(Hausa Novel) Matar Mijina By Kamala Minna Page 1,2,3,4&5

[1/9, 3:27 PM] Denny Minna ZWA: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION*.

Kamala Minna
Kamalminna217@gmail.com

MATAR MIJINA


01.


A hankali take takawa kan kafafuwanta, da wani irin yanayi mai tattare da natsuwa, zuciyarta take ji tana mikata wani mataki mai tsayi, wanda yake kara buɗe mata zuciya da ruhi zuwa  bangare, mai dauke da damuwa.

Kara danke file din dake hannunta tayi, idanuwanta na lumshewa a hankali, har ta karasa sakkowa daga benen da take jin sa kamar tana saman gajimare ne.

"Nusee!!".

Ta ji kunnuwanta sun ansa, sautin muryar da taji an yi amfani da ita wajan furta sunan nata wanda mutum daya ne a filin duniyar nan yake kiranta da wannan sunan.

Numfashi taja mai tafe da kwalla, kafun ta tsaya cak! da tafiyar da take yi, tana dago dara-daran idanuwanta da suka kaɗa kadan, ta sauke su a saitin da taji sautin ya taso.

Jingine yake jikin motarsa kirar Benz mai launin ja, sai faman daukar idanu take yi. jikinsa sanye da kananun kaya da sukayi matukar ansar tsarin
halittarsa, na ɗa namiji. kau da kai tayi.

Bata so ya fahimci halin da take ciki, ba ta so ya gane a wani mataki take na damuwa, a daidai wannan lokacin murmushi take so ko ya ya ne, ya wanzu a fuskarta. so take yi tayi abin da zai wanzar da fararan

hakoranta waje ya gani. Bata so yaji wani iri a ransa, tafi kaunar ta ajje wannan damuwar a zuciyarta ita kadai, ta magance ta ba tare da Yah Jaamal ya sani ba...

"Nusee!!".

Ya sake fadi da wata irin murya, mai sauti da mamakin yanayin da ya ganta a ciki. takunsa take ji yana kusanto ta, takun da take jin sa har cikin zuciyarta yana haifar mata da wani irin yanayi, tsayawa tayi cak! tana kokawa da numfashinta da take jin sa yana sama da kasa, kamar zai fice daga gangar jikinta. kamshin turaransa Dark wood take ji yana dukan kofofin hancinta, yana kara narkar mata da duk wata gaɓa na jikinta.

Numfashinsa take jin yana ajjewa a hankali, da yanayin da ba zata iya cewa gashi ba. runtse idanu tana buɗe su lokaci guda, kafun ta dago idanuwanta, bayan tayi kokawa da zuciyarta ta wanzar da wani wahalallan murmushi gami da bayyanar da ratsantsiyar wushiryarta, dake tsakanin fararan hakoranta masu k'yalli da ban sha'awa.

"Uhmmm...!!".

Tayi hakan cikin wani irin sauti, kafun ta daga dan yatsarta guda ta saka cikin baki tana cizawa, so take yi ta sauke damuwarta akan sa, so take yi duk wani gazawa da rashin dauriya da zuciyarta take kokarin kawo mata ya tsaya a dan yatsar Hannunta, ciza shi take yi sosai. sosai take jin zafi amma hakan sai yafi mata dadi akan ta bayyana da damuwarta ga Yah Jaamal.

"Yaushi ka dawo?".

Ta furta tana kara matse damuwarta, a wani sashi na zuciyarta. wanda tayi kokarin kwatoshi ta dasa masa jarumtar dole.

Bai ansa ba, illa idanunsa da yake watsawa akanta. Sosai take jin kallon da yake mata yana taba mata zuciya, sosai take jin yana haifar mata da wata irin kasala, dake kokarin karyata mata duk wata jarumta da tayi kokarin dasawa kanta.

gefe guda ta mai da kanta tana kallon tsarin filawowin dake shirye reras cikin filin Company din. zuciyarta na kara matsewa da abin da ya faru da ita, a daidai wannan lokacin zuciyarta take ji tana wani ɗaci-ɗaci har saman laɓɓanta.

"Nusee me ke damun ki haka?".

Ya fadi yana harɗe murɗaɗɗun hannayansa saman fanfaɗar kirjinsa, mai cike da zati da tsarin halittar cikakken ɗa namiji.

Ba ta ansa shi ba. illa kara danke file din da tayi, kafun ta dago idanuwanta wanda suka kara tona asirin halin da take ciki, laɓɓanta ta shiga motsawa magana take son furtawa ko da kalma daya ne, amma yanayin da zuciyarta ke bugawa duk ta karya mata jarumtarta.

Bin laɓɓan nata yake da kallo, wanda suka wadatu sosai da taushi, ga pink din jan baki da ta zizara ya kara ƙawata laɓɓan nata sosai.

"Yi magana mana Nusee".

Ya fadi yana kara kusanto ta, hannunta ya kamo wanda ta damke jakarta dake rataye a kafaɗarta gam! Ya hada dana shi yana murzawa, hakan ya sanyata runtse idanu kafin da sauri ta kwace hannun nata, tana matsawa baya kadan zuciyarta na furta.

'Astagfirullah wa'atubu ilai'.

"Yaaa Jaamal...".

Da sauri ya sanya ɗan yatsarsa saman laɓɓansa masu duhu kadan yana furta.

"Shiiit".

Murmushi ne kadan ya wanzu, a fuskarta don ta san abin da yake nufi, don haka ta dago idanuwanta ta sauke a saitinsa, tana yatsine fuska kamar karamar yarinya mai shirin ballewa da rigima.

"Uhm...Uhmm fa Yaa Jaamal Is Not Good To Us".

Yatsine fuska yayi. kafun ya daga kafadunsa alamun ko a jikinsa, sannan yayi mata nuni da motarsa.

A hankali ta shiga takawa tana dosar motar tashi, a hankali take jin yarda idanuwansa ke kanta suna kara narkar mata da gajiyayyen jikinta, bata son irin kallon da yake yi mata, bata so sam! Sosai yake haifar mata da wani irin yanayi a jikinta, ta san TUHUMA ce yake yi mata, da wannan kallon ta sani kuma in har bata yi wasa ba to tabbas komai zai yi faru ita, shi ya san salon da yake hukuntata dashi, in har yana son sanin abin da ta boye a bayan zuciyarta.

"Gaba zaki shiga mana".

Ya fadi a saitin kunnanta na dama, sam! bata san ya iso daf! da ita ba, sautin muryarsa ce kawai ta tabbatar mata da hakan, zuciyarta ta doka kadan da sauri ta saki handle din kofar, baya tayi niyyar shiga, ta shiga ja da baya kamar mai tsoron sake taba motar, matsawa yayi sosai ta wuce ta zagaya ta dayan hannun da yake motar matukinta a dama yake.

Binta yake da kallo yana karantar yanayin ta, sosai ya gane akwai abinda ke ɗawainiya da ita a cikin zuciyarta, amma take boye masa. sai da ya shigarta sa'annan shima ya buɗe bangarensa ya shiga ya zauna, gami da dafe sitiyarin yana danke shi cikin hannayensa, kafun ya ja numfashi yana sauke idanuwansa a saitin ta. Kanta a kasa tana faman wasa da jakarta gami da File din da har lokacin bata sake shi daga rikon da tayi masa ba.

"Ba su dauke ki bane hala?".

Ya fadi yana kara kureta da idanuwansa, bai so tayi masa karya duk da ya san ba halinta bane, amma a yanzu a daidai wannan lokacin yana hango abubuwa biyu da suka wanzu a idanuwanta, gaskiya da akasin hakan kuma yana hango akasin yarda yake kokarin danne gaskiyar ta ta.

"Yaah Jaamal mana!".

Ta fadi da alamun riga a muryarta, bata so ta fadi masa abinda ke damunta, sannan bata so tayi masa karya, wacce ta tabbata in tayi sai ya gano, domin ta gano hakan a yanayin kallon da yake yi mata, wanda take jinsa yana kaiwa har zuciyarta...

"Rigima..Rigimarki ce bana so Nusee kiyi magana kawai ban son rigimar nan taki".

Ya fadi yana kara buɗe idanuwansa akanta, turo baki tayi gaba tana mai cewa.

"Ni fa ba komai...".

"Ban yarda ba!".

Ya tare ta da sauti da muryarsa, mai nuna da gaske yake.

Gabadaya cikin motar ya dau shiru, na batun da suke yi sautin waƙar Because Of You ce kawai take tashi can kasa-kasa.

Nusaiba sai satar Kallon Jaamal take yi take gefen idanu, tana jin yarda zuciyar ke shiga wani irin yanayi musamman in ta kalli yanayin fuskarsa, laɓɓanta ta motsa tana faman hade hannayenta waje daya ta shiga mutsu-mutsu kamar wata maras gaskiya.

"Ki zauna dakyau mana!".

Ya fadi da sauti hankalinsa na saitin tukin da yake yi, runtse idanu tayi kafun ta saita kanta cikin kankanin lokaci. bata son abin da zai bata ran Jaamal sam! Bata so a ce daidai da sakan daya ransa ya bace a dalilinta.

hakan daukar shi take yi a matsayin butulci mafi girma a filin duniyar nan.

"Kayi Hakuri".

Ta fadi da rawar murya, kamar mai son fashewa da kuka. bai kalle taba illa numfashi da ya ja ya fesar ya daki sitiyarin kadan, a daidai wannan lokacin suka iso Estate din dake Unguwar Bosso Lowcost.

A hankali ya rage gudun motar har suka isa saitin gidan na su. Horn yayi ajere da sauri mai gadin ya zo ya buɗe musu, bayan ya leko ta karamar kafar kofar ya ga su waye.

Bayan sun shiga gidan Jaamal yayi parking, ba tare da ya sake duban Nusaiba ba, wacce sai faman mutsu-mutsu take yi.

"Fitar min daga cikin mota".

Ya fadi ba tare da ya kalle ta ba, ya sauke kujerar motar zuwa baya ya kwanta idanuwansa a rufe.

Dubansa tayi da idanuwanta da suka fara zubda hawaye, ta shiga motsa laɓɓanta kafin lokaci guda sautin kukan nata ya fara fitowa kadan-kadan, buɗe idanuwansa yayi akanta kafun ya kau da kai.

"Ba kiji abin da nace dake bane, ki ka tsaya zaki cika min kunne da kuka, shin me ma akayi miki?".

Ya fadi da nuna fushi a muryarsa sosai. girgiza kai ta shiga yi kafun lokaci guda ta ja numfashi.

"Yah Jaamal kayi hakuri, ba zan sake ba don Allah!".

Ta karashe muryarta da zuciyarta na kara karyewa da wani irin yanayi.

"Nusaiba mana I say get out!".

Ya fadi da wata irin murya, wacce ta ansa sauti a cikin motar baki daya.

ita kanta Nusaiba firgita tayi sosai, idanuwanta a runtse tana jin yarda zuciyarta ke matsewa da fushin da take ganin Jaamal nayi akan ta, ba zata iya jurewa ba, ba zata iya ganin Jaamal na fushi da ita ba, ko da na sakan daya bane. zuciyarta zafi take yi, zuciyarta kunewa take yi, ji take yi kamar an watsa mata acid a cikinta.

"Na tuba Yah Jaamal. zan fadi maka komai don Allah karka yi fushi dani...".

"Oh God! nace ki fice mani a mota ko!".

Bata san lokacin da hannunta ya kai saitin murfin motar ba ta bude, kawai ganinta tayi saman kafafuwanta da suke ta faman kaɗawa kamar za su watsar da ita kasa.

Durkusawa tayi tana tattare file din hannunta da suka watse, dago kai tayi tana duban Jaamal. da ya runtse idanu zuciyarsa yake ji tana harbawa sosai, wani irin yanayi yake ji na rashin jindadi, bai san mai yasa ya yiwa Nusaiba magana da murya mai sauti har haka ba, abin da bai taba yi mata ba tsayin shekaru masu dama, amma yau rana daya yayi mata magana har ta firgita tayi kuka.

"Yaa zuljalalu wal'ikram!".

Abin ya ya shiga furtawa kenan cikin zuciyarsa, har zuwa lokacin idanuwansa a rufe suke, amma zuciyarsa tana hango masa yanayin da Nusaiba take ciki, a daidai wannan lokacin. yana jin zuciyarsa na ansa takun sautin takalmar dake kafafuwanta, sake tanke idanuwansa yayi yana jin yarda zuciyarsa ke kara mikashi wani mataki, tana yanke masa hukunci akan abin da ya yiwa Nusaiba.

