(Hausa Novel) Kasarmu Ayau By Abubakar Saleh Al~Quyraemey, Part 1





https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*_🇳🇬KASARMU AYAU🇳🇬_*


*🆕 2020*

                     
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​


______________________________________
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร
______________________________________



*Writing by:*
_Abubakar Saleh Al~Quyraemey✍_
___________________________



~Happy New Year Allah ya sadamu da alkairin dake cikin wannan shekara da muka shiga, Amin.~



 *_Bismillahir rahamanir rahim_*

_Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin halittu, wanda bai Haifa ba kuma ba a haife shi ba, wanda yake da mulki cikakke kuma tabbatacce. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) dangatan Allah, wanda dan shi Allah ya haliccemu. Tareda iyalan sa da sahabbansa da duk wanda yabi tafarkin gaskiya._


```SADAUKARWA```


   _Wannan littafi sadaukarwane ga mahaifina *Dr Saleh Aliyu Kurami (Saleh Mai Allura)* ya Rabbi kakai Rahma, Ni'ima, gafara a kabarinsa, ya ALLAH ka ni'imta ruhinsa zuwa aljannarka, da dukkan sauran musulmai, mu da ya bari ALLAH ka rayamu cikin ni'imominka da rahmarka._


```GARGADI```

Wannan littafin kagagge ne, nayi shine badon cin zarafin kowa ba, sai don fadakarwa musamman ga 'Yan siyasar kasata ta gado {Nigeria}. Ban kuma yarda ajuyashi ta kowacce irin hanya ba, batare da izini naba. Fatana Allah Ubangiji yasa sakon da nakeson isarwa ya isa ga wadanda nayi domin su.


```Part 1```


★.★.★.★.★.★.★.★.★.★.★.★.★.★



“Haba Alhaji! Dan Allah yaushe rabonka da kazauna kaci abinci? tun jiya kamar yanzu fa, kanason ulcer ya..” Daga mata hand yayi alamun tayi shiru.

Sannan ya fara magana  “Kinga jeki kikawo abincin” sai alokacin ya cire babbar rigar dake jikinshi ya nufi dinning table, bai jimaba ta shigo d'auke da kayan abincin ta diresu a gabansa, sannan ta zauna gefen domin a ganin da tayi masa indai ba zama tayi ba to bata da  tabbacin zai ci abincin.

Bud'ewa yayi ya fara cin Fruit, sannan yabi da drinks. Hajiya ta kalleshi tace “Alhaji wai lafiya kuwa? tsakanin jiya zuwa yau naga duk baka cikin kwanciyar hankali, a sanina da Kai bamu saba 6oyewa junanmu sirri ba, ko office ne sukayima wani abun? Ta jefa mashi tambayar da alamun itama ta fara shiga tashin hankali, kasancewarsu shekarun su goma sha biyar kenan da aure amman dukkansu ba wanda ya taba boye wa dan uwansa wani sirri face yau da Alhajin yake so ya maida hannun agogo baya.

Numfashi ya furzar yace “No karki damu Hajiya it's myn not urs”.

Mamaki ya sake rufeta tace “It's myn not urs” duk da a zuvi tayi maganar amman saida maganar tata ta fito fili, kara kallonshi cike da dunbim damu da tashi hankali sannan tace “Yanzu har akwai abinda zaka 6oyemun Alhaji, karka manta fa tunda nake banta6a boyema komaiba ammah abin mamaki kai kanason fara 6oyemun ko meye amfanin hakan? A tunanina ni da kai duk d'aya ne, idan ka fadaman may be zan iya baka shawara idan kuma banda shawarar zan iya tayaka addu'a.”

