(Littafin yaki) Maalikus-saif By Abubakar Saleh Al~Quyraemey, Part 1

*⚔MAALIKUS-SAIF⚔*
    _{Littafin Yaki}_

                     
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​

______________________________________
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร
______________________________________



*Writing by:*
_Abubakar Saleh Al~Quyraemey✍_
___________________________


_Book One_
  _______





  *Page 1*


Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki da manzon sa Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi, wanda ya bamu iko ga jama'a domin su samu abin ɗebe kewa da nishaɗantarwa yayin karantashi.

     Shi wannan littafin, fassarace daga harshen larabci zuwa na hausa domin jama'a su amfaneshi. Shi wannan littafi mafi yawancin mutanen yanzu basu sanshi ba, domin Malamai ne ada suke karanta wa jama'a shi idan sunajin nishadi. Zakuji cewa Wannan littafin ya kunshi labaran soyayyaya, nishadi da kuma abubuwa iri daban-daban, wadanda suka kunshi sha'anin bokanci da tsafe-tsafe wanda mutanen wancan lokaci suka kware a kai. Za kuma aji yadda rayuwa take kasancewa ga wannan sarki, tun tasowar sa da kuma girmansa, kama izuwa lokacin daya zama kasaitaccen Sarki da kuma mutuwar sa. Kuma za aji cewa wannan littafin ya shafi bangaren addini da kuma ma'amaloli na rayuwar alumma.
halakata. MAALIKUS-SAIF Bin ZIYAZINUN a karan kansa an taba samu rayuwa irin tasa. Idan muka duba tarihin masarautar BORNO zamu samu cewa daya daga cikin wadanda suka taba yin sarauta a wannan masarauta wadanda akeyiwa lakabi da Saifawa Dinas (Wato Daular Saifawa), tayi kimanin Shekara dubu kafin ta gushe, wannan zuria ta saifawa sun samo sunansu ne daga wannan babban Sarki kuma kamar yadda tarihi ya nuna shine ya kafata. Don haka labari da aka bayar akan wannan Sarki SAIF yana iya zama kirkirerren labari ko kuma shi Sarkin ya zamto antaba samunsa A hakikama yankin da wannan sarkin ya zauna wato HAMRA'U YAMEN ko YAMEN wato kamar yadda wannan littafin tarihin ya nuna.




★.★.★.★.★.★.★.★.★.★.★.★.★.★



    A wani zamani mai tsawo daya wuce, zamanin Annabi Nuhu {Alaihissasatu wassalam} yayi wa 'ya'yansa addu'ar Allah yasa daya daga cikin 'ya'yansa a samun wanda zai mallaki duniya ya kuma yada addinin Allah. Cikin ikon Allah sai wannan addu'a ta sa ta fada akan babban dansa SAMU, wanda shi SAMU a wannan lokaci zuriyar sa farare ne {larabawa}, shikuma karamin dansa HAMU zuriyar sa bakake ne.

    Bayan sun bar wajen Mahaifinsu, sai SAMU ya doshi gabashin duniya, yayin da shikuma HAMU ya doshi yammacin duniya.

    Bayan wani lokaci mai tsawo, sai akayi wani Sarki mai suna ZIYAZINUN shi wannan Sarki ire-iren zuriar SAMU ne, kuma ya samu tarihin adduar da Annabi Nuhu {Alaihissasatu wassalam} ya yi wa kakansu na cewa "Allah yasa a irin zuriyar sa a samu wanda zai mulki duniya, kuma a samu wanda zai yada addinin Ibrahimiyya, da yake a wannan lokaci zamanin Annabi Ibrahim ne {Alaihissasatu wassalam}. Sarki ZIYAZINUN ya lashi takobin InAllah ya yarda a kansa wannan addu'ar zata fada, saboda haka ya yi ta yake-yake a gabashin duniya kuma ya murkushe kasashe da dama da yaki, har ya fado yammacin duniya. Sai da takai hardai tsufa ya riskeshi.