A hankali ya shiga jan numfashi kafun ya dago kansa, yana saitawa inda zai hangota. tafiya take yi kamar mai tausayin kasa taku daya biyu in tayi sai ta tsaya ta juyo ta dubi motar tashi, yanayin da ya hango fuskarta a ciki ya kara sanya gabansa bugawa, da sauri ya mike ya zare key ya dauki wayarsa ya fice daga cikin motar ya rufe.

Harɗe hannayensa yayi a kirjinsa, yana saita idanuwansa a saitin kofar falon da Nusaiba ta karasa shigewa. numfashi ya ja kafun a hankali shima ya shiga taku da wani irin sanyi da zuciyarsa ta haifarwa gangar jikinsa.

Da sallama ta shiga cikin falon, Mami ce zaune gabanta files ne duk tayi ɗai-ɗai dasu. sallamar da taji ne ya sanyata dago fuskar mai dauke da medical glass. ta sauke ganinta ga Nusaiba da tayi tsaye bakin kofa, kamar wacce aka dasa. sosai take dubanta bakinta na ansa sallamar kafun ta kau da kanta, tana maidawa kan aikin da take yi. zuciyarta na tsanar wannan halin na Nusaiba, bata san ya zata yi da ita ba, yarinya gabadaya ba a gane mata, kamar wacce aka halicci rayuwarta daban da sauran mutane.

"In ba za ki shigo ba, ki fice mani daga falo".

Mami ta fadi kanta a kasa,a daidai lokacin Jaamal ya sako kai maganganun Mami suka sauka a saitin kunnuwansa, runtse idanu yayi kafun ya yi koƙarin yin sallama. Mami dago kai tayi ta dube shi da wani irin kallo na tuhuma.

"Sai da ka je kenan ko?".

Hade hannayensa yayi waje daya, alamun neman afuwa. kafun ya dubi Nusaiba da tayi tsaye kamar wacce aka dasa, sai faman ajiyar zuciya take yi har zuwa lokacin idanuwanta da kwalla.

"wuce muje".

Jaamal ya fadi can kasar makoshi, ita kanta da take kusa dashi ba ta ji shi da kyau ba.

A hankali ta shiga taka kafafuwanta kan lallausar kilishin dake malale tsakar falon ji take yi kamar zata zube a kasa, kafafuwan nata take jin suna lauyewa zuciyarta ce take kawo mata jarumta tana taimakawa gangar jikinta, a haka har ta kusanto kusa da Mami, dago kai tayi ta dube ta.

"Ba dai kin ce kunne k'ashi gareki ba, ga fili ga mai doki ai, ki shirya yin sukuwa da turjiya".

"Mami mana!".

Jaamal ya fadi da sautin rarrashi a muryarsa, dubansa tayi kafun ta dauke kai, tana cigaba da abin da take yi.

Nusaiba dake kokarin zarcewa zuwa dakinta, da sauri Jaamal ya kira ta cak! ta tsaya da tafiyar da take yi, bata so haka ba, ta so ta isa dakinta ko za ta samu saukin zuciyarta. hawaye ne a fuskarta bata so Jaamal ya gan su bata so sam! sam!.

"Dawo ki zauna nan mana".

Ya fadi da muryar mai dauke da rarrashi ya san halin ƙanwar tashi, abu kadan ne ke rikita mata zuciya, abu kadan ne zai hana ta sukuni, ya lura kuma akwai jikakkiya tsakaninsu da Mami ya san dole ta kasance cikin yanayi na damuwa, sosai da sosai.

abin da shi kuma ya tsana kenan a filin duniyar nan, damuwar Nusaiba baya so sam! sam!.

"Ban san abin dake damun Nusaiba ba, ban san mai yasa take kokarin takura kanta ba, gani take yi kamar bana so taje Bukar Kutigi Company aikin ne, gani take yi kamar bakin cikin aikin nake yi mata acan".

Mami ta fadi lokacin da ta shiga tattara files din, ta mai da gefe guda tana duban Jaamal da ya zauna kusa da ita, a daidai lokacin Nusaiba ta juyo zuciyarta na karyewa, dauke kwallar idanunta tayi ta, dubi Jaamal sannan ta dubi Mami da fuskarta take hade alamun ranta a bace yake.

Tayi da nasanin daukar kafafuwanta taje BKC don yin aiki. tayi kaico in da ta bi maganar Mami da bata fuskarci matsalar da take ciki a yanzun ba, in da ta dauki maganar Mami da zuciyarta bata dauko mata ciwon da zai jima yana damunta ba, tayi da na sani...Dana sani mai girman gaske a filin duniyarta...

"Ba cewa nayi ki tsaya a tsaye ba zama zaki yi".

Muryar Jaamal ta katse mata bak'in tunanin dake haifar mata da ciwo mai girma, numfashi ta ja kafun ta sauke idanuwanta zuwa kasa tana takawa a hankali har ta isa kusa da kujerar da Jaamal yake zaune, ta dora kugunta kadan kamar wacce take kan ƙaya haka ta shiga yatsine fuska zuciyarta na matsewa da wani tsananin haushi da takaicin kanta, domin bata ga laifin kowa ba sai nata, in da bata je ba duk haka ba zata faru da ita ba.

"Me yasa haka Nusaiba, mai yasa kika ƙi jin maganar Mami haka, ban san ki da taurin kai ba, ban san ki da kalar wannan halin ba, me yasa kika canza Nusaiba?".

Jaamal ya fadi cikin wata irin murya mai taushi, da kuma alamun damuwa a cikinta.

Zuciyarta taji ta sake harbawa, ji take yi kamar ta daura hannu aka ta kurma ihu, don wani irin tukuki take jin zuciyarta da ruhinta nayi, ji take yi ta tsani kanta sosai da sosai yau rana daya taji takaicin kanta, yau rana daya taji bata kyautawa kanta ba da Maminta, har da Yah Jaamal don ta tabbata shima dole yaji damuwa a zuciyarsa, musamman kan batun da Mami tayi akanta na kin yi mata biyayya da bin ra'ayinta.

Runtse idanu tayi gami da bude sua lokaci guda, ta shiga motsa laɓɓanta a hankali.

"Yah Jaamal...Uhhmm can nake so fa dama".

"Saboda can kike so hakan ya baki damar ƙin yiwa Mami biyayya ko!".

Ya fadi da sauti a muryarsa mai nuna alamun ransa ya sosu.

"Uhm..Uhmm fa Yah Jaamal".

"Ya isa haka!".

Mami ta tare su tana mikewa kan kafafuwanta.

"Amma Mami...".

"komai ya wuce Jaamal a bar maganar".

Ta sake tare shi tana wuce wa zuwa sashin dakin ta.

Shiru ne ya gilma tsakanin su na dan wasu lokuta, zuciyoyinsu gabadaya sun mika su wani sashi na daban, Musamman Nusaiba da zuciyarta ke ta faman tariyo mata abin da ya faru da ita a Company din da haduwarta da FAROUK MA'AROUF KUTIGI...

*Assalamu alaykum*

*My Beautifull People*

*I'm back with another Saga...*

*lot of Love*🥰🥰
Kamala Minna
[1/9, 3:27 PM] Denny Minna ZWA: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION*

Kamala Minna.
Kamalminna217@gmail.com


*MATAR MIJINA*


02.

Mikewa tayi a hankali kan kafafuwanta, da take jin su kamar zasu watsar da ita kan lallausar cafet din,  malale a tsakiyar falon.

A hankali take jan numfashi, zuciyarta na kara matsewa waje guda.

Laɓɓanta take tura cikin bakinta tana cizawa, bata so ta ce komai, bata bukatar ta bar harshenta ya daga har ya furta wata kalma guda a yanzu.

Ta tabbata in tayi gangancin yin hakan, sosai abin dake damunta a gurbin zuciyarta zai fallasu, alkawari tayi wa kanta alkawarin da bata so ya karye, a kasar zuciyarta zata binne komai bazata fallasa ba.

"Kina takura kan ki da yawa Nusaiba, ban san mai yasa ba? rayuwarki nake kallo a daban a filin duniyar nan, ban san mai yasa haka ba? Kin zabi rayuwa a hagu wacce bana tsammani zata kai ki inda kike muradi".

Muryar Jaamal ta tsinkayo a saitin kunnanta na dama, da sauri ta runtse idanu, kafun ta daga kafafuwanta tana cigaba da taka su a yarda suke.

Dakinta ta nufa zuciyarta da wani irin yanayi, tura kofar tayi ta shiga, kafun ta tsaya cak!. Daga bakin kofar tana bin cikin dakin da kallo kamar wacce ta ga sabon abu.

Tsarerren daki ne mai cike da kayan more rayuwa komai na cikinsa dangin su Furnitures duk Pink-Colour ne masu k'yan tsari da burgewa.

A hankali ta shiga taka lallausar Cafet din, dake malale tsakar dakin mai tsananin laushi da burgewa.

Karasawa tayi ta zauna bakin gadon tana rufe idanu, gami da tallabe haɓarta da dukkan hannayenta.

Sosai take jin zuciyarta na buɗewa tana kara wassafo mata Farouk Ma'arouf Kutigi mutumin da take jin sunansa, ya karade waje da yawa tun da take bata taba ganinsa a zahiri ba, bata taba kawo wa kanta zata ganshi ba, amma yau rana daya ƙaddara ta zano mata shi cikin filin duniyar rayuwarta, wanda bata san ya zata fuskanci al'amarin ba, sosai zuciyarta ke taɓuwa a yarda ya dube ta bayan ta isa gareshi, bata taba kawowa kanta shi zata tarar ba...

*******

"Yes Come in".

Abin da taji an fadi kenan da wata irin murya mai dauke da izza, numfashi ta ja ƙafun ta rike handle din kofar tana saita numfashinta gami da natsuwarta, da take jin tana kokarin yi mata karanci.

Runtse idanu tayi sannan ta tura kofar a hankali, tana mai sanya kafafuwanta cikin Office din da take jin wani kamshi na dukan hancinta, yana mikawa can cikin kwanyarta. Zuciyarta taji ta buga da wani irin yanayi, hakan ya sanyata buɗe idanuwanta sosai da sosai tana saukewa a saitin cikin office din.

Zaune ta hangoshi saman Table din dake dauke da kayan files-files da sauran karikitai.

Mamaki ne ya dan taba mata zuciya, ganin yarda yayi zaman bayan ga kujera ta asali da ake zama akanta, amma duk ya ture ya haye inda aka tanada don ajje duk wasu kayan da zai duba dangin su Files.

Kau da kai tayi, tana gargadin zuciyarta na shiga hurumin da ba nata ba.

"Nusaiba Bukar Kutigi".

Taji sautin muryarsa ta ambaci sunanta, Haka kawai taji gabanta ya buga da sauri ta dago kai ta dube shi, shima jajayen idanuwansa suna saitin ta sai dubanta yake yi kamar wanda ya ga wata halitta ta daban a filin duniya.

"Uhmm...".

Tayin kokarin jan numfashi, tana mai kara danke file din dake hannunta.

"Zan iya zama please".

Ta fadi kanta na duban inda kujeru biyu ke girke, domin sosai take jin kamar zata fadi.

"Why not zaki iya zama".

Ya fadi yana mai dire kafafuwansa a kasa, yana mikewa sosai dogo ne fari mai cikar saje a fuskarsa, laɓɓansa masu duhu idanuwansa ba manya bane sosai sun kaɗa sunyi ja kadan.

"An sanar dani za ki zo, but a yanayin da nayi zaton ganinki sai ba haka ba".

Ya fadi da wani murmushi a fuskarsa, hannunsa guda saman sajensa yana faman shafawa a hankali idanuwansa yake juyawa akan Nusaiba, da take jin ta wani iri.

Zuciyarta take ji tana harbawa, sosai take jin dama bata zo ba, bata san mai yasa lokaci guda zuciyarta taji rashin amincewa da wannan mutumin ba, mutumin da ake ce shi zata je wajansa shine Manager Director na BKC.

Shine zai anshe ta shine zai bata gurbin da take bukata, ba tare da an karanta mata akwai wata matsala ba.

Ita ma bata taba kawo haka a ranta ba, fatanta burinta shine ta samun abin da take so...

"Ba ki ce komai ba".

Ta sake jin amon muryarsa a saitinta, sosai take jin bugun numfashinsa a kusa da ita. kanta dake kasa ta dago, tsaye ta ganshi a saitinta taku daya ne zai iso gareta.

Bugun zuciyarta taji ya sauya cikin sakanni, kanta take ji yana juyawa da kamshin da take ji yana tasowa daga gareshi, a duk lokacin da ya saki numfashinsa zuwa waje.

