]Hausa Novel] Bamisriya Ta Page 4 By Abubakar Saleh Alquyraemey


πŸ’ž πŸ’ž πŸ’ž πŸ’ž πŸ’ž πŸ’ž πŸ’ž πŸ’ž
        *BAMISIRIYA TA*
         πŸ’ž πŸ’ž πŸ’ž πŸ’ž πŸ’ž πŸ’ž πŸ’ž

πŸ‘¨πŸ»‍πŸ’»πŸ‘©πŸ»‍πŸ’»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
​​WΙ› Ι‘Κ€Ι› Ι¦Ι›Κ€Ι› tΡ³ Ι›Ι—ucΙ‘tΙ›, MΡ³tiΡ΅Ι‘tΙ› Ι‘Ι³Ι— Ι›Ι³tΙ›Κ€tΙ‘iΙ³ Ρ³uΚ€ Κ€Ι›Ι‘Ι—Ι›Κ€ΰΈ£​.
___________________________________

©2019

*πŸ†™DATE*


*Page 4*


*STORY BY*

      _DEEN_πŸ’˜


*TYPING BY*

      _Abubakar Saleh Al-Quyraemey_πŸ’˜

 ```Facebook.Abubakar Saleh AlQuyraemey```


~Sadaukarwa Ga Zamani Writer's Association Allah Ya Kara Hade Kanmu Ameen Ya Hayyu Ya Qayyumu.~






*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*



.............. Bazan manta ba ina fadamaku cewa: Naji wani daci ya lullube mani zuciyata, sai na saduda mai yuwuwa irin wannan abun ne dazaka hadu da mutum sau daya tak a rayuwarka, wanda zakaji kana tambayar kanka mai yasa tun a farkon rayuwarka baku hadu ba?.

Amman kuma kafin ka farka,  sai ka nemeshi karasa, baka sake ganinsa ba har abada.

*INNALILLAHI WA`INNA ILAIHI RAJI`UN..........* Haka na dunga furtawa a zuciyata. Haka kuwa akayi na samu sassauci a cikin zuciyata.

Kamar yanda kaddara ta tanadar mana haka muka kwana a garin tanta. Abokaina suna ta bacci,  amman nikuma ina zaune ko runtsawa banyi ba, tunanina yana wani wajen ina ta tunanin wannan yarinya cikin tashin hankali, cikin fargaba da firgici ko wane hali suke ciki a can garin kairo Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ‘Ω„Ω…haka dai nayi tayi in mirgina nan in mirgina can har aka kira sallar asuba.

Cikin Sauri na mike na tashi sauran abokaina sunata yi Mani sambatu amman ban damu ba haka dai na samu da kyar suka mike, na ce masu "Ya kamata muyi Sauri muyi Sallah in yaso sai mukasa kunne muji abunda yake faruwa a can Cairo din".

Saboda haka, muka Shiga masallaci muka yi Sallah sannan muka ji cewar a can Cairo din abubuwa sun dan lafa. Sabo da haka muka yi Sauri muka karasa tasha saboda munsan cewa kowane lokaci zamu iya cigaba da tafiya, muna isa bamuyi wata-wata ba muka nemi jirgin karfe *6:00am* muka shiga.

Su abokaina suna Allah-Allah muyi Sauri mu isa sbd kada wani sabon rikicin ya barke, ni kuma ina Allah-Allah sbd na tabbatar da cewar hayaniyar da akayi bata ta'ba mani *bamisiriyata ba* .

Haka jirgi ya cigaba da tafiya abokanaina sukayi shiru basu musayar da suka saba, ni kuma daman kamar yanda muka je bana ce wa komai haka muka komo bana ce wa komai, sanadiyyar gurbin tunanina ya cike fal da tambayoyi haka zalika da fatan cewa wani abu bai ritsa da *bamisiriyata ba*.

Bayan tafiya ta dan lokaci wanda bazan iya kintatawa in ce ga tsayinsa ba, kasancewar baxanyi adalci wajen fada ba domin ni a nawa tunanin karni 100 muka bata, kasancewar zuciyata tayi matukar kaguwa ta ganta a tashar jirgin kasa ta Ramsis daga karshe sai gamu a tashar.

