π»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈ
SUHAIMA ( Yar Sarki ce)
π»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈ
*NA*
*Shafa'atu* *Muhammad*
( *Beauty* *Beby*)
*Yar* *Mutan* *Kebbi*π³π¬
ZAMANI WREITER'S ASSOCIATIONπ€
____________________________________
We are here to educate motivate entertain our readers
_____________________________________
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
1/JUNAURY/2020
*DUK* *KAN* *GODIYA* *TA* *TABBATA* *GA* *SHUGABANMU* *ANNABI* *MUHAMMAD* ( *S.A.W* )
*LOKACIN* *DA* AKA SAU *KAR CEWA QUR'ANI YACIKA SAHABBAI SAI MURNA SUKE SHIKO SAYYADINA ABUBUKAR SAI YA KOMA GIDA YANA KUKA SAI SAHABBAI SUKA BISHI SUKA TAMBAYISHI SABO DAME YAKE KUKA SAI SAYYADINA ABUBAKAR YACE TUNDA KUKAJI ANSAUKAR CEWA QUR'ANI YACIKA. TAU MANZON ALLAH (S.A.W) YAKUSA WAFATI SAI SUKAJE SUKA TAMBAYI MANZON ALLAH (S.A.W) YACE HAKANE SAI SUMA SUKA KAMA KUKA ALLAHU'AKBAR WANNAN TUNA TARWANE YAN UWA ALLAH YA *SAMUDACE AMIN** π
*Wannan* *Novel* *nawa* *na* *sadaukar* *da* *shi* *ga* my sweet mum dina Khadija love uπ₯°
*BISMILLAHI* *RAHAMANI* *RAHIM*
*3* & *4*
Rarrahin Innaro ya farayi amma taki yadda da shi dole saiya fitar da yarinyar, haka ya fita ya koma dakin Ma'u ya gayamata yadda su kai yi da Innaro kuka ta dingayi harda majina, hakuri yake bata da kyar tayi shiru yace daina kuka yanzu zanje na fadawa Malam Musa idan yaso yazo yayi mata magana ko taji toh Ma'u tace ta dauki jaririyar ta Goya ta a baya shi kuma Malam Garba ya fita yanufi wurin Malam musa da isar sa ya iske bayanan, ya tambayi mutanen gurin suka fada masa ya shiga gida.
Yaro ya aika yayi Sallama dashi yana fitowa yayi masa bayanin yadda sukai da Innaro, hakuri ya kara bashi sannan yace suje ko zai jarraba tashi nasihar ko zataji, suna isa gida suka shiga sashen Innaro tana ganin Malam musa ta washe baki tayi masa sannu da zuwa amsawa yayi rai a sake tayi iso har rumfa sannan ta kawo masa ruwa mai sanyi yasha.
Gaisawa sukai sannan Malam Musa ya fara kora mata bayani, kamar haka, kamar yadda kika ganni a gidannan Innaro alfarma nazo nema a gurinki "Dan Allah Innaro kibar Garba ya rike wannan jaririya, "kai Malam Musa oho zuwa yayi ya fada maka qarya da gaskiya to wannan shegiyar Yarinyar ba'a gidannan ba wlh, " haba Innaro taya zakice mata shegiya bayan ba'a san iyayen taba Malam Musa ne yake magana cike da damuwa a fuskar sa, yau Malam Musa inba shegiya ba wadansu iyayene zasu haifi Yarinya su ajjeta a bola, a'ah ba haka bane Innaro kowa da gaddararsa a rayuwar sa, inajin sato yarinyar nan akayi aka jefar Dan Allah Innaro kiyi hakuri kibar yarinyar nan takai ko da shekara goma sha shida ne a lokacin tayi wayo inyaso sai ta nemi iyayen ta da kanta, da kyar da sidin goshi Innaro ta yadda, shidai Malam Garba yana tsakar gida yana jinsu, godiya Malam Musa yayi yasa hannu a aljihu ya fito da dubu daya ya bata, tana washe hakora ta karba tayi godiya sannan tace dashi ya gaida gida, fitowa yayi suka wuce cikin gida gurin iyalan sa suna shiga lami ta fara bala'i da zage2 munafukai ko mai ya kawosu ko anzo munafurcin da aka saba ne ko kulata basuyi ba suka shiga dakin Ma'u.