"Ehm...".

Harshenta taji ya sarke da wani irin yanayi, a daidai lokacin da ta dago kanta tana kokarin sanar dashi komai da yake tafe da ita, duk da ya fadi mata an sanar dashi zuwanta. Amma ai zai so karin bayani daga gareta.

"Ya dai ko wani abu na damunki ne? ki bude baki kiyi magana mana, karki damu fa ba abin da zai faru".

Ya fadi yana mai daga kafadunsa alamun son ta gasgata shi, fuskarsa da wani guntun murmushi.

Yaƙen dole ta kalato ta sauke a fuskarta, kafun ta gyara zamanta, ta shiga yi masa bayanin abin dake tafe da ita, cikin sanyin murya wacce in ba kana da karfin ji ba sosai ba zaka ji mai take fadi ba.

Yawatawa kawai yake yi da idanuwansa akan ta, yana jin yarda sautin muryarta take kaiwa ga zuciyarsa tana ba shi wani sauti mai dadi sosai gami da dandano da yake jin sa har saman harshensa, sosai yake ji tana burgeshi, sosai yake jin zuciyarsa na budewa da wani irin yanayi ansar kalaman yake yi yana mikawa zuciyarsa, tana kara wassafa masa wani al'amari.

"Cigaba mana".

Ya fadi a sa'ilin da yaji ta tsagaita tana mai da numfashi, ita kadai ta san abin da take ji, ita kadai ta san yanayin da zuciyarta ke ciki, gabadaya taki yarda dashi sosai zuciyarta take matsewa da wani irin yanayi game dashi, lokaci guda take jin, rashin son aiki tare da BKC burinta fatanta duk ta ji sun sauya a lokaci guda.

"Are you Done?".

Ya fadi yana mika hannayensa yana ansar file din da take kokarin mika masa amma ta kasa, ansa yayi a saitin dan yatsanta kuda daya ya daura nashi hakan ya sanya Nusaiba runtse idanu gami da saurin sakin file din da bai gama ansa ba, watsewa sukayi gabadaya a kasa dubansa tayi cikin idanunsa wanda shima ita yake kallo wani murmushi ya sakar mata, kafun ya rankwafa da sauri yana kokarin tattare file din, ita ma a daidai lokacin cikin sanyin jiki tayi kokarin yin haka, bisa akasi suka sake gwara kai wanda har sai da Nusaiba ta saki yar kara kadan.

"Ouchh!!!".

Abin da ya fadi kenan, yana daura hannunsa daya kan goshinsa.
Sosai jikin Nusaiba ya shiga rawa, gabadaya taji ta firgice sosai zuciyarta take bugawa.

"Am so sorry".

Ta fadi can kasan makoshinta laɓɓanta na faman rawa.

"Sorry For what?. Kina kokarin fasa min kai kike bani hakuri".

Ya fadi da Confidence a muryarsa, hakan ya kara tsinkar mata da gaba sosai, musamman yarda ya kara fiddo da idanuwansa waje.

Tattare Files din yayi kafun ya mike kan kafafuwansa, yana duban su daya bayan daya fuskarsa na murmushi wanda ya zame masa kamar al'ada.

"Me yasa kika zabi aiki tare da BCK bayan kuma akwai inda ya kamata ace kin je in da yafi nan komai game da abinda kika karanta?".

Maganar ta zo mata a bazata sosai, da sauri ta shiga sarke hannayenta waje daya tana kara yin kasa da kanta, don har yanzu zuciyarta da jikinta ba su dai ansa bakon lamarin da ta samu tare da wannan mutumin ba, sosai take jin wani iri, sosai take jin komai ya sauya mata a yan dakiku.

"Say something mana, ban son mutum mai shariya sosai nake jin rashin jin dadi a zuciyata, musamman ke da ban yi zaton haka daga gare ki ba, ina son mutum mai magana ba mai ƙin ta ba".

Suna da bambaci a tsakaninsu, ba za su zauna inuwa daya dashi ba, ita kam magana ce bata so a rayuwarta wuya take yi mata sosai, ji take yi kamar wani sashi na jikinta ake cirewa a duk lokacin da tayi magana mai tsayi, anya kuwa aikinta zai yuwu tare da BKC? bata tunanin haka, tun yanzu an fara samun bamabanci ra'ayi ina ga kuma taji dokokin su kila sai ta tsani aiki da Company din gabadaya...

Maganar sa ce ta katse mata zancen zucin da take.

"Komai yayi Normally..Sai dai abu guda...".

Da sauri ta dago kai tana kallon sa, har zuwa lokacin idanuwansa na kanta. Kau da kai tayi jin yarda gabanta yake kara tsanarta bugu, duk da tana ji a zuciyarta ra'ayinta ya sauya game da kin aiki da BKC.

Amma a yanzu da taji maganarsa sosai gabanta ya fadi, don ta tabbata akwai abin da yake kokarin yi mata shamaki game da zamanta tare da inda take zaune a yanzu.

Bin ta yake yi da kallo yana so ya ga yanayin Tention din da take ciki, ya sani abin da ya fadi a yanzu dole zai canza mata yanayi, amma bisa mamaki yarda take a da yanzu ma hakan ne, buɗe idanuwansa yayi sosai cike da mamakin rashin tsoro ko wani firgici a tattare da ita, shi akaran kansa ya sani duk wani mai neman abu, yaji ance ya samu yaji an ambaci kalmar 'But' (amma) dole ya ji faduwar gaba don ya san akwai rashin tabbas a ciki.

Ji yayi zuciyarsa ta mikashi wani bangare na tunani akan yarda ya ga Nusaiba a ciki, anya kuwa ra'ayinta ne ya kawota ba tilasta ta akayi ba, anya kuwa a son ranta ne ta tako BKC?.

Girgiza kai ya shiga yi alamun bai yarda ba, ba a karan kanta ne take son aiki tare da su ba, in kuwa hakanne da matsala don har kasar zuciyarsa yake jin ya samu abokiyar aiki, sosai yake hango kwarewa da iya jajircewa a cikin idanuwan Nusaiba, yanayin natsuwarta ya san sosai zai sabu abun da yake bukata daga gareta.

Zuciyarsa yake ji tana kwadaita masa ita, so yake yi komai ace ya tabbata, so yake yi ace ra'ayinta ne ya kawo ta ba tirsasata akayi ba...ko da yake wannan ba damuwarsa bane, burinsa yake so da fatansa akan ta. Ya sani zai samu ko ta halin k'ak'a ne dole wannan matashiyar gogaggiya a fannin na'ura mai kwakwalwa ta kasance tare dashi, domin yaji a zuciyarsa ta samu gurbi, gurbi na sosai da sosai.

"Congratulation Ms.Nusaiba Bukar Kutigi and Wellcome to BKC".

Zuciyarta take ji tana kara matsewa da wani irin yanayi, haka kawai taji a ranta bata aminta da wannan ansar da yayi mata ba, duk da a ranta wani sashi a zuciyarta ta ji dadi amma hakan ba wai yana nufin zata zauna bane, a matsayin da yake kokarin daura ta a kai.

Dago kanta tayi ta dube shi a daidai lokacin da ya tura laɓɓansa cikin bakinsa, yana cizawa da wani irin yanayi murmushi ne a fuskar tashi, a hankali ya rufe file din yana mai lumshe idanuwansa, kafun ya bude su harɗe hannayensa yayi a kirjinsa a hankali.

"Nusaiba!".

Bata ji dadin kiran ba duk da yayi amfani da murya mai taushi, amma hakan ko kadan bai burgeta ba, sai ma wani dandanon ɗaci da taji sautin ya bata a zuciya har kan harshenta.
Zuciyarta taki ansar lamarin sosai take jin ba zata iya ba, sam-sam gangar jikinta taki ansa haka kawai take jin bata ra'ayin zama tare dashi in da ta san haka HADUWARSU zata kasance da bata zo ba kawai damuwa ce ta tarar...

Numfashin da taji ya sauka a saitin tane ba tare da ta sani ba, hakan ya sanyata saurin tsaida tunanin sa da take yi, a hankali ta shiga kokarin mikewa kan kafafuwanta da take jin su wani iri.

"Ina zaki je kuma?".

Ya fadi yana mai kusanto ta sosai, numfashinta da nashi har suna bugun juna.

"Ina bukatar lokaci Please I need more time to think about...".

Da sauri ya katse ta gami da kara kusanto ta, kamar zai hada jikinsa da nata. Runtse idanu tayi bugun zuciyarta na daduwa, sosai kanta take ji ya fara juya mata.

"Nooo! Please mana Nusaiba ba komai fa na gaya miki, kin zama ma'aikaciya a BKC bai kamata ace kuma kina kokarin ruguza komai ba".

Dago idanuwanta tayi ta sauke su a saitin sa, kafun ta dubi file dinta dake hannunsa, ta mika hannu tana kokarin ansa da sauri ya danke su, hakan ya bata damar danne zuciyarta dake kokarin bankaɗe halin da take ciki.

"Please mana!".

Ta fadi da sauti mai kara kadan a muryarta, baki ya saki yana mai lankwashe hannayensa gami da sakin murmushi.

"Karki damu fa. Karki yi zaton wani abu daban akai na, haka nake in muka kasance da juna zaki fahimce ni".

'NEVER'.

Ta fadi can kasar zuciyarta data ke jinta kamar zata kama da wuta, sosai ranta ya sosu sosai take jin kiyayyarsa na dalsuwa a ranta, amma ba za ta nuna masa hakan ba dole ta koyi zama dashi, dole kuma ta nuna masa ita wacece ba zata dauki wannan rainin wayon ba, a filin duniyarta sam-sam abin ba tsari ansar file din tayi, a karo na biyu bai hanata ba, don haka a hankali ta shiga daga kafafuwanta tana tunkarar kofar fita daga office din...

******

"Nusaiba!".

Sautin muryar Mami ne ta katse mata dogon tunanin da take yi, da sauri ta zame hannunta daga tagumin da ta zabga tana mai saita ganinta zuwa inda take jiyo muryar Mami bakin kofa, kallonta tayi kafun tayi kasa da kai gabanta ta ji yana bugawa kadan-kadan ganin kallon tuhuma da Mami ke yi mata.

Mami dake tsaye hannayenta harɗe a kirjinta, ta fesar da huci mai zafi kafun ta buɗe idanuwanta sosai.

"Wannan damuwar da kike saka kan ki a ciki Nusaiba abin dacewa bane gareki, da rayuwarki gabadaya. Akwai abin dake damun ki yau sosai na lura da hakan...".

"Bakomai fa Mami".

Tayi saurin fadin haka don ta san halin Mami tsaf! zata turketa da magana, har sai ta gaji don kanta ta sanar da ita abin dake damunta, ita kuma abin da bata so kenan a tambayeta.

"Abbanki na falo na jiranki tun dazu ya dawo yana cigiyarki, amma ke kina nan shanye da baki kina sanya kan ki ciki damuwa As your Age bai kamata ba Nusaiba, yarinya ce ke bai kamata ace tun yanzu kin fara saka kanki a irin wannan halin ba".

Rau-rau tayi da idanu kamar wacce zata yi kuka, mikewa kan kafafuwanta tayi gami da gyara mayafin da ta lullube kanta dashi, sannan ta fara takawa a hankali tana tunkarar inda Mami ke tsaye.

Ganin ta taho ya sanya Mami juyawa ta fice daga cikin dakin. Nusaiba ta mara mata baya cike da wani irin yanayi a zuciyarta.

"
Kewo no Nusaiba nnaawe gan wo zhin daga BKC amma wa ganyu endwaa?.
(Ya akayi ne Nusaiba Maminki tace kin dawo daga BKC amma baki ce da ita komai ba?)".

Abin da Dr.Kutigi ya tari Nusaiba dashi kenan, cikin harshen nufanci bayan sun iso tayi masa sannu da zuwa.

Ya tsine fuska tayi kamar mai son fashewa da kuka, kafin ta shiga sarke yan yatsunta kamar mai nazarin abin da zata fadi, dago idanu tayi ta dubi Mami wacce hankalinta kacokam! na kan Nusaiba din zaro idanu tayi kadan ganin yarda Mami tayin kicin-kicin da rai.

""Wei ga mei shi tupbo"
(Ke nake sauraro mana)".

Ya sake fadi yana mai dubanta fuskarsa da murmushi mai nuna cewa yana ji da 'yar tashi sosai da sosai.

"Dady...".

Ta fadi tana mai cizon laɓɓanta ta dora da fadin.

