https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
π»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈ
*SUHAIMA* ( *Yar* *sarki* *ce* )
π»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈ
*NA*
*Shafa'atu* *Muhammad*
( *Beauty* *beby* )
*ZAMANI* *WREITER'S* *ASSOCIATION*π€
_____________________________________
We are here to educate motivate entertain our readers
_______________________________________
I *na matukar kaunar ku a rayuwata yan KUNGIYAR ZAMANI WREITER'S ina alfahari da ku Allah ya barmu tare* π€π₯°π
*Wanna* *pg* *nakine* *ke* *kadai* *bazan tafa mantawa da hallacin da kikamun ba* *Allah ya miki jagora aduk kan lamarinki*
*my* *sweet* *sister* *BINTA* *UMAR* *ABELLE*
*Allah* *ya* *gafartawa* *mahaifamu* *Amin* *ya* *rabbi*
*BISMILLAHI* *RAHAMANI* *RAHIM*
π
Ώ *9* & *10*
....da shigarta daki Umma Ma'u ta bita a baya, Mamana maiya faru naganki cikin farin ciki haka, "Ummana bana fada miki zamuyi jarrabawa ba kuma idan mutum yaci za'a kaishi birni ba ya cigaba da karatu. Eh kwarai kin fadamin diyara, to Umma naci jarrabawar kuma makarantar gidan Sarki naci, kuma kinsan wani abu kuwa Umma, A'ah saikin fada diyata Umma ce take magana cike da mamakin yarta ta, haka aka ce a gidan Sarkin zamu zauna Umma.
A gaskiya Mamana da kamar wuya na barki kitafi karatu har na tsawan lokaci batare dana ganki ba, ce war Umma dan Allah Umma ki amince mana wlh zamufa rika zuwa hutu gida duk qarshen zango karatu.
...Tau shikena ki bari Malam yazo muji ta bakin sa duk abinda yace da shi za'ayi amfani. To SUHAIMA tace ta samu guri ta kwanta duk jikinta yayi sanyi dan tasan da kamar wuya Baban nata ya yadda tayi nesa da dasu, haka ta wuni sukuku babu walwala kamar yadda ta saba, Ummah ta duk tana lura da halin da yarta ta take ciki.
Da daddare kuwa Malam ya shigo domin yi musu sallama sabida ba'a dakin Ma'u yake ba, ajjiye musu leda yayi da Malam musa ya bashi yace ya kaiwa SUHAIMA, ya juya da zummar fita, Ma'u ta katseshi da "Malam ina son muyi magana, wata magana ce haka Ma'u da daddaren nan, zayyane masa komai tayi da SUHAIMA ta fada mata, ajiyar zuciya yayi yace da ita ta bari sai gobe zasuyi maganar(saboda kar lami ta zargesu) toh tace domin tasan abinda yake nufe sukai sallama ya tafi, duk hirar da sukeyi duk SUHAIMA tana jinsu sai tayi kamar tayi barci cikin dare SUHAIMA ta tashi tayi alwala tayi sallah kamar yadda ta saba duk wani dare sai tayi sallah, sannan tayi addu'o'i masu yawa sannan ta koma bacci.
Washe gari da safe Malam yana tashi ya wuce gurin Amininhi domin tattauna wannan maganar da SUHAIMA tazo musu da shi.
*******************************
Kai tsaye gurin sanarsa ya nufa domin yasan anan zai samaishi, da zuwansa kuwa ya iske shi yana zaune bisa kujera, gaisawa sukai sannan ya sami guri ya zauna, sannan ya fada masa abinda yazo da shi.
....To Malam Garba abinda yaka mata anan shine kabar yarinyar nan ta tafi karatun ta, wannan fa dama Allah ya baku, wata qila a dalilin haka ta samu iyayenta, sannan Abu na biyu shine yarinyar nan ilimi zataje nema ba wani abinba, sannan idan kana kokwanto akan SUHAIMA ka dai na domin Yarinya ce mai hankali da natsuwa ga kamun kai shiru Malam Garba yayi sakamakon maganganun da abokinnasa yayi masa masu gamsarwa godiya yayi masa ya koma gida domin tattaunawa da matarsa.
-------------------------------
Da shigarsa gida ya wuce dakin Ma'u ya samu wuri ya zauna, sannan ya kirata ta fito rumfa, sannu da zuwa Malam Ma'u ce ke magana sannan ta debo masa ruwa a kwanon sha. Yawwa Ma'u maganar yarinyar nan nazo da ita, naje gurin Malam musa ya bani shawara kuma haka za'a yi, to Malam meyace maka, Ma'u ce take magana dauke da mamaki a fuskar ta fada mata yayi duk abinda suka tattauna akai sannan yace da ita kinga Asma'u abinda nakeji idan auren yarinyar nan yazo meza muce. Kin san ko ni dake mun boye lami da saura mutane bazasu boyewa Wanda yazo neman auren ta ba.
Sannan kinsan yarinyar nan bata San ba mune muka haife taba. Kawai abinyi mubarta ta tafi karatun ko Allah yasa ta samu iyayen ta a can, idan kuma ba'a yi daceba sai ta dawo garemu muciga ba da riqeta har Allah ya bayyana iyayenta. hakane Malam duk abinda ka fada gaskiya ne, sau daya banasan SUHAIMA tayi nesa dani, wlh inaji ta kamar jinin jikina Ma'u ce take magana tana sharar qwalla, nasan da haka Asma'u wlh nima banso haka ba, amma ya zamuyi dole mubarta ta tafi.
*(Allah sarki duniya baka sanin ka shaku da mutum sai yayi nesa da kai)*
Yawwa wai ina ta tafine, Malam ne yake magana domin kawar da zancen da sukeyi akan SUHAIMA , ai Malam tana makaranta yanzu ma zaka ganta ta dawo.
Bata rufe baki ba sai suka jiyo sallamarta, gaishe su tayi sannan ta dubi Ummar ta tace lafiya naga idonki sunyi ja, A'ah babu komai Maman kaina ne yakemin ciwo, Allah sarki Umma ta sannu kinji amma kinsha magani koh, ehh Umma tace sannan ta tambayi diyar tata yaushe zasu tafi birni karatun.
La'a Umma ai sati mai zuwa ne zamu tafi, toh shikenan yarinta maganar da mukeyi kenan da babanki dan har ya barki ki tafi, wani runguma tayiwa Ummar ta ta, don murna sannan ta jiyo gurin Baban nata tana tayi masa godiya tareda addu'o'i sannan ta shige uwar daki tana murna.
____________________
Malam da Ma'u kuwa sai mamakin murnar ta sukeyi gaskiya SUHAIMA tana son karatu kowannen su magana yake a cikin zuciyar sa.
*******************
Tun daga wannan rana Umma da Malam suke shirye2n tafiyar diyar tasu, kuma a yaune zasu tafi tare da qawayen ta.
Tun da garin Allah ya waye SUHAIMA take ai kin kuka.
*Adadin Comments dinku Adadin typ ehh*
Vote and share
Comments
*Mmn beby ce* π₯°
0 Comments