Kara jan numfashin yayi a karo na biyu sannan ya ture flates din dake gabanshi ya kalli Hajiya yace “Kinsan da cewa za6e na tahowa nanda shekara 1 da watanni 2, yanzu ne kowane d'an takara ke kokarin fara tallata kanshi, saidai ni a jam'iyyarmu sun tsaidani takarar Senator, dukda cewa Governor na nema amman hakan ya faskara dole takaran Senator d'in aka barmin, amman a hakan ma akwai wad'anda ke kalubalanta ta kan cewa ban tsinana wa jam'iya komai ba, kuma sun nuna basaso na, idan har muka 'kara zama meeting babu tabbacin na samu certificate na tsayawa a matsayin Senator din sabida akwai Alhaji Lawwali da Alhaji Ibrahim wad'anda kowa ke ganin sunfini farin jinin mutane da kuma can-canta, bansan me yasa hakan ba? kuma ni yanzu idan har ban tsaya takararnan ba lallai komai zai iya faruwa, Hakan yasanya narasa me ke mani dadi” ya karashe maganar cike da tashin hankali domin kana kallon fuskarsa zaka tabbatar da hakan.

Hajiya ta d'ago kai tace “Alhaji suwaye kake tunanin ko suke nuna basasonka a jam'iyyar taku?”

Alhajin yace “kinga babbansu Alhaji Musa da Alhaji Isa wad'anda jigo ne a jam'iyyar, domin indai wadannan mutane biyu suka nuna sunayinka to shikenan an gama magana. Lallai idan har muka kara zaunawa meeting wanda zamuyi a next week babu makawa sai sun chanja ni dukda cewa Alhaji Lawwali ma  baidamu da mulkinba....”

Hajiya ta katse shi da cewa  “Alhaji ai wannan kana 6ata lokacine, indai har dan wannanne inaso kabar komai a hannuna, gobe insha Allah zanje wani kauye a cikin Ungoggo LGA akwai wani kauye Namanta sunanshi 'kawata ce ta fad'aman akwai wani Boka aikinshi tamkar yankan wukane, domin kuwa yakamata mu kauda duk wani ma'kiyinmu a doron 'kasa indai zai kawo mana cikas ko wayeshi”.

Da sauri Alhajin ya d'ago ya dubeta yace “Da gaske?”

“'Kwarai kuwa!” hamdalah yayi sannan yace “Lallai naji dad'in hakan, domin kuwa nafara nunamusu kud'i ammah hakan baisanya sun janye adawar ba, har suke i'kirarin Alhaji Ibrahim zasu tsayar don yafini chanchanta. Tunda haka sukeso lallai zan nunamusu nine Alhaji Bishir Dodo, saina kaudasu d'aya bayan d'aya a doron 'kasa, kishirya goben kije nawa kike tunanin zasu isheki?” ya 'karashe maganar yana mai fara'a da kara jin san matar tashi yana shigarshi.

“Eh toh dukda banta6a zuwa ba but I think 4 million is ok, ammah what ever dai I will call u.”

Buga tebur yayi ya furzar da iska sannan ya miqe yana dariya ya fad'a bathroom.


★.★.★.★.★.★.★.★.★.★.★.★.★.★


Tunda safe kimanin karfe 7:30am Jamal yashigo da sallama, maigadi ne yafara gaisheshi sannan yawuce cikin gida tun a parlour yapara ganin 'kannensa duk suka gaisheshi sannan yawuce chan cikin d'aki. Da shigarsa sai ya tarar da Umman kan sallaya tana lazimi. Sit yanema yazauna yana jiranta, bata wani jimaba ta juyo kanshi dur'kusawa yayi ya gaisheta sannan ya tambayi ya 'kannen nasa suka kwana, duk ta amsa mashi da lafiya kalau. Ya kuma tambayi lafiyan Abbansu shima da sau'ki ta fad'a, ya kuma ce Allah 'kara lafiya. “Ameen” ta fad'a. Sannan ya miqe yace Ok“ Umma zan shiga na gaisheda Abba” ta amsa mashi  da “To”

A Gaskiya dukda cewa Umma ba Jamal ne kawai d'anta ba amma tafi sonshi bisa sauran, dukda cewa shineh babbah amma hakan bai sanya yanada girman kai ba ganin yanda mahaifinshi keda kud'i tamkar Hussain 80k hakan baisanyashi d'aukar head ko jiji dakai ba, hasalima Jamal yana yawan shiga talakawa duk majority abokansa 'yayan talakawane. Sannan wani abin sha'awa a rayuwar shine dukkan gidan shi kad'ai ne ya tsaya yayi ilimi both Islamic da bokon domin kuwa yana haddar sittin a kansa, wannan dalili ne yasa kowa a gidan yake sonshi. Gashi irin mutanen nanne da ake Kira da ‘Social man’ masu dad'in, zama duk yanda kake tunanin Jamal yawuce don ko baka ta6a ganinshi ba indai zaku zauna tsawon minti 2 wlh ko waye  kai sai Jamal yashiga ranka, tun a school da yawa a cikin 'yan mata more especially course mate nashi suna yawan yimashi request about Love amma saidai yayi murmushi baidamu da mata ba kawai abinda ke gabanshi yake. Yanzu haka shine babbah a gidan su, kuma yanada kimanin shekaru 29, ya gama degree dinshi na farko afannin Sociology, yanzu haka yana preparing ci gaba da karatu a kasar malaysia.