"Kawai Mia lotun bei annya..
(Kawai na fasa aiki da su...)".

Numfashin da taji Mami ta fesar ne, ya sanyata saurin dubanta tana dakatar da maganar da take yi, wata uwar harara ta ga ta watso mata kafun ta shiga fadin.

"Au! rainin wayon zaki kuma yi? To bari ki ji Allah in har sun dauke ki, sai kinyi aiki da su ai ba wani ya zaɓa miki ba, ke kika ce kin ji kin gani don haka duk yadda kika dama haka zaki sha kayan ki".

Ta san za a rina dama ta san Mami sai ta kalubalance ta akan batun nan in kowa ya yarda da ita ban da Mami.

"Haba mana bai kamata ba ki din ga takura mata har haka ba, ki barta ta fadi dalilin ta na kin aiki da su, bayan ta ansa a farko su take so yanzu ta canza ra'ayi kin ga kenan akwai dalili".

Dr.Kutigi ya tari Mami da fadin haka yana duban Nusaiba da tayi kasa da kai, tana faman wasa da jelar mayafin da ta naɗe kanta dashi, ba abin da take tunano wa sai HADUWARSU ita da shi mutumin ya ke kokarin canza mata fasalin rayuwa, mutumin da yake kokarin tayar mata da hankali a rayuwa, mutumin dake kokarin haifar mata da matsala mai girma a filin duniyarta, ba yarda za ayi ta anshe shi har ta zauna dashi a waje daya, da sunan aiki ba za ta iya ba, gwanda ta zauna a hakan babu aiki...

"Me yasa kika ce kin fasa Nusaiba, shin suna da aibu ne ko wani naƙasu a Company din na su".

Tambayar taji ta a bazata, ba tayi zaton Dady zai ja maganar da tsawo haka ba, ba ta san me zata ce masa ba, a karan kanta ba zata ce ga abin da zai hanata aiki da BKC ba duk da tana da dalili amma bazata iya fuskartar iyayen nata da hakan ba.

"Ai ba zata ansa ka da komai ba, saboda bata da gaskiya a lamarinta na lura so take yi kawai tayi ta wahalar mana da baki in ba don haka ba, ya za ayi tace ga wajan da take so yanzu kuma tace ta fasa abin da ba zai taba yuwuwa ba kenan, kuma wallahi Allah sai tayi aiki da su in baka manta ba akan idanunka muka yi TAQADDAMA na nuna mata ga wajan da nake so taki ansa ta nuna min raayinta, na bar ta don haka a yanzu bata isa ba tayi kadan".

Mami na gama fadin haka ta mike ta bar cikin falon ranta a haɗe.

Dr.Kutigi ya dubi Nusaiba da gabadaya jikinta ya gama saki sosai yaji tausayinta, sosai yake jin tausayinta a zuciyarsa yanayin sanyin halinta yana matukar damunsa bata son fadin abin dake damunta, sai dai ta bar wa ranta yayi ta cin ta.

"Kin ji batun Mamin ki sai kiyi hakuri Nusaiba ,in har baki da wani kwankwarar dalili na kin fara aiki da BKC".

Da sauri ta dago kai ta sauke idanuwanta da su ka kada kadan a saitin sa, tana faman gyaɗa kai kafun ta mike kan kafafuwanta da wani irin yanayi na rashin madafa, ta nufi dakinta zuciyarta na kara matsewa sosai da damuwa game al'amarin nan wanda ita akaran kanta ta zama sila...
[1/9, 3:27 PM] Denny Minna ZWA: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION*


Kamala Minna.
Kamalminna217@gmail.com


*MATAR MIJINA*


03.

Ta tabbata kenan sai tayi aiki da shi, ta tabbata kenan dole su zauna inuwa daya dashi.

Sosai zuciyarta ta shiga kai kawo, tana sake watso mata komai da komai, da kaddara ta zano mata gami da jeho mata Farouk cikin rayuwa, ba ta san ya zata yi ba, ba ta san wacce irin rayuwa zata ansa ba. In har ta yarda ta anshi aiki da Bkc, ba wai aikin ta tsana ba a,a kawai dai Farouk ne matsalar ta a wannan matakin.

Tana tsoron fushin Mami, sosai zuciyarta ke kara narkewa da wani irin rauni in ta tuna yarda suka kasance da Mami, ta sani tun farko ita ce ta haifar da komai dake faruwa da ita a yanzu.

Numfashi taja mai tauri, kafun ta buɗe idanunta da suke rufe tana zamewa zuwa kasa, daga jikin kofar da ta jingina.

Zuciyarta take ji tana kara matsewa, komai take ji na duniyar a yanzu ya sauya mata, bata san ya zata fuskanci wannan lamarin ba, wanda ta tabbatar dole a gareta ita ta zaɓawa kanta, ba wani ya zaɓa mata ba don haka komai ya faru da ita ita ce sila.

***

"Karfe Shidda har da rabi Nusaiba me ki ke nufi da hakan?".

Muryar Mami ta karaɗe mata kunnuwa, juya tayi kafun ta buɗe idanuwanta ta zame bedshit da ta rufe rabin jikin ta dashi, gabanta taji ya yanke ya fadi, lokacin da suka haɗa idanu da Mami kallon da take mata mai cike da alamun fushi, ya sanyata runtse idanu jin zuciyarta take kamar zata faso kirji tayo waje.

"Mami mana!".

Tayi kokarin fadi cikin wani irin yanayi, tana zuro kafafuwanta zuwa kasa, ta zauna sosai tana zabga tagumi.

"Ban son jin komai Nusaiba, kawai ki tashi tun kafin raina ya gama baci, ai dama na fada miki tun da kika zaɓi abin da kike so har kika samu, to ba ki isa ki zo mani da wata banzar magana ba na anshe ta".

Kanta taji ya yi wata irin sarawa da sauri ta dafe tana ambaton 'Yaa hayyu Yaa Kayyum' kokarin mikewa ta shiga yi, tana jin zuciyarta na kara matsewa da damuwar da take ciki ga kuma Mami da ta zo tana kokarin kara mata.

"Na baki minti biyar ki same ni a falo".

Muryar Mami ta sake dukan kunnuwanta, ba tace da ita komai ba illa gyaɗa kai da tayi, tana shiga tafiya saman kafafuwanta da take jin su wani iri.

Toilet ta nufa tana tunanin yadda zata anshi wannan lamarin, da take ganin sa ba komai bane a cikin sa sai tarin damuwa da ciwon rai a gareta.

Mintina sha biyar ta shafe cikin toilet ta fito, jikinta har zuwa lokacin bai saki ba komai yinsa take kamar wacce kwai ya fashewa a ciki.

Gaban Mirrow ta karasa ta zauna, zuciyarta na sake matsewa da wani irin yanayi musamman in ta tuna in da zata a yanzu haka, sai taji gabadaya tashin hankalinta karuwa yake bata san mai yasa hakan ba, duk da ta san haduwarta da waccan mutumin shine silar komai.

Zuciyarta take ji na kara kwaso mata wasu zantuka nashi suna maimaita kansu a gareta.

Runtse idanu tayi kafun a hankali ta bude su, tana kallon kanta a saitin madubin yanayin fuskarta take kallo idanuwanta sun kaɗa kadan, wanda hakan ya tabbatar mata da cewa rowar barci da tayi wa kanta a DAREN JIYA shi ya haifar mata da komai.

'Kina son matsawa kan ki da yawa Nusaiba'.

Wani sashi na zuciyarta taji tana sanar da ita haka.

Girgiza kai ta shiga yi ta sani ita ce ta jefa kanta a komai da take ji a yanzu, in da ba don ta so ba ba yadda za a yi har hakan ya haifar mata da yanayin da take ciki a yanzu, ko da yake ba ita ta assasa ba tuntuni Allah ya ƙaddara hakan gareta amma ita ce SANADI.

Sautin muryar Mami ta tsinkayo tana kwala mata kira a dan razane ta ware idanunta, da sauri ta mike ba tare da ta gyara fuskar tata da tayi niyya ba, gabadaya ji tayi bata muradin kwalliyar bata so sam-sama a yanzu, damuwar da take ciki ta isheta bata da lokacin da zauna har tayi wata aba wai kwalliya, duk da kaunar da ke tsakaninta da ita.

Da sauri ta karasa ma'ajiyar kayanta, buɗewa tayi tashiga yawata idanuwamta cikin wajan, kayane reras a shirye kala daban-daban numfashi taja kafun ta mika hannunta zuwa kan wata doguwa riga ja, wanda akayi mata surki da duwatsu masu ruwan Gold sai faman ƙyalƙyali take haka kawai taji tana son saka rigar a ranta taji ta burge ta kyautar Yaya Jaamal ne lokacin da yayi wata tafiya ya taho mata da ita bata taba saka taba.

A hankali ta maida murfin ma'ajiyar kayan ta rufe bayan ta zaro rigar gami da dan yalolon mayafinta. Kwance shawul din dake kanta tayi gashin kanta ya baje a gadon bayan sai faman sheƙi yake da daukar idanu yayi baki siɗik!.

A hankali ta shiga shiryawa lokaci guda ta fito fes! da ita, sosai rigar ta anshi jikinta bata kamata sosai ba, amma hakan bai hanna bayyana yanayin dirin halittarta ba rolling din dan yalolon gyalan tayi wanda ya bayyanar da kyankyawar fuskarta, wacce tayi fayau ba ɗigon tabo ko kadan sai dai da ka kalleta zaka gane akwai damuwa a cikinta, jakarta ta janyo gami da saka lapton dinta a ciki ta zura takalminta mai kama da silifas wanda samansa akayi masa kwalliya da wasu duwatsu masu kyan gani, hannunta daure yake da wani siririn agogo na zallar fata a hankali ta shiga taka kafafuwanta tana bin dakin nata da kallo, kafun ta isa bakin kofar tana buɗewa ta fice.

Sallamar da tayi ne ya sanya Mami dubanta sosai take karantar yanayin da take ciki, kafun lokaci guda ta dauke kanta tana jin wani iri game da 'yarta ta.

Bata san wani irin salon rayuwa gareta ba, bata san ya take jindadin rayuwa a haka ba,? kullum ace mutum kamar mara jini a jiki komai naka cikin sanyin jiki fuska kullum ba fara'a sai yanayi kamar na mai son fashewa da kuka.

"Ban san yaushe rayuwarki zata zama kamar ta sauran al'umman Nusaiba?, kullum sabon salo fitowa yake a duniyarki.".

Mami ta fadi tana tallabe haɓa, har zuwa lokacin da Nusaiba ta iso gareta tana faman sakin yaƙe, tana kokarin zama Mami tayi saurin tararta.

"Ke! Kin san kuwa karfe nawa yanzu, kike kokarin zama?".

Turo baki tayi gaba tana duban agogon hannunta 6:50 zaro idanu tayi kadan, kafun ta dago ta dubi Mami dake ta faman bin jikinta da kallo cikin yanayi na raunin da take hangowa a rayuwar 'yarta ta.

Laɓɓanta ta ciza kadan, tana rufe idanu gami da buɗe su lokaci guda.

"Coffee Mami".

Ta fadi tana mai dago hannunta gami da ɗora yatsunta biyu saman laɓɓanta, gami da kaɗa idanu kadan cikin yanayi na roƙo.

Wani kallo Mami ta bita dashi, kafun ta juya ta dubi dan karamin table din dake tsakiyar falon, gami da yi mata nuni da wani kyankyawar flask.

"Ba zan alamunci shiriritarki ba gaskiya, gashin nan ki dauka in kin karasa kin yi Breakfast din a can".

"Mami mana!".

"Kisan Allah duk taurin kan ki sai na nuna miki na shanye ki, bar ganin ina sakar miki Allah tsaf zan jaki da kaina na kai ki, tun da na lura banza zaki mai dani maza dauka ki bar mani gida tun kafin raina ya gama baci".

Duban flask din tayi kafun ta kau da kai, ta shiga takawa a hankali bata san mai yasa Mami ke mata haka ba, bata san mai yasa Mami taki fahimtarta ba akan aikin nan, ta sani ita ce tace taji ta gani amma yanzu ta sauya, amma Mami taki yarda da ita akan akwai dalili ta sani ko da ta faɗa mata dalilin ba tabbacin zata ansa lamarin a yadda ta dauki komai da zafi.

"Sai na dawo".

Ta fadi a can kasan makoshinta kamar wacce akayi wa dole.

"A dawo lafiya Allah ya tsare mani ke".

