*** *BINTA* ***
_'Yