https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*MATAN MU AYAU*
🆕2020
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*
____________________
📝 .
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ t ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร
_______________________________
LABARI:
__________
*ZEESA MUHD (MUM NIHAL)*
SADAUKARWA
__________________
*GA KUNGIYAR ZAMANI INA AlFAHARI DAKU A DUK INDA KUKE*
KIRKIRARREN LABARI NE.
*BISMILLAHIRRAHAMANIRAHIM*
________________________________
1⃣➡5⃣
"Nifa ka takuramin tun dazu sai mita kake uwa inyamiri"
Cewar wata matashiyar mata data ke kwance a kan doguwar kujera
"Haba Zahra ya kike so nayi? Kina kallo tun safe zan fita nema bazan dawo ba sai magriba, Amma ace bazan hutaba, Dasafe kamin na fita bazan samu abinda zanci a gida ba,Sai kice min bacci bai ishe ki ba,Nadawo din ma bazan samu abinda zansa abaki na ba,Kece kullum kafa a titi saboda karki zauna kiyi girki kici, Yakamata kiyi tinani ko haka kika ga anayi a gidan ku eye"
"Kut me kake nufi Umar? Zagina kake kome? To banyi niyyar yiba, Ni kenan kullum aiki babu hutu, Kana gani ai makociyata har me aiki mijinta ya dakko mata saboda yana son ta, Am.... "
"Ya isa Zahra, Wai me kika dau kanki ne kina abu saikace wata karamar yarinya, Dakike batin Aisha dani da mijinta dayane iyi? Ko samun mu daya? Kinsan dai Yafini karfi ta ko ta ina, Narokeki ina hadaki da Allah ki canza Kafin lokaci ya kure miki"
"Yo to kai meya hanaka kaima kayi kudin? Konice nace kazama matsiyaci kana kallo dai irin hakurin danake agidan nan, Dubeni ace kamar ni wai a wannan rubabben gidan nake rayuwa, Abin kunyane aguna yasin mtss Allah nayi danasanin aurenka dan....
" Allah yashiryeki yasa kigane gaskiya ki sauka daga keken beran dakika hau"
******************
"Assalamu Alaykhum"
Cewar wani wata'yar dattijuwar mata
"Wa'alaykhsalam Sannu dazuwa Innah"
Fadin matar gidan da'akayiwa sallama
"Yauwa Sannu Zainab, Ke kadaice agidan naji babu Hayaniya? "
"Eh Innah yanzu suka tafi islamiyya kinsan dayake yanzu anyi hutun bokon saboda kirsimeti"
Nan tashigo suka gaisa kana takawo mata abun motsa baki kana Innar tadora dacewa
"Dama nazo nagayamiki sakon malaman makarantar Zadul-Mar'at"
Nanta Fiddo wani kati a jakarta ta bata
"Masha Allah kice abin har yazo haka? Tom Allah yakaimu"
"Naji suna cewa zakiyi musu lacca akan aure a musulunci duba da yadda muka dauki aure a wannan lokacin"
Nan suka cigabada Tattau nawa akan wannan batu kana tayi mata sallama ta huce.
********************
"Zahra Dan Allah kamin na dawo ki daure kimin tuwo, Yau natashi dason cin sa kinsan nadade banciba, Dan rabona dashi tun agidan Innah damukaje"
"Lallema Umar samun wuri, Dan kaci sa'a zanyi girkin shine har kanada wani zabi naka, To wallahi idan kai wasa bazanyi ba, Mai zai hana kaje gidan Innar kaci dan wallahi banga wanda ya'isa yasa nayi masa tuwo a gidan nan ba"
Nan taci gaba da babatun ta duk akan yace tayi tuwo, Itakuma ta dage bazatayiba
"Tom Nidai nafita sai nadawo amin addu'a mosoyiya"
Yafada cikin sugar zolaya
"Idan ma makiyiyace ba damuwa na bane tuwone dai bazanyi ba, Sannan Inkafita kar kadawo, Dazake nayima addu'a me kake tsinanamin dazan bata lokacin gurin yima addu'a kamar mara aikin yi? To wallahi bazan ba ehe"
Takarasa cike da masifa
Shikam tuni yafice Dan yariga da yasaba da halayyar ta Zahra.
Zeesan kuce📚📝😍
0 Comments