Murmushi ya kufce mata dama ta sani za a yi haka rigimar Mami na lokaci ne amma ka na yin abinda take so shikenan an shafe babin.

*****

Tunda ta isa Company din ta ji gabanta na sake tsinkewa yana faduwa, zuciyarta take ji tana matsewa da wani irin yanayi.

Bata so haka ba, bata so ace ta sake taka kafafuwanta har cikin BKC ba, zuciyarta taki aminta duk da kauna da so da ta nuna masa, amma cikin daƙiƙu komai ya sauya, komai ya canza a zuciyarta.

Numfashi taja mai zafi kadan, kafun ta buɗe murfin kofar motar ta ta kirar Ferari mai launi Pink sai daukar idanu take yi itama tana sahun tsarabar Yaya Jaamal.

Fitowa tayi a hankali tana miƙewa kan kafafuwant da take jin su wani iri daban ba ma kafafuwanta kadai ba hatta halittun jikinta jin su take wani iri.

"Mrs.Kutigi your first time kin fara latti anya kuwa kin shirya ansar aikin nan da muhimmanci?".

Wani irin bugu taji gabanta yayi, zuciyarta lokaci guda ta buga wani tsalle tana kokarin faso kirjinta runtse idanu tayi lokaci guda, gami da jan numfashi mai tafe da wani kamshi wanda ta tabbatarwa kanta kamshin daga jikinsa yake.

Bata taba zaton zata ganshi a saitin ta a daidai wannan lokacin ba, abin da ya sanyata duk ta hana kanta sakat! Kenan haduwa dashi ne bata son yi sosai take jin zuciyarta tana firgicewa, wanda bata san mai yasa haka ba tun haduwar su na farko a jiya take jin al'amura mabambata, suna samun gurbi a gareta suna hanata yin komai da komai.

Takunsa jinsa take yi kamar a kirjinta yake, gabanta ya iso jikinsa sanye da kananun kaya, wanda sukayi matukar ansar jikinsa fuskarsa da murmushi kamar ko yaushe sajensa da yakarawa fuskar tashi armashin kyau sai kyalli yake yi alamun ya samu gyara sosai.

"Jajircewar da na fuskanta kina da ita a jiya ashe ba haka abin yake ba, ban taba hasashena na samu akasi ba sai a kan ki me yasa haka? Na tabbata ba haka kike ba shin akwai wani abin dake ɗawainiya dake ne ko baki da lafiya ne shin ko akwai abinda bai miki bane a jiyan har yau kika kasa ganɗokin zuwa cikin hanzari ki a matsayin First Person da ta rigayi ko wani ma'aikaci a cikin BKC?".

'Yaa Rabb!'.

Zuciyarta ta furta jin tambayoyin daya shiga jero mata, kamar a gaban alkali a matsayin wacce ake tuhuma da laifi mai girma. Sosai taji kanta ya fara ansa da yawan maganganun nasa bata fiye son yanayi yawan magana ba ya cikin ajandar abubuwan rayuwarta.

"Uhmm?".

Ya fadi yana binta da kallo cikin wani irin yanayin wanda shi kansa bai san yana mata hakan ba, haka kawai yaji zuciyarsa na mikashi wani mataki na daban game da ita.

"Kina da damuwa ko? yanayin ki ya nuna ji fuskarki please tell me ko zan iya yin wani abu a kai bana son ganin yanayin fuskarki a haka kin ji ko".

Dago idanuwanta tayi tana saukewa a saitinsa a sakanni kuma ta dauke tana mai jan numfashi.

"Uhmm Afuwan kasan sabon shiga na saba da rashin tashi da wuri hakan ne yayi tasiri a tare dani...amma..hakuri..kayi hakuri wannan shine first and last".

Da wani irin yanayi mai rauni tayi kokarin haɗa kalaman, ta sauke su muryarta na rawa kadan sai faman wasa take yi da key din motarta, so take yi ya bata hanya sosai take jin kafafuwan na kokarin watsar da ita a kasa, ta gaji sosai da tsayuwar musamman a gaban wannan mutumin da take jin shine mutum na farko da yake kokarin rikita mata lissafin zuciyarta a lokaci guda wanda ta rasa dalilin hakan.

"Shikenan!".

Ya fadi da wani irin sauti kafun ya shiga juyawa yana dosar wani sashi daban na cikin harabar Company din, hakan ba karamin dadi ya yiwa Nusaiba ba don ji tayi kamar an sauke mata wani katon dutse mai kokarin karya mata duk wata gaɓa ta jikinta.

A hankali ta shiga taka kafafuwanta tana karasawa cikin Company din, zuciyarta na kara matsewa gami da tunanin yadda rayuwarta zata kasance a wajanta bata tsammanin zata iya jurewa musamman yadda taji ZUCIYARTA na kawo gajiya sosai da sosai.

*****

Bai san mai yasa zuciyarsa lokaci guda ta aminta da ita ba, tun kafin ya ganta cikin idanuwansa sunanta ya dinga masa kuwwa a kunnuwa gami da zuciyarsa.

Sosai yake jin danɗanon sunan yana samun muhalli a harshensa, yana jin wani irin garɗi na musamman da bai taba ji a duk wani suna ba, gani yake yi a duk filin duniya sunan 'Nusaiba Bukar Kutigi yafi na kowa.

Juyi yake yi hannunsa dauke da karan sigari sai faman zuka yake yi cikin yanayi na gwanancewa, yana fesar da hayaki ta baki da hanci idanuwansa sun kaɗa sun jajir fuskarsa da wani guntun murmushi kamar ko yaushe.

Tun da yake a duniyar nan bai taba jin wani irin yanayi na daban ba, tare da wata ɗiya mace sai akan Nusaiba Bukar Kutigi sosai yake ji zuciyarsa da ruhinsa na buɗewa da wani irin al'amari na musamman wanda shi a karan kan sa ba zai ce gashi ba.

Numfashi yake ja a hankali yana lumshe jajayen idanuwansa, yana buɗe su cikin wani irin yanayi mai ruɗa duk wata ƳA MACE.

Murmushinsa ya shiga faɗaɗawa jin zuciyarsa na kara ƙawata al'amarin da yake tunani akansa, wani irin yanayi yake jin zuciyarsa na miƙashi na musamman wanda bai taba tsintar kansa a ciki ba.

Wayarsa ce ta dau ruri a hankali ya shige buɗe idanuwansa da suke lulluɓe, ya shiga duban wayar lokaci guda fuskarsa ta canza daga yanayin da take ciki, tashi yayi sosai daga shingiɗan da yake yana faman jan tsuki kamar zai tsinke harshensa.

Bai bi ta kan wayar ba har lokacin da ta gama ihunta karo na ba adadi, tashi yayi sosai kan kafafuwansa ya zagayo zuwa tsakiyar Office din nasa, sai faman lumshe idanu yake yi kamar mai jin barci.

Kwankwasa kofar aka shiga yi a hankali, ya tsagaita da tafiyar da yake yi, ya shiga bin kofar da kallo kamar wanda ya ga sabon abu haka kawai yaji zuciyarsa wani iri baya kaunar ko waye ya shigo duk da a tsarin sa bai damu ba, ba ya jin kunyar kowa waye ya zo ya tadda shi yana karawa gajimare hazo, amma yau daya kacal yaji zuciyarsa bata so a tadda shi a hakan.

Ya tsine fuska ya shiga yi yana harɗe hannyensa saman kirjinsa, cikin wani irin salo mai kama da Style sai kara buɗe idanuwansa yake yi a kofar.

"Yes Come In".

Ya fadi da wata irin murya maras sauti sosai.

Ba a shigo ba tsayin sakanni har ya fidda rai za a shigo, tsaki ya ja a daidai lokacin da aka turo kofar wani kamshin Turare mai dan karan hawan kai da kamshin dadi yaji ya yi masa sallama, da sauri ya dan ja baya kadan sa'ilin da ya hango kafar da ta sanyo kanta cikin Office din, mutuwar tsaye ya yi na yan dakiƙu kafun ya dawo hayyacinsa yana mai da numfashi mai tauri, zuciyarsa yaji ta buɗe gabadaya yanayin sa ya sauya sosai yaji gabansa ya shiga bugu amma duk da haka bai bari hakan yayi tasiri a zuciyarsa ba.

Mamaki al'ajab da almara duk suka dire masa lokaci guda, abin da bai taba faruwa dashi ba ko ma ya taba faruwa dashi to da jimawa yau shine gabansa yake cikin fargaba da wani irin yanayi akan wani zai shigo gareshi girgiza kai ya shiga yi, yana tura laɓɓansa masu duhu cikin bakinsa yana cizawa.

Gabadaya gangar jikinta suka dire a tsakar Office din, bakinta dauke da sallama, hannayenta dauke da wasu fiyal fiyal kanta a kasa sosai taji gabanta ya yanke ya fadi, a sa'ilin da kofofin hancinta suka shako mata wani irin wari don ba zata kira shi kamshi ba, sosai ta fahimta sosai ta gane abinda ke faru gabanta taji ya yanke ya fadi, da sauri ta tsaya cak! jikinta har rawa rawa yake yi don tsoro.

"Uhmm...afuwan..Ban san zan tadda hakan ba cikin uzuri...kayi...hakuri...".

Dif! taji bakinta ya kulle ta kasa karasa datsatsun kalaman da take jin fadin su kamar an shakar mata wuya anyi mata dole.

Ɗago idanuwansa yayi sosai ya sauke a gareta da wani irin yanayi, har zuwa wannan lokacin da murmshin nan da ya zame masa jiki.

Ja da baya ta shiga yi wanda ba ta san dalilinta nayin haka ba, haka kawai taji gangar jikinta da zuciyarta suna sarrafata yadda suke so har takai bakin kofar tana kokarin ficewa idanuwanta a kasa.

Kofar da ta jiita lokaci guda an rufe ya sanya ta saurin dago idanuwanta, tana buɗe su Farouq ne tsaye jikin kofar idanuwansa a lumshe hannayensa suna nan yadda suke harɗe a kirjinsa da kafarsa yayi amfani ya tura kofar ya rufe ruf!
Dubansa take yi da wani irin yanayi idanuwansa take kallo, wani irin al'amari take hangowa wanda sam take ji babu dadin a ranta haka kawai taji wani abu ya tokare mata zuciya mai kama da bakin ciki, duban sa take yi fuskarta a haɗe kamar bakin hadarin da ya gangamo yake kokarin zubda ruwa.

"Me yasa zaki koma bayan baki yi abin da ya kawo ki ba?".

Ya fadi yana dubanta da buɗaɗɗun idanuwansa kau da kai tayi, da saurin don ba zata iya cigaba da kallon sa da irin kallon da yake mata ba, zuciyarta take ji babu dadi zuciyarta take ji tana shiga kunci zuciyarta take ji tana mikata wani mataki na rashin armashi.

"Ina jin ki Ms.Kutigi".

Ba wai bata shirya ansar sa a yadda yake bane har tayi abin da ya kawo ta, amma bata zaton zuciyarta zata iya tsayawa da shi har na tsayin lokacin da zai gama mata abin da ta zo bukata.

Dago idanuwanta tayi tana dubansa kafun ta sake sauke kallonta, zuwa kasa a hankali take taka kafafuwanta wani kwarin guiwa ne taji ya zo mata ta isa cikin Office din sosai ajje Fiyal din tayi saman Table din sosai kafun ta juyo har yanzu yana inda yake tsaye yana dubanta baki a buɗe.

Handle kofar ta rike duk da ya rufe kofar kaɗan, amma hakan bai hanata kau da komai na fargaba a gareta ba, ta tura kofar sosai har tana shafarsa ta ficewarta zuciyarta da wani irin yanayi wanda ta kasa tantacce shi.

Farouq yabi kofar da kalau kafun ya ajje wani numfashi mai kwari, sosai fuskarsa ta shiga matsewa a hankali idanuwansa yana lumshewa ya jingina da kofar sosai kamshin da tun ɗazu ke masa yawo a kofofin hancin sa shine sai yake ta faman shaka wanda yake jinsa har cikin kwanyarsa da zuciyarsa da sassan ruhinsa.
[1/9, 3:28 PM] Denny Minna ZWA: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION*


Kamala Minna.
Kamalminna217@gmail.com


*MATAR MIJINA.*



04.

Tagumi ta zabga zuciyar ta sai faman sukuwa take yi, akan mutumin da lokaci guda take jin sa a zuciyarta.

Bata san mai yasa haka ba, bata san mai yasa lokaci guda take jin komai na rikiɗe mata ba?. Sosai take jin komai na duniyar na canzawa zuwa lamarin sa.