A hankali ya bud'e dakin, da sallama ya shiga ya tarar Abba yana gyangyad'i, murmushi yayi sannan ya tasheshi sannu2 Abba ya bud'e eyes nashi yaga Jamal shima murmushin yayi.

“Abbah ina kwana” yafad'a ya kuma amsamashi tareda tambayarshi ya jikin nanma ya gaisheshi sannan yafito ya koma palour. Su Beauty; Baby da King ne sukataso da gudu suka rungumeshi,  murmushi yayi don yasan halin 'yan 'kannen nashi ya jasu zuwa sit chair duk suka harhad'u suna fira, zuwa karfe 9 Umma ta shigo dukkansu ta korasu akan suje suyi break a dinning shi kuwa anan aka kawomashi nashi.

Alhaji Ibrahim wato mahaifin Jamal Mutumne mai 'kima a idanun mutane saboda tun kafin yanzu Alhaji Ibrahim ya riqe mu'kamai a gwamnati masu matukar yawa, wad'anda duk jam'iyyar babu wanda ya ri'kesu, amman ba'a ta6a samunshi da laifin koda sama da fad'in naira ba, hakan yasanya yake da farin jini wajen talakawa. A kullum safe; rana da kuma dare baka rasa mutane a kofar gidanshi. Tunda safe kafin yafita talakawa masu bu'katu kamar na haihuwa dadai sauransu sukanzo ya basu taimako. A kullum da safe akanyi Koko d kosai musamman saboda mutane, haka za'a raba da kuma na almajirai. Da rana kuwa shinkafa haka dare ma da kalar abincin da za'ayi shiyasa kullum yake 'kara masoya.

Allah ya albarkance da yaya biyar Uku maza yayin da biyu suke mata, na farkonsu shine; Jamal mai shekara 29; sai Kamal mai shekara 25; Shafa'atu suna kiranta dasuna (Beauty) mai shekara 18; Hafsat suna kiranta dasuna (Baby) mai shekara 15; sannan Auta dangwali shalele mai suna Isa shi kuma suna ceshi (King) shi yanada shekara 10. kuma dukkansu Hajiya Binta. Hajiya Binta tana  masifar ji da 'Ya'yanta amman hakan bai hanata basu tarbiyya ba, domin duk inda sukaga wanda ya girmesu to ko basu sanshiba sai sun gaishehi, hakan ne yasa suka fita daban a layin wannan kenan.

Yauma kamar kullum, bayan Alhaji Ibrahim yadawo daga masallaci sallar asubahi gida yashiga yad'an karya sannan yafito, mutane duk sukayo kanshi haka yagama dasu sannan yashiga mota yanufi office. Yana isa duk yaranshi neh suka run'ka zuwa suna kawo gaisuwa, saboda baida jin kai ko kad'an haka yake sakarmasu fuska sometimes yakanzo cikinsu su runqa labarai kamar abokai, shiyasa da yawa suke ganin yadace yafito takarar Senator ganin yanda yakeda al'ummah. Shikam ba wannan baneh gabanshi. (Kunji dattijon arzi'ki.)


★.★.★.★.★.★.★.★.★.★.★.★.★.★


*BARI MU WAIWAYI ALHAJI BASHIR DODO*

Tunda safe matarshi wato Hajiya Nafisa ta shirya ko break batayiba tafito tajawo motarta horn 1 tayi maigadi ya bud'e, shi kanshi yayi mamakin pitar hajia har yana tunanin da yake anya ba matsala suka samu da Alhaji ba. Cikin sanyin safiyar ta doshi hanyar zuwa Rijiyar zaki domin achan 'kawarta Hajiya Maryam take, wadda tasan kauyen da Bokan yake da yake gari bai idasa wayewa ba, tsala gudu takeyi tamkar zata tashi sama hankalinta kwance tamkar tayi ba'ko ya mutu. Cikin mintuna kalilan ta isa anguwar Rijiyar Zaki. Layinsu tafara lalube saboda ta jima batazo anguwarba ammah takasa ganoshi saboda gine-ginen da aka 'karayi, dole saidai a waya ta kirata shganoshi suka had'u sukahau mota hanyar Daura suka nufawa direct.......



°°°Zanci Gaba°°°

Post a Comment

0 Comments