    Wata rana Sarki ZIYAZINUN ya sauka a wani guri, sai yaga yanayin wannan waje yana da kyau kuma yana da dadin zama, saboda haka sai yasa aka gina masa birni aka sa masa suna HAMRA'U YAMEN. Shi wannan birni daya gina yana karkashin masarautar HABASHA ne, wanda a wannan lokaci ita wannan kasa tana karkashin wani sarki mai suna SAIFURRA'ADU su kuma ire-iren HAMU ne wato su bakake ne. Sarki SAIFURRA'ADU ya samu labari cewa ga wani farin Sarki can ya sauka a kasar sa, harya kafa birni ba tare kuma da izininsa ba. Dan haka sai ya tura 'yan leken asiri domin su gano masa irin shirin da Sarki ZIYAZINUN yazo dashi. Suka je suka sanar wa da Sarkin su cewa ai Sarki ZIYAZINUN yazo da runduna ta sadaukai masu tarin yawa, kuma suka fada masa cewa bazai iya yakarsa ba. Nan da nan Sarki SAIF yasa a ka tara masa bokayen kasar HABASHA domin su ba musulmai bane, taurari suke bauta mawa. Ya umarci bokayen nan dasu duba masa  su gani idan ya yaki wannan Sarki akwai nasara ko babu. Bokayen nan suka dukufa suka fara bincike kowanne yayi-yayi amman babu nasara, karshe dai suka sanar wada Sarki SAIF ya hakura babu nasara. Sarki ya sallamesu suka watse daga nan kuma Sarki yasa a ka kira masa wasu manyan bokayensa masu suna SAKARADISA da SAKARAJUNA da Wazirinsa mai suna Waziri BAHARU. Nan da nan wannan mutane guda uku suka zo gaban Sarki SAIFI suka zauna. Sarki ya ce "Yana so ne su bashi shawarar yadda zai bullo wa Sarki ZIYAZINUN?". Da bokayen nan suka ji wannan bukata ta Sarki sai sukace "Tauraruwa ta baka nasara, ai abinda zaka yi shine ka dauki daya daga cikin yardaddun bayin ka ka bata guba, ka ce kana so ta boyeta a jikinta yadda kowa bazai iya ganinta ba, idan ta boye sai ka turata izuwa Sarki ZIYAZINUN a matsayin kyauta ta karramawa, ita kuma ka umarceta da idan ta tashi bawa Sarki ZIYAZINUN ruwa ko abinci da ta saka masa wannan gubar daya ci ko ya sha, sai ya mutu kaga shiken ba sai mun yakesa ba. Sarki SAIF yayi murna da wannan shawara daga bakin SAKARAJUNA. Nan da nan yasa a ka kirawo wata kyakykyawar kuyanga wadda tana daya daga cikin yardaddunsa mai suna KAMRIYYA. Aka kawo guba ya bata ya ce "Ta boye inda ba wanda zai ganta koda cajeta aka yi". KAMRIYYA ta karbi gubar nan ta cusa a gashin kanta yadda inba wanda ya sani ba ba yadda za'ayi mutum ya gane. Daganan ya yi mata bayannin ce wa zaiyi kyautar ta ga Sarki ZIYAZINUN, idan ya karbeta suna tare to tasan yadda za tayi domin ta bashi wannan gubar ko dai a abinci ko kuma ruwan sha yaci ko ya sha. Ya ce “Idan ta aikata hakan zai 'yantata kuma zai bata dukiya mai tarin yawa, idan kuma ta kasa yin hakan to muddin ta dawo HABASHA to sai ya halakata”. Da KAMRIYYA taji haka sai ta ce “Zata aikata duk abinda Sarki yake so.

*Domin samun complete Book1 saika tuntubeni ta wannan number 08138873799 akan naira 200*

Post a Comment

0 Comments