Kiyayya ce tsana ce bata san a matsayin da za ta ajje shi ba.

'Me yasa kika damu kan ki, da tunanin mutumin da bai shafi duniyar rayuwarki ba, ki ke kokarin barin sa ya faɗo miki rayuwa ya rikita miki lissafin tunanin?'.

Zuciyar tace ta shiga kwaso mata zantukan, wadanda take jin su wani irin bambarakwai.

Girgiza kai ta shiga yi, tana daga hannayenta daga madannan Computer din dake gabanta.

Runtse idanu tayi, gami da tura yatsunta biyu cikin baki tana cizawa.

"me yasa haka, mai yasa nake kokarin barin lamarin mutumin nan yayi tasiri akai na?".

Ta shiga furtawa can kasan makoshi, kamar wacce aka yiwa dole.

Duban agogon hannun ta tayi lokaci guda ta zaro idanu kamar wacce taga mugun abu, da sauri ta sake buɗe su sosai.

"Yaa Rabb! har yaushe lokaci ya tafi haka ban sani ba, anya kuwa lafiya ta kalau ni Nusaiba?".

Mikewa tayi tana tattare kayan ta komai da komai, da ta san ita ta zo dashi jakarta a kafaɗarta, ta suri wayarta da Car-key dinta.

Sai da ta karewa Office din kallo sosai, wanda yake a matsayin nata kafun wani murmushi ya kufce mata wanda bata san hakan ya faru da ita ba.

A hankali ta shiga takunta har ta fice gami da jan kofar, sosai ta ga raguwar ma'aikata irinta, sosai ta ga duk sun tafi alamu ya nuna kenan ta yi lattin ta shi.

"Na zo a latti na tashi a latti".

Ta furta a hankali, tana karasa ficewa zuwa inda ta ajje motar ta. Sosai taga raguwar motoci a wajan, sai dai mota daya da ta gani har ta kure ta da idanu, haka kawai taji motar ta burgeta sosai a rai taji tana sha'awar ace ta mallaki irinta, duk da bata fiye son bakin abu ba amma wannan baƙar motar ta tafi da zuciyarta.

Sai dai abin da Nusaiba bata sani ba, shine motar da ta zubawa idanu ba kowa bane illa Farouq, duk abin take yi akan idanunsa ne.

Motsin da taji ana kokarin buɗe ta ne ya sanya saurin kau da kanta, tana jan tsaki can kasan makoshinta a hankali ta isa zuwa motar ta, ta rike kenan zata buɗe ta ji saukar sautin muryar da ta ki jini ta ji.

"Ms.Kutigi tun yau kin fara kaiwa wannan lokacin a Office, tun ɗazu nake zaman jiran ki, don ban yi zaton kaiwar ki war haka ba".

Wani nauyi taji zuciyarta tayi mata, a hankali ta saki marikin motar tana mai da numfashi, haka kawai taji tana bukatar dubansa ta gaya masa maganar da zai sanya ya rabu da shiga lamarinta ba ta so, ba wai don tana aiki dashi bane hakan zai ba shi lasisin takura mata.

Hannayenta ta daura saman kirjinta ta harɗe, a hankali ta juyo tana ajje kallonta a saitin sa. Jingine yake jikin motar tashi shima, hannayensa harɗe fuskarsa da murmushi kamar ko yaushe ya daura kafarsa daya kan daya.

Duk wani kuzarinta da ta juyo gami da abinda tayi niyyar yi, lokaci guda ta ji ya rushe komai ya shafe kamar ba ita bace mai kudirin aniyar gargaɗi gareshi, bata san lokacin da ta saukar da idanuwanta zuwa kasa ba, gabanta taji yana wani irin bugu bakinta na rawa sosai abubuwan da take hangowa cikin idanuwansa wadanda ta bar su a matsayin kwarjini da cikar zatin sa ne suka rusa mata komai.

"Fadi abin da kika yi niyya, na san kin juyo ne don cewa wani abu ina jikin".

Ya fadi yana tashi daga jikin motar ta shi, yana takowa zuwa gareta hakan ya kara rusa mata duk wata natsuwarta.

Ba wai tsoron sa take ji ba, ba wai kuma ba zata iya ce masa komai ba ne, a,a zuciyarta da gangar jikinta ta rasa abin da suke nufi, komai ji take yi suna sauya akan sa.

"Na takura miki ko Nusaiba? Karki damu kin ji ko, ba abin da zan yi miki ni kaina ban so haka ba, kawai dai ba yadda zan yi ne".

Kalamansa sosai suka samu gurbi a zuciyarta, suka haura kwanyarta suka shiga sakin kuwwa. Mamakinta ya daɗa karuwa sosai, yadda ta ji yana sakin kalaman da wata irin murya da bata taba jin wani yayi amfani da ita ba, wajan magana ita a karan kanta za ta iya cewa tun da take a filin duniyar nan bata taba jin mutum mai taushin lafazu kamar Farouq ba, lokaci guda taji zuciyarta ta fizgeta da wani irin yanayi mai girma.

Runtse idanu tayi kafun ta dago kanta, sosai ta ajje kallonta a saitin sa zuciyarta na sake kecewa da bugu.
Bata san mai yasa lokaci guda take jin ta wani iri ba, haka kawai ta ji mutumin da sam bai mata ba take jin zuciyarta ta addabeta da lamarin sa.

'yawan tunanin mutum da kula shi yana sahun dangogin alamun so'.

Wata irin firgita tayi, har sai dashi Farouq din ya dago sosai yana dubanta, idanuwansa a waje cikin yanayi tambaya ita kanta ta san jikinta ya bayyana yanayin da take ciki, laɓɓanta suka shiga motsawa a hankali cikin yanayi na rawa, alamun tana son magana amma batutuwan da taji zuciyarta ta kwaso mata hakan ya rikita mata lissafi.

"Yaa Rabbi meye haɗi na dashi, har da zuciyata zata kawo mani waɗannan rikitattun kalaman".

Abin da ta shiga faɗi kenan tana danne laɓɓan nata da yatsunta, mamaki ne yake son kashe ta amma kuma maganganun take jin su kamar wasu abubuwa ne na musamman yadda taji zuciyarta na SAFAH DA MARWA akan su.

A hankali ta shiga juya kafafuwanta da take jin su kamar za su watsar da ita a filin wajan, zuciyarta take ji tana kara matsewa gami da buɗewa duk a lokaci daya akan Farouq.

Kokawa ta shiga yi da zuciyarta wajan karyata lamarin, da take kokarin dasa mata shi akan dole ta ansa ko taki ta so, ita kuwa ba yadda za ayi ta anshi lamarin nan da bata san ina zuciyarta ke kokarin kai ta ba in da komai zai rushe mata bata san mai yasa zuciya take haka ba?.

'Mene ne Laifin Zuciya?'.

Kwanyarta taji ta ansa kuwwa da kalmomin wanda bata san daga ina suka taso suka sauka akan ta ba.

Bata san ta buɗe motar ta har ta shiga ba, sai da ta tsinkayo muryar Farouq daga nesa sannan tayi firgigit ta dawo hayyacinta. wani GWAURON NUMFASHI ta ajje kafun ta dago idanuwanta da suka ƙanƙance kadan, ta dube shi har yanzu yana tsaye inda yake fuskarsa na dauke da murmushi sai faman shafar sajen fuskar shi yake yi, cikin yanayi na nuna alamun ba abin da ya addabe shi.

Key tayi wa motar kafun ta fizgeta cikin yanayi na aikin zuciyarta, ba wai akaran kanta ba ta fice daga Get din zuciyarta da wani abu mai girma wanda ya yi matukar ɗaure mata kai.

*****

"Farouq".

Juyo ya yi cikin yanayi na mai jin barci, sai faman lumshe idanu yake yana buɗewa a saitin matar dake tsaye gefensa, fuskarta a haɗe kamar wacce take shirin rufe shi da bugu.

"Please Nasreen mana ki rabu dani nayi barci".

"Kamar ya na barka kayi barci? bayan kuma kasan abin da ya sanya ni na zo gareka yanzu".

Tsaki yaja gami da mikewa ya zauna, wani abu yake ji ya zo masa saitin zuciyarsa ya tsaya cak! ji yake yi kamar ya shakota ya buge ko ya huce haushinsa kan katse masa barcin da yake yi, mai cike da mafarkai masu dama wanda suka canza masa duniyarsa lokaci guda, ba tare da ya sani ba komai yake jin sa a nishaɗi, komai yake jin sa a farinciki, komai yake jin sa a muraɗi mai matukar burgewa gare shi.

"Wulakancinka ya fara isa fa!".

Wani kallo ya watsa mata kafun ya sanya hannu yana shafe fuskar sa.

"Wulankacin na ne ya fara isar ki?".

Wani murmushi ya saki kafun ya saita ganinsa sosai a gareta.

"Ni ban miki wulakanci ba, sannan ni ban iya wulakanci ba, ke ce dai a karan kanki duk kika azawa kan ki abubuwan da kike faɗi na yi maki".

Zaro idanu tayi sosai jin kalaman Farouq akanta, wani irin kunci da takaici take ji na fesowa a ko ina na sassan jikin ta, ji take yi kamar ta rusa ihu ko ta samun saukin wulakanci da halin-ko-in kula da Farouq yake a gareta, ita fa matarsa ce matar aure bai wai MATAR WANI ba, balle yace ta zo gareshi da wata manufa ya ji dadin gaya mata abin da ransa ke so.

Numfashi ta fesar kafun ta gyaɗa kai cikin yanayi na nuna damuwarta a fuska sosai, Farouq bai son ta, Farouq bai kaunarta, bata san mai yasa haka ba, bata san mai yasa yatsane ta ba a duniyarsa?.

"Ki tashi mani daga kai, ina bukatar runtsawa don Allah na roke ki".

Wasu hawaye ne masu dumi taji sun sauko mata akunci, da sauri ta sanya hannu ta shafe su murmushi na bayyana sosai a fuskarta ta, wanda hakan bai hana ka gane damuwar da take ciki ba.

A hankali ta shiga juyawa kafafuwanta da rauni kanta take ji yana juya mata kamar zata zube a kasa, numfashi take ja mai cike da takaici da bakin cikin Farouq Ma'arouf Kutigi.

Bata san mai yasa ta aure shi ba, bata san mai yasa ta bari zuciyarta ta ajje GURBIN SO na Farouq a gareta ba, ta sani Farouq baya son ta ba ya kaunarta ko kadan, amma bai kamata ace yana nuna mata hakan ko ba so a tsakani akwai zumunci ZUMUNCINSU zai duba, ko ba kauna da so a tsakaninsu ya sot da son ZUMUNCINSU amma hakan duk babu.

Duk abinda Nasreen ke yi akan idanuwansa har sai da ya ga ficewarta daga cikin dakin, ya ja tsaki gami da komawa ya dunkule waje daya zuciyarsa da wani irin yanayi akan Nasreen, ko kadan ba ya jinta a ransa, ba ya jin zai iya bata wani abu mai girma wanda take ganin in har ma yace zai bata ko kadan ya yi wa rayuwarsa mugun cuta, don ko kadan baya jin zuciyarsa zata iya son Nasreen. Ba wai tsanarta ya yi ba, kuma bai wai kiyayya ce ba, kawai zuciyarsa ce taki yadda da ita a matsayin MATAR SO gareshi.

Zuciyarsa ƙiwa take masa, ko ya yi kokarin baiwa Nasreen kashi goma ne na cikin kashi dari din da ya yi tanadi na so, ga wacce yake fatan ya so ba wai Nasreen ba wacce yake kallo a matsayin matar HADIN ZUMUNCI.

Shasshekar kuka ya tsinkayo yana kokarin gyara kwanciyarsa, haka kawai yaji wani kunci ya ziyarce shi ya san Nasreen ne, in da sabo ya kamata ace ya saba da wannan kukan nata, ba abin da yafi tsana yaji tana kuka bai san wacce irin zuciya gareta ba bai san mai yasa ta zaɓi zama dashi b,a bayan kuma ta san baya sonta ya kamata ta ceci kanta kawai ta tafi gidan su.

'Ka sake mata ai komai a hannunka yake, yanzu ko ka manta matar ka ce ba matar wani ba'.

Tsuki yaja kamar zai tsinke harshensa, a sa'ilin da yaji zuciyarsa na tunatar dashi Nasreen. Gyara kwanciyarsa yayi gami da dunkulewa cikin bedshit din gadon, zuciyarsa na sake hasko masa abin da ya gama mafarki akai.