To tun jirgi bai gama tsayawa ba na mike tsaye ina dakon yana tsayawa niko zan fice, kana kamin ya tsaya ina ta leleke. In-leka kaina tacan in-kalli can ina kokarin hango dai-dai inda yarinyar nan take zama ba'ama kai ta in ganta ba, babban fatana a wannan lokaci shine naga na'urar dafa shayin ta, wannan ya ishe ni farin ciki fal mara a dadi.

Sai dai kuma kash! banga na'urar ba haka zalika naduba×2 banganta ba a zuciyata na ce "To ko wajen ya juye minne amman bari jirgin ya tsaya mugani", su kuma abokaina sai kallona suke yi suna tunanin meye ne hakan nake yi?zato suke ko tsoro nake ji ko akwai miyagu a tashar.

Hixbullah ya kalleni cike da kulawa yace "Kaga malam ka kwantar da hankalinka tasha fa lpa lau take, ka zauna kawai ka nutsu ba wata damuwa ka gane."

A zuciya ta na ce ina niko nake cikin damuwa, dakasan damuwar da nake ciki da baka fada mani haka ba, ban kulashi ba na cigaba da dube×2 ko zan ganta tawani wajen.

Ana cikin haka sai jirgi ya nemi waje ya tsaya ina ganin haka banyi wata×2 naje na bangaji kofar jirgin na fice, abokaina suka biyoni a guje tunaninsu wani Abu nagani nakeson guduwa.

Na karasa gurin da *bamisiriya* take na tsaya ina kallon wajen sai na ganta a zaune, ta juyo ta kalleni tayi mani murmushi sai tayi mani alamun nazo na zauna, na fara kokarin zama ina tunanin mai zan fada mata, kawai sai naga jikinta ya fara marmashewa kamar gari, sannan duka launun kan kayanta shima haka yana bin iska har tagama bin iskar gaba daya, ashe gizau take Mani, ba ita ba na'urar shayinta gurin yai fayau bakowa ba komai.

Na shiga tashin hankali haka na durkusa a wajen ina ta haki, ina ta tunani ina kuka abokaina suka karaso wajen suna tambayata lpa meke damu na? ban basu amsa ba dan a wannan lokaci ko magana bazan iya yi ba, bana iya komai banda tunani da bakin ciki sannan dajin kunci na rashin wannan yarinya a dai-dai wannan lokaci.

Suka kamani suka cicci'beni izuwa gida, washe garin wannan rana nafito da niyar zuwa tashar  jirgin kasa ta Ramsis da niyar in duba wannan yarinyar, amman sam-sam masu ababan hawa basu zuwa ta wajen, kwata×2 ba wanda yake jirga×2 kasancewar ana cikin wannan rikici, domin wannan rikici lafawa kawai yake amman yakan dawo aci gaba. Na rasa abun hawa sai na yanke cewar a kasa zanje koma meye ne zai sameni sai dai ya sameni, na fito ina tafiya, har na fara tafiya sojoji suka tare ni sukace na koma gida gari ba lpa, na matsa masu kan cewar ni akwai inda zanje yana da matukar mahimmanci a gareni, suka cemani lallai na koma naki yarda haka suka sani a motar su ta karfi da yaji suka mai dani anguwarmu. Kashe garima na sake fitowa aiko na sake haduwa da su suma sukayi mani yanda na fΓ rko suka yi mani, haka mukayi tayi da su sai da muka shafe kwanaki shida muna haka dasu karshe na hadu wasu nayi mashu gardama suka rufeni da duka.....



_Muje zuwa ......._



*Dan jin yadda zatΓ  kasanΓ§e.................*




*✒Abubakar Saleh Al~Quyraemey*


 ```{Young Writer}```

Post a Comment

0 Comments