*-GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJI SAMMAI DA KASSAI DA YA BANI IKON FARA RUBUTA WANNAN NOVEL DIN LAFIYA ALLAH KA BANI IKON GAMA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA-*
*Page 1*
Hankali a tashe duk sukayo cikin ɗakin babu abinda ke tashi a ciki sai sautin nishinta ga gefen gaďon duk jinin da dukkan alamu amansa tayi.
Da gudu Hajiya Habiba tahu kan gaďon tare da ɗago ta ɗaga ƙwancen da take sannan ta fara magana ciki tsananin damuwa " me yake damunki ne? tunda kika shigo cikin ɗakin nan ki ke kuka gashi abin har ya ke da aman jini so kike ki kashe kanki ..........bata samu damara ƙarasawa ba sabida yanda numfashin yarinyar ya ɗauke lokaci guɗa
Cikin tashin hankalin Alhaji Sani ya matso gare su wanda tun shigowar su ɗakin bai ce komai ba ya taɓa kirjin ta ya sa hannu sa akan hancin ta amma duk da haka bai ji alamar numfashi ba ɗaukar ta yayi gaba ɗaya yayi waje da sauri cikin tsananin damuwa yana kwallawa get man din su kira da ya bude masa get ya sata a mota sannan ya zagayo ya shiga Hajiya ta shiga su kayi asibiti da ita.
suna zuwa likitoci su ka kawo mata ɗaukin gaggawa, sintiri su ka fara a baƙin ɗakin da aka shiga da ita
sai bayan awanni sannan likita ya fito daga ɗakin ciki sauri Alhaji Sani ya je gare shi yana tambayar likita " likita ya ake ciki? me ya faru? ta tashi ne?". yayi tambayoyin cikin ruɗewa.
Dr jamil ya kalle shi sannan yace " ina son ganin ka a offiec" da sauri yabi bayan shi dan kar ya ɓace masa yana shiga, shima yana biya dashi a baya sai dai ya zauna kana ya nuna mai siti din kusa dashi yace " zauna Alhaji. sannan Dr jamil ya kalle shi ya fara magana cikin muryar sa mai sanyi yace" Alhaji kayi haƙuri da abinda da zan fada maka domin yarinyar ka ta na buƙatar taimakon ka tayi rashin wani abu wanda yake damunta har ta saka shi cikin ranta shine ya haifar mata da matsala babba domen yanzu haka da muke magana da kai ciwon zuciya ne ya kama ta kuma a ko wanne lokaci za ku iya rasa ta, lallai duk abinda ta ke so toh a yi mata shi wannan shawara ce daga gareni dan Allah a taimaka a kiyaye ɓacin ranta, domin tana cikin wani hali, yanzu muyi nasara ceto rayuwar ta da yarda Allah..
Alhaji Sani wanda tunda likita ya fara magana ya shiga cikin wani irin hali mai wuyar fasarawa da ƙyar ya buɗe bakin sa " yace toh Dr Jamil na gode sosai Allah yasaka da Alhaire" ya bashi hannu su kayi musabaha sannan ya tashi ya fita.
Duk abinda ya faru tsakanin Dr Jamil da Alhaji Sani, Hajiya Habiba taji domen ta biyo bayan su lokacin da Dr Jamil din yace a biyo shi.
Yana fitowa ya ganta a zaune ta haɗa kai da gwiwa tana kuka kamar ranta zai fita da sauri ya matso kusa da ita yana tambayar ta mai ya faru me yake damunta menene matsalar? Duk lokaci daya ya watsu mata wannan tambayar,
Da hawaye fal idon ta ta ɗago ɗaga ɗir kushen da take, ta kalle shi tace" yanzu Alhaji yarinyar tawace ke da ciwon zuciya?"
Ƙureta yayi da idanu yama rasa me zai ce mata, sabida ya santa aƙawai ruɗewa.
" Alhaji magana fa nake, kace min wani abu dan Allah?."
Da ķar ya buďe baķin sa yayi magana da "a Eh ita ce,
Tafe yake a cikin motar sa babu abinda yake tashi a cikin ta sai karatun Al ķur áni mai girma.
Wayar shi ce dake gefen sa ta fara tsawa wanda dama an kira ta babu adadi
Cike da kosawa ya daga wayar bakin sa ďauke da sallama abinda aka faďa masa a cikin wayar ne yayi mugun daga hankalin sa ya saki sitiyarin motar da mugun gudu motar tayi kana wani Almajiri da ke zaune bakin titi yana bara........
Tunda ta farfaď o take faman kuka da sambatun ambaton sunansa, Dr jamil da iyayen ta sai lallashin ta sukeyi amma taki sauraran kowa a cikin su Hajiya Habiba ce ta matso gareta ta daga hannu kwasheta da mari sannan ta suma magana cikin daga marya da tsananin baci rai
" toh ki kashe kanki tunda babu wanda ya isa dake,yarinya duk kinbi kin daga mana hankali ce miki akai so hauka ne?koke kaďai ce macen da tafara soyayya?
Bata karasaba sabida yanda muryar ta take faman rawa idan kuma ta cigaba toh lallai ita ma kukan zatayi ita kanta tusayin yarinyar take ji tasan dole hakan ce zata faru,
A matuk'ar razane yarinyar take kallon ta wai yau Anty ce da kanta ta daga hannu ta mari fuskar ta mai daraja abinda tafi kauna a duk sassan jikin ta
Lallai yau ta kai ta mak'ura,
Amma ya zatayi da abinda take so ba fa ita ta durawa kanta ba wannan kaddarar tace,
*TOH FA WANNAN LABARIN YA ZO MUKU DA SABON SALO DOMEN LABARIN SOYAYYA DA TUSAYI DA KAUNAR JUN DA RAKON AMANA TUN DAGA YARINTA AKE FAMA HAR KA WO GIRMAN SA A KAWAI RAKICI BABBA AKAN WANNAN SOYAYYA KAR KU BARI A BAKU LABARI*
0 Comments