*****

mikewa tayi jikinta sanye da kayan barci ta kunna fitila mai haske wacce ta haske dakin gabadaya kamar rana tsaka zama tayi bakin gadon ta na zabga tagumi kafun ta daga kanta ta dubi agogon dake jikin bangon 1:30 abinda idanuwanta ta gani kenan wani numfashi taja mai tauri kafun ta fesar dashi tana sake tallaɓe haɓarta.

Me zuciyarta take son sanar da ita.

ba dai so ne ba yake kokarin samun gurbi a cikinta ba, ba dai so ne ba yake kokarin shigowa rayuwarta ba tare da tsammani ba, ba dai son mutumin nan bane yake so farka mata zuciya lokaci guda.

Rufe idanu tayi ta buɗe lokaci guda ba abin da take gani sai Farouq Ma'arouf Kutigi mutumin da ta ji zuciyarta ko kadan bata muradi tun a kallo daya ta ji zuciyarta tana kokwanta akan sa komai take ji na shi ya mata wani iri a cikin yan kwanakin nan da ta fara aiki dashi.

Mikewa tayi ta shiga kai kawo zuciyarta na sake yi mata lale marhabin akan abin da ta zo mata dashi.

Bata taba so ba bata taba kula wani saurayi da sunan so ba tunda take domin ba shine a gabanta ba bata dauki so a lokacin kuruciya musamman ana karatu a matsayin yi ba sannan bata taba kawo wa ranta zata fuskanci so a cikin irin wannan lokacin ba idan har zuciyarta tayi mata haka bata kyauta ba ta ba ba ta shirya so ba bata shirya yin sa a wannan matakin ba ba wai taje BKC bane a salon samun soyayya taje ne a matsayin ma'aikaciyarsu me tasa zuciyarra za tayi mata ganganci har haka sam-sam Farouq Ma'arouf Kutigi bata tsammani rayuwarta da tashi za su zauna inuwa daya ba dacewa a tsakanin su.

Mikewa tayi sosai bisa gadon bayan ta kwanta akan sa tayi ringingine kanta a sama idanuwanta sosai suka buɗe ba wani alamun barci a cikin su ba abin da zata ce ta jima rabonta da shi wato rashin barci bata taba kai wa tsawon lokaci kamar wannan bata yi barci ba ko da kuwa tana wani aiki amma ace a yau ita ce take raba dare akan wani mutum.wanda bata san waye shi ba labarin sa take ji amma daga haduwar farko ace ya firgita mata zuciya da rayuwa ina! hakan ba mai yuwuwa bane.

Runtse idanu tayi da karfinta don kawai samun barci amma abinda take gani cikin rufaffun idanuwanta yayi matukar bata mamaki gami da al'ajabi da sauri ta buɗe idanuwan nata tarwai gami da mikewa zaune tsakiyar gadon.

"Yaa Rabbi wani irin lamari ne wannan Yaa Allah ka zuciyata ta gane wannan lamarin ba wai mai yuwuwa bane Yaa Rabbi ka ganar da zuciyata sam-sam ba abin burgewa a lamarin nan".

Abinda ta shiga fadi kenan tana faman girgiza kai kamar ita da wani take maganar kafun lokacin guda ta koma ta kwanta gami da jan bedshit din tana lullube kanta gabadaya.

*****

"Jamaal".

Mami ta fadi tana dubansa, hannunta rike da jaka.

Ajje glass-cup din yayi bakin sa cike da plantanin.

"Wai yaushe zaka koma ne?".

Murmushi yayi yana mai kara mai da hankalinnsa sosai ga Mami.

"Mami har kin gaji da ganina kenan ko shikenan na kusan barin gidan".

Murmushi tayi tana gyara zaman babban mayafin dake jikinta.

"Jamaal mana! Ka fiye rigima wallahi, meye na fadin haka akwai abin da nake so kayi mani ne a satin, domin bani da hutu sosai kwanakin satin nan ina da shari'o'i masu dama ban so na takura kai na ne".

Jin abin da tace ya sanya shi saurin mikewa daga inda yake zaune ya iso gareta gami da riko jakar hannun ta.

"Muje na kai ki".

Tsuru tayi masa da idanu, ta san abinda yake nufi da hakan don haka ta dan bugi kafaɗarsa gami da murmushi.

A daidai lokacin Nusaiba ta iso falon, fuskarta da wani irin yanayi.Mami ce ta tsaya da tafiyar da take yi tana kure ta da idanu sosai.

"Nusaiba!".

Ta kira da wata irin murya wacce ta sanyata tsayawa cak! A inda take tsaye, tayi kasa da kai don ta jiyo alamun tuhuma da gargaɗi a muryar Mami.

"Meye haka a fuskar ki?".

Ta sake fadi tana kara tsuke fuskarta.

Jamaal dake tsaye yana duban Nusaiba shima da sauri ya isa gareta, yana sanya hannunsa ya dago haɓarta ya saka idanunsa cikin nata.

"Faɗa mani me ke damunki har haka, kin ga kuwa fuskar ki Nusee whats is wrong with your you look so sad?".

runtse idanuwanta tayi ta sani dole sai ta fuskanci haka a garesu, in har suka ganta ita kanta ta san bata kyautawa kanta ba, sosai da sosai amma ba yadda da iya LAIFIN ZUCIYA ne da take kokarin jirkice mata rayuwa a wani gurbin da sam bai dace ba.

"Ka rabu da ita nace!".

Muryar Mami ta karaɗe falon da sauri Nusaiba ta ja da baya kwalla na zubo mata.

A hankali ta tako ta iso gare su, duban Jamaal tayi kafun ta sauke idanuwanta masu dauke da tuhuma sosai a saitin Nusaiba.

"Me ya hanaki barci har haka, ji idanuwanki ji fuskarki yadda ta sauya kina da hankali kuwa Nusaiba kina son rayuwarki da farinciki kuwa?".

"Mami mana don Allah ki rabu da ita ki barta haka, ba ki san abin da ke damunta ba ki bari ta faɗi mana".

Wani kallo ta watsa masa kafu ta mika masa hannu.

"Bani jakata na san darajar lokaci, na nasan darajar aikina. Ka zauna ku yi duk abin da za kuyi, lamarin Nusaiba ya fara isa ta tun yaushe...tun yaushe nake mata magana ya kamata ace a matsayina na mahaifiyarta ta sanar dani damuwarta, bata da wanda yafini bata da wanda ya dace ace ta duba da damuwarta kamar ni, in ma tana jin kunyata ba ga ka nan ba, amma ta nuna ba mu kai matakin da za ta iya faɗa mana matsalolinta ba".

Tana gama fadin haka ta fizge jakarta.

"Allah ya shirya min ke Nusaiba ya canza miki wannan baƙin halin naki".

Tana gama fadin haka ta fice da sauri.

Jamaal na kiranta amma ko ta kansa bata bi ba, juyowa yayi ya dubi Nusaiba da take ta faman sharar kwalla.

"Kina da matsala Nusee, ban san me yasa kike son ɓatawa Mami ba, kin san halinta ba tun yau ba bata son boye abu ko me ke damunka tafi kaunar ka sanar da ita amma ke kin kasa gane hakan".

Dago jajayen idanuwanta tayi ta sauke a saitin sa, wani kuka take ji yana kokarin balle mata da sauri ta sanya hannu ta toshe bakinta, tana girgiza kai. Hannunta ya ja ya zaunar da ita kafun ya mike ya isa wajan Dinner ya kwaso kayan karin nasa da yake yi ya iso gareta ya ajje, dubanta yayi da idanuwansa masu sanyata saurin natsuwa.

"Dauka ki yi breakfast".

Sauke hannunta tayi daga bakinta, ta dauki Glass-cup din mai cike da hadadden Tea mai kauri ta kai bakinta kadan ta kurba ta sauke, ji take yi kamar ta kurbi maɗaci runtse idanu tayi ta haɗiye daƙyar.

Dubanta yake yi cikin yanayi na tausayi, da irin raunin da take ciki halayenta sun fiye rauni da yawa, bai san mai yasa haka ba halinta da daban rayuwarta daban komai ma nata ya fita daban a gidan...


*kamala Minna*.😘😘
[1/9, 3:28 PM] Denny Minna ZWA: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION.*


Kamala Minna
Kamalminna217@gmail.com


*MATAR MIJINA.*


05.

"Sosai za ki sha, ban so naga kin rage ko kadan ne a ciki".

Jamaal ya fadi, cikin yanayi na rashin wasa.

Hakan da Nusaiba ta gani ya sanyata, sake daukar cup din ta kai bakinta, duk da rashin dadin danɗano da take ji a harshenta kamar zata yi amai hakan bai hanata runtse ido ta yiwa Tea din ƙyanƙyawar zuƙa ba.

Kafun ta dire kofin idanuwanta a runtse, zuciyarta take ji tana murɗewa tana kokarin dago kirjinta kamar zata amayar da kayan cikinta.

"Next".

Ya fadi yana nuna mata plat din soyayyiyar plantanin din. Zaro idanu tayi kadan, kafun ta shiga tura laɓɓanta cikin bakinta tana cizawa.

"Don Allah Ya Jamaal cikina kamar zai fashe, ka rabu dani ba zan iya ba".

Ta fadi da rawa a muryarta, kamar zata fashe da kuka.

Tagumi ya zuba yana yi mata wani irin kallo, mai dauke da tuhuma sosai. Kafun ya numfasa har zuwa lokacin fuskarsa ba alamun wasa.

"Common Wannan ruwan banzan da kika sha shine kike ce mani cikin ki kamar ya fashe, me kika ci bayan wannan ruwan Tea din faɗa mani me kika ci?".

Girgiza kai ta shiga yi tana ɗaura yatsunta biyu a fuskarta, tana dauke ƙwallar da suka fara zubo mata.

"Kin san bana son wannan kukan ko na rashin dalili".

"Ya Jamaal ban san abinda ke damu na ba, amma Mami take fushi dani kaina ne fa ya ke ciwo tun jiya".

Ta fadi kanta a kasa. Tana jin yadda kirjinta ke bugawa kadan-kadan, bata so ta haɗa idanu dashi ta sani sai ya fassara maganar da tayi masa, kuma tabbas zai iya gano gaskiya.

"Kalle ni Nusee!".

Runtse idanu tayi tana jin yadda kanta ya sara, da sauri ta saka hannayenta tana dafe kanta.

"Ban yarda da abin da kika ce ba Nusee, akwai abinda ke damun ki a zuciyarki kike boye wa, fuskarki ta nuna akwai damuwa tattare dake".

"Allah Ya Jamaa...".

"Tashi ki wuce lokaci tafiya yake yi zaki makara".

Dago kai tayi tana dubansa yanayin sa ba alamun fushi sai dai kuma ba walwala a tatare dashi, miƙewa yayi saman kafafuwansa yana dauke kayan Breakfast din.

"Muje na kai ki don ba zan barki kiyi tuki da kan ki ba, akwai damuwa a zuciyarki sosai da sosai".

Jamaal ya faɗi bayan ya kai kayan hannunsa zuwa Dinner din, ya dauki ƙey dinsa ya yi hanyar fita.

Ita kuwa ƙyam! ta tsaya tana dubansa har ya kai bakin kofa, rashin motsinta da yaji ya sanya shi tsayawa gami da juyowa, ganinta tsaye ya sanyashi harɗe hannayensa a kirji yana dubanta, da wani irin kallo na rashin fahimta. Kasa tayi da kai, tana wasa da yatsun hannunta.

"Ko ba zaki aikin bane yau?".

A hankali ta shiga taka kafafuwanta da take jin sun mata nauyi, tashiga tafiya hakan da ya gani ya sanyashi buɗe kofar ya fice.

Cikin motarsa ta tadda shi zaune, wayarsa a kunne yanayin fara'ar dake fuskarsa hakan ya sanyata sakin baki, tana masa wani irin kallo na mamaki sauke wayar ya yi ba tare da ta san ya yi haka ba, har ya sauke idanuwansa a gareta.

"In kin gama kallo na ki zo mu wuce, don na lura sabon mutum kike gani ba wai Jamaal din da kika sani ba ne".

Murmushi tayi wannan iyakarsa laɓɓanta, ta rufe fuskarta da haɓar mayafinta, cikin sauri ta karasa ta buɗe motar ta shiga ta zauna kanta a kasa.

"Nusaiba!".

Taji ya kira sunan nata da wani irin amo mai sauti, da sauri ta dago kanta ta sauke idanuwanta a saitin sa, shima ita yake kallo.

"Baƙya son aikin ne? in har baƙya so ki faɗa mani sai a canza maki, ba zan iya cigaba da dubanki cikin wannan halin damuwar ba, zuciyata ba zata iya dauka ba kin dai sani in har akwai mai takurawa rayuwarki ki sanar dani".

Girgiza kai ta shiga yi, zuciyarta na miƙata wani mataki wanda ba za ta ce gashi ba, ba zata iya duban Ya Jamaal tace ga damuwarta ba. Shin in tace ma zata faɗa masa mene sanadin damuwar me zata ce ya kawo mata damuwa a duniyarta.

***

Shafe hawayen da suka zubo mata a ƙunci tayi, tana mai jan hanci ta dago idanuwanta ta sauke a saitin sa, zuciyarta take ji tana kara buɗewa da son sa son da ta jima tana tanajin sa, duk a dalilinsa zuciyarta tuni ta rufe kanta da kaunarsa ta jefar da mukulli acan kasar maliya sai dai kash! Ashe duk haukarta take yi bata san cewa ba so a zuciyar Faruoq nata ba ashe ba kaunarta a zuciyarsa ko kadan bata san ya za ta dube shi ba bata san ya zata yi jinyar kanta da son mutumin da bai son ta ba.

Burinta tayi aure ta sami miji da zai yi mata tattali ya dauke ta ya mai da ita wata mace wacce tafi kowa daraja a duniyarsa macen da zai nunawa kulawa da so da kaunarsa duka ya daura mata sai dai ashe ba haka bane tayiwa kanta bahagon tunanin da ya zame mata ciwon rai ya hana zuciyarta sak!.

"Farouq!".

Ta fadi tana mai tura laɓɓanta cikin bakinta tana cizawa wani irin kunci da damuwa take ji yana taso mata tun daga kasar zuciyarta ji take kamar ta rushe da kuka ko ta samu sauki sai dai tayi wa kanta ALKAWARI ba zata taba sake kuka akan Farouq ba za ta yi hakuri ta zauna dashi a duk yadda yake so sai dai ya sani ko ajalinta ya zo to son sa ne sila.

Juyowa ya yi yana dubanta fuskarsa ba yabo ba fallasa kau da kai ya yi sa'ilin da yaji zuciyarsa na fizgarsa ganin yanayin da Nasreen ke ciki.

"Ban san mi zan ce miki ba Nasreen...".

Da sauri ta daga masa hannu tana tashi daga bakin gadon da take zaune muryarsa sosai take taɓa mata zuciya a duk lokacin da ya furta irin wannan kalamin gareta sosai zuciyarta ke kumbura kamar zata faso kirjinta ta fito kanta taji ya fara juyawa da sauri ta daura hannayenta duk biyun tana dafewa.

"Yaa Rabb!!!!."

Ta furta daƙyar daga can kasar makoshinta tana jin yadda zuciyarta ke wata irin kartawa sautin muryar tashi tana kara rikita mata lissafi bata san yadda aka yi ta faɗa tarkon son Farouq lokaci guda ba har ta amincewa kanta shine ABOKIN RAYUWA agareta sai dai ashe ba haka bane tuni lissafinta ya faɗi mata karya gashi dai ta aure shi da sunan samun kulawa da tattali daga wajansa a matsayin miji sai dai sam-sam ba hakan.

Idanuwansa yake saukewa a duk wani sashi na jikinta yana jin yadda zuciyarsa kekara matsewa da rashin son Nasreen shi kansa bai san abinda yasa baya sonta ba sam-sam zuciyarsa taki koyan sonta kau da kai ya yi ya fara takawa saman kafafuwansa zuciyarsa na kara buɗewa.

"Farouq".

Ta fadi da wani irin sauti da hakan ya sanya shi tsayawa da tafiyar da yake yi ba tare da ya dubeta ba ya gyaɗa mata kai.

"Ya kamata izuwa wannan lokaci rayuwar nan tamu ta zaman doya da manja a canzata don Allah".

Sosai yaji kalamanta na masa kuwwa akai da cikin zuciya amma komai bai canza masa ba idanuwansa ya buɗe sosai ya juyo ya dube ta wani murmushi ya saki wanda ya zame masa kamar al'ada a gareshi.

"Nasreen please leave me alone I done have time akan zantukan nan naki da ba sa karewa".

"Farouq yaɓkamat ka bani lokacin ka don kai miji na ne ina da dama da hakki domin yin magana da kai!".

Ta faɗi tana takowa zuwa gabansa ta sauke jajayen idanuwanta cikin nasa wani irin emotion ne take jin zuciyarta na kawo mata ga wani irin abubuwa da take hangowa daga idanuwan Farouq wanda suke kara rikita mata lissafi amma duk da hakan sai da ta jajirce ta kokarta ta cigaba da kallonsa kafun ta kau da kai da wani murmushi mai ciwo wanda yake kokarin narkar mata da zuciya.

"Baka sona Farouq".

Ta faɗi zuciyarta na sake matsewa.

Girgiza kai ya shiga yi yana shafar haɓarsa bai san mai zai ce da Nasreem ba ya rasa gane me ke damun sa zuciyarsa taƙi bashi gurbi ko ya ya ne ya so Nasreem.

"Da gaske?".

Ta faɗi tana jin wani irin juwa na kwasarta runtse idanu tayi a hankali ta shiga ja da baya tana komawa kusa da gadon ta zauna.

"Kaddarata a son ka ta sauka fata Allah ya bani ikon cinyewa....".

Wani tari ne ya sarƙe ta kafun ta numfasa ta dago idanuwanta da suka kaɗa.

"Zan cigaba da zama da kai a haka amma karka ga laifi na don na nace akan son ka".

Zuciyarsa zata iya bugawa in har ya cigaba da zama yana sauraron kalamanta ba ya son abin da zai canza masa lissafi.

"Sai na dawo".

Abin da ya kokarta faɗi kenan yana taka kafafuwansa da yake jin rashin ƙwari a jikinsu zuciyarsa ce kawai ke kalato jarumta.

***

Dauke hawayen dake zubo mata ta cigaba da yi gabadaya duniyar take ji tayi mata zafi alkawarin da tayi na daina kuka akan Farouq ba zai taba yuwuwa ga rayuwarta ba komai babu dadi a rayuwa bata ga amfanin auren Farouq ba bata ga wata daraja da kwanciyar hankali dake cikin rayuwar aurensa ba in da ta san haka kaddara zata yi mata da tun farko bata bar zuciyarta ta fara son shi ba...ko da yake so ba shi da wannan batun ba ruwansa da cancanta ko dacewa...

A firgice ta dawo hayyacinta tana mai gyara zaman rigar barcin dake jikinta idanuwanta ta sauke saitin da taji an taɓa ta.

"Nasreem!".

Ta faɗi tana girgiza kai Nasreem da ta zuba mata idanu cikin mamaki ta shiga jan hanci tana mai murmushin yaƙe.

"Hayat!".

Ta faɗi can kasan makoshi da sauti kafun ta cigaba da cewa.

"Wallahi ban san kin shigo ba...".

Daga mata hannu tayi kafun ta zare jakar dake kafaɗarta ta ajje kan table din dake gabansu.

"Ta ya ya za ki san na shigo kina cikin wannan yanayin anya kuwa Nasreem rayuwa zata yuwu a haka anya kuwa...".

Ta karashe tana mai girgiza kai yanayinta na nuna tsananin damuwa game da halin da Nasreem din take ciki.

"Hayat! Anya ba wani kuskure dana tafka kafin aurena da yake bibiyata?".

Murmushi mai ciwo Hayat tayi kafun ta nisa.

"Matsalar ka nuna wa ɗa namiji so ziryar kenan. Nasreem ba ko wani namiji bane yake maida alherin so, kamar yadda aka yi masa ba, sannan ba ko wani namiji bane ake nuna wa so ya yi halacci a duk faɗin duniyar nan. Kalilan ne a cikin mazaje za ki samu masu biyan bashin so ga matayen, da suka nuna musu maitar son su a fili".

Gyaɗa kai ta shiga yi kafun ta nisa hawaye na sake zubo mata.

"Amma Hayat! Farouq bai taba cewa baya so na ba, sannan bai taba nuna min ba...".

"Wannan ba zance bane Nasreem.

Duk fa mai son ka dole ya nuna maka son nan, ko bai furta maka ba to akwai hanyoyi da yawa da zai nuna maka eh yana matukar son ka".

Shiru tayi zuciyarta na kai komo game da zantukan Hayat! kafun ta numfasa. Kokarin cewa wani abu take amma ta rasa abin da za tace komai ya kulle mata tunaninta ya tsaya cak! ba ta san ya zata yi ba, ba ta san wacce hanya zata bi ba, don Farouq ya so ta ba iya kulawa da tattali tana nuna masa amma ko sau daya bai taba ce mata, ta burgeshi ta fanni kaza ba.

Runtse idanu tayi tana jin wani ciwo mai girma na sake samun masauki a gurbin zuciyarta jikinta sosai yake ansawa da lamarin.

"Ɗa Namiji da kike gani Nasreem gwanda ace shi yake son ki, ba wai ke 'ya mace ke son sa ba, don hakan ba karamin ganganci bane da wauta a wajan 'ya mace.Abu daya na sani a wajan namiji in har kina neman tattalinsa to ya kasance son da yake miki ya rinjaye naki, in kuwa ba hakan ce ta kasance ba to duk son da za ki nuna masa dashi zai dinga amfani, ta fannoni da dama domin cimma wani buri nashi, musamman mu mata da muka kasance masu rauni a zuciya wannnan na taka muhimmiyar rawa wajan jefamu halin da na sani".

Zuciyar Nasreem sake tsinkewa tayi, da jin batutuwan Hayat! Tabbas ta gasgasta, domin kuwa taga hakan zahir a gareta...amma kuma ai ba laifi take masa ba balle ace yake hukunta ta da son da ta bashi wanda ya zarce kaso mafi tsoka akan wanda take zato kila tana dashi a zuciyarsa.

"Ban san yaushe zuciyata ta fara son shi ba, ban san har yaushe zuciyata ta bashi gurbin so ba...".

Murmushi Nasreem tayi, kafun ta numfasa.

"Shi so da kike ganinsa ba a masa wannan tuhumar domin ba shi da amsar bayarwa. Abu daya ne shi so matsalar sa bai san cancanta ko dacewa ba sam!. Al'amuransa in har ya tashi kamar tsuntsu yake ko wani waje zai iya sauka ba ruwansa don haka ki daina tuhumar zuciyarki Akan So".

"Ya zan yi Hayat?! Ina son Farouq zuciyata bata da wani buri da kudiri illa rayuwa dashi har karshen numfashi".

Ta karashe kamar zata fashe da kuka, sosai fuskarta ta canza lokaci guda. Idanuwanta sun kaɗa sun yi jajir sai faman numfashi take ja kamar wacce take kokawa dashi.

"ƊA NAMIJI da kike gani tamkar zuma yake samun sa sai da wuta da wutan ma sai an jure an cije".

Cikin rashin fahimta Nasreem ke dubanta tana faman gyaɗa kai.

Ita ma kai ta shiga gyaɗa mata kafun ta dafa mata kafaɗa.

"Dole ki miƙe tsaye ki jajirce, domin YAƘI A SOYAYYA ba abin sauki bane, dole ki samo makaman yaƙi domin samun gurbin so a zuciyar Farouq".

Gyaɗa kai kawai take domin gabadaya kanta ya kulle zuciyarta bugawa kawai take yi kamar zata faso kirji tayo waje so take yi ta hasko wani abu a zantukan Hayat! Amma kamar wacce aka kullewa fahimta komai ya ɗoɗe mata runtse idanu tayi wasu kwalla masu zafi suka zubo mata ta sanya hannu ta shafe su..

"Ɗa Namiji kenan tabarmar ƙashi".

Hayat! Ta faɗi cikin yanayi na tausayin Nasreem don ita shaida ce ba tun yau ba zata iya cewa tun kafin auren ma ta san halin da Nasreem take ciki amma bata taba tunkararta da hakan ba tayi tunanin in tayi tsami zata nemi wanda zata zanta dashi duk da tsakanin lamarin mata da miji akwai sirri mai girma.

Miƙewa Nasreem tayi lokaci guda fuskarta ta sauya daga damuwa zuwa wani murmushi wanda dai daka kalle shi zaka fahimci ba wani jindadi a cikinsa ta dubi Hayat!.

"Nagode Hayat! Na san abin da zan yi in har nacika mace to zuciyar Farouq sai ta zamo tawa sai yadda nayi da ita".

Post a Comment

0 Comments