Gaisawa sukai Malam Musa ya karbi yarinyar yayi mata addu'o'i sannan yace da Malam Garba wani suna kuka saka mata.
Sai alokacin suka tuna basu samata suna ba, Ma'u ce ta sunkuyar da kai tace "ina Neman alfarma Malam a gurin ka, " wata alfarma ce Ma'u fadamin kowace iri ce indai batafi qarfina ba zanyi miki ita, godiya tayi sannan tace " dama sonake asaka mata sunan Mahaifiyata. Farin cikine ya cikasu su duka Malam Musa da Garba sai shi mata albarka sukeyi a take a gurin Malam Musa yayi mata huduba da sunan mahaifiyar Ma'u wato(AISHA HUMAIRA )suna kiranta da (SUHAIMA) .
Tun daga wannan lokacin rigima takulu a gidan Malam Garba Ma'u bata da ikon fitowa tsakar gida sai Malam Garba yana gida, lami kuwa da yayanta kullum suna gudure da niyyar dauke yarinyar suje far da ita.
A haka rayuwa tace gaba da tafiya a gidanna Malam Garba dadi da badadi.
Kuma a yau ne SUHAIMA tacika shekara sha shida cif da haihuwa inda Malam Garba ya sanyata a makaranta allo da na boka, kullum Malam Garba ne zai kaita ya daukota saboda masifar lami.
**shin wanene Malam Garba*
Malam Suleiman yana da mata daya mai suna Hajara(Innaro) wadda ta kasance bata haihuwa ga masifa da San abin duniya arashin haihuwar ta ne yasa shi qaro aure inda ya aure kanwar abokinshi, mace mai tarbiyya, ga hankuri gakuma sanni yaka mata ga son mutane babu ruwanta watan uku a gidanna ta samu ciki zo kaga murna gurin ta da Mijin ta, tun daga lokacin Malam Sule yake bata kulawa ta musamman dalilin haka ne Hajara ta tsani Khadija, haka suka cigaba da rayuwa dadi da rashin sa inda cikin khadija ya tsufa haihuwa yau ko gobe.
Wata ranar laraba Khadija ta tashi da naquda cikin ikon Allah ta sauka lfy inda ta haifi santalelen yaron ta namiji.
Da labari ya iske Hajara Khadija ta haifi d'a namiji kamar ta hadiye zuciya ta mutum, tun daga wannan rana Hajara ta tsani Khadija da d'anta, a kwana atashi babu wuya gurin Allah yau ne sunan Khadija inda yaro yaci sunan ABUBAKAR, amma suna kiransa da Garba.
A haka rayuwa tacigaba da tafiya inda yau Malam Suleiman ya tashi da shirin tafiya birni domin sayar da wasu kadarorin sa dan yana son dansa yayi karatu.
Sallama yayi da iyalansa ya kama hanya ya fita, tunda ya fita Khadija gabanta yake faduwa.
Bangaren Malam Suleiman kuwa yana fita ya wuce gidan abokinsa dama tare zasu tafi da isarsa shi yake jira, bashi hannu yayi suka gaisa sannan suka kama hanya zuwa tasha, suna isa suka iske saura mutum daya ma motar ta cika, haka mota ta tashi, tafiya sukeyi cikin natsuwa, sunje dai2 wani hanyar da zasu sha kwana sai ga wata qatuwar mota ta bigi tasu motar.
Bugar ta keda wuya motar ta kifa ta dinga juyi har saida ta shiga wani daji babu shiri aka kira ambulance aka ciro wadanda suka mutu wanda suka ji ciwo aka tafi da su asibiti gaba dayan su.
(Allah sarki Allah yasa mu cika da kyau da imani yan uwa Amin)
Veto and share
Comment
*Mmn Beby ce*π₯°
0 Comments