https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍
*WASA DA SO* 🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍
_{ Ganganci }_
*TRUE LIFE LOVE STORY*. _(Labarin Soyayyar Gaske)_
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻*
__________________________
*we are here to educate,motivate, and entertain our readers.*
__________________________
*Story And Edited By:*
*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_.
*Writing by:*
*Aysherth Mohammed Sani*
_(Preety Xayyeesherth)_.
*Facebook Aisha Mohammed Sani*.
*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*.
_Duk kan godiya ta tabbata ga ubangiji madaukaki sarki. Gaskiya ina matukar farin ciki da fara sabon novel dina fatana Allah yasa ya ilmantar da al'uma tare da nishdantarwa, ina rokon Allah ya yafemin kurakuren da zan yi wayanda bansani ba. Alkhairan da ke ciki kuma ya isa ga al'umma su amfana tare da alfahari damu_.
*KAMAR YADDA KUKA GANI TUN FARKO WANNAN LABARIN BA KIRKIRARRE BA NE YAFARU DA GASKE NE SAI YAN WASU ABUBUWAN DA AKA GYARA DOMIN TAFIYARDA SHI A TSARI*.
_Sis faty fatymarh dauda wannan shafin naki ne ke kadai kiyi yadda kikeso dashi much luv dear mie😘_
*PAGE* 1
------------------------------------------------------------------------------------------
Wani dan Matashi ne yashigo tare da dan murmushinsa .
Yana zuwa ya dire kusa da yar uwarsa tare da ce wa, "Haba Sweery na kidan bani ruwa mana,ba ki ga agajiye na dawo ba ne?"
Budurwar tayi murmushi tare da gyara zama tukun ta ce, "Wai yaushe zaka bar kirana da sunan budurwayen ka ne? niko zan yi aure ma ance ma zan auri dan karya irinka ne?" takai karshen maganar tana kallonsa sama da kasa.
Shiko saurayin ko ajikinsa sai ma kara matsawa gareta da yayi ya na, "Yarinya kimin ladabi in rabaki da wannan kwamar VIVON taki in sai miki koda iphone 10 ce."
Maganar tasa ta mutukar bata dariya hakan yasa ta tashi tare da fadin, "Kan ka kasheni da karyar nan taka gwanda naje nadibo ma abincin na huta."
Wata dariya yayi tare da fadin, "Yauwa masoyiyata yi sauri kinsan sahib din naki ya kwaso yunwa awajen boll, jeki dawo ma nabaki labari yarinya."
Ta tafi tana, "Toh naji ina zuwa dai."
Tana zuwa bata jima ba ta ce, "Toh MESSI ko Ince Adamu gashi."
Tuni ya Bata rai , "kinga Wallahi zamuyi fada inkika kara ce min Adamu sai kace wani Kada?"
Hamida tasa dariya ta ce, "Yooo Inba Adamu ba me zance?,Messi dai ba sunanka bane bare kace."
Adam ya ce, "Eh dai naji din Amman ai haka ake kirana ko?, kinga ma ni bazan ci abincin nan ba wallahi,da kicemin Adamu ai gwanda kinmin kyakkyawan mari." yana fadin hakan ne yayin da yake tafiya.
Ita ko Hamida Ba abinda take banda dariya tana, "Yooo kai ka sani Adamu bara ma kaga nadauke abinci na nayi gaba."
Fita kawai yayi yana un'uni ko waigowa bai ba.
Hajiya ce ta shigo tana, "Toh anfara halin ko?"
Hamida tayi murmushi tana, "Umm Mama Ai Adam din ne sai ya kashe mutum azaune."
Mama tayi murmushi tace, "kwaji dashi dai tare na gankU."
Adam kuwa na fita yayi wajen Abokinsa mubarak .
Mubarak na ganinsa yafara, "Haba Alhaji na ya naganka haka ."
Adam ya tinsire da dariya sannan yace, "Wallahi Hamida ta rainani wai ni ta ke cewa Adamu?"
Yakara wata dariyar sannan yace, "Allah yarinyar nan ko ta rainani,umm ba ma wannan maganar ba ya zancen bikin nan ne kasan fa nariga nakai dinki dan zamuyi wuta agun wallahi,banaso yaran nan su rai namu."
Mubarak ya shekye da dariya yana, "Yoo ai nasan indai kana waje ba raini nidai damuwata musami fararen da zamuyi manni."
Adam ya dafa mubarak sannan yace, "Kai ko na Abulle akwai ka da son karanta ina zamuyi manni da wasu farare ai wallahi dolas zan samo mana."
Mubarak yayi wani tsalle yana, "Shiyasa nake sonka Alhaji na."
Adam ya ce, "Bari kawai,bara naje gida tukun dan inaso muje da hamida ko ta rage rainani."
Mubarak ya ce, "Toh sai naganka,kana Wuta Fa mutumina."
Adam banda kwanbo ba abinda yake yana tafiya kaman wani sarki dan ya huce dan sarki ma shi aganinsa.
*INDAI KUNASO NAGA RUWAN COMMENTS ZAKUGA RUWAN TYPING*.
URS PREETY XAYYEESHERTH.😘
0 Comments