar  gidan baya  suka  dannata a ciki 🀣  kana suka rufe mata kofar,  su kuma hau  wata  Mercedes new model  ta  abokin  angon  kawarsu ,  duk drivers in  suka  yi  masu  key suka  harbata kan titi . Harabar gidan a  dade take  illah  mai gadi sai kuma sauran masu aiki da  basu  kammala nasu  ba aka  bari  kawai a gidan  domin duk wani  mai ruwa tsaki  a  bikin  sun wuce,  har da su teemash  na  hango an  cakare  a  gaban mota 😺



A motar ango da amarya kuwa, shiru sukai domin kowa da tunanin da yake a zuciyarshi, a bangaren amarya kuwa gabantane keta faduwa tun safiyar yau tarasa dalilin hakan, a wani bangare kuma sai ta daukeshi a matsayin alhinin rabuwa da iyayentane dake tunkarota gobe idan har Allah ya kaiku, shiyasa yau tazama so silent kamar ba *ISLAM* dinta ba.



Shi kuma a bangaren angon kamshin perfumes collection dinta ne ke fisgar shi har ya fara fita daga control in shi, ba zato ba tsammani taji kawai ya jayota izuwa ta fado kan faffadan kirjinshi atare suka sauke wata nannauyar ajiyar zuciya.



Hannunsa yasa ya fara shafa gashin goshinta da ya fito ya kwanta luf-luf baki sidik dashi, cikin sanyayyar murya yace  babynah kinyi kyau fah da yawa kuma ni banaso gardawan gurin nan su kallemin ke,  in ba"ai sa'a ba saidai aga na janyeki a gurin ko kuma kawai mu fasa zuwa domin bazan iya jurewa ba ko kadan wlh.



Wani lafiyayyen murmushi ta saki kana tace baby taron fah na yaune kawai, kaima kasan da ra'ayina kabi da atleast sai munyi party πŸŽ‰ kamar guda biyar haka dinnan.


Babynah kishin ki yasa na hanaki yin events da yawa wannan ma dankin matsane kuma suma can gidanmu sun matsane da yawa saisa, amma wannan kwalliyar taki is too over ki bari in rage miki ko kadan ne ya karasa cikin kallon soyayya tare da kashe mata ido guda daya. ❤️ ❤️ ❤️ ❤️ ❤️ ❤️ ❤️ ❤️ ❤️








_Ya kuka jishine? ga numbata domin jin ra'ayinku 08141251537_







JamaalDattiπŸ‘ŒπŸΌ

Post a Comment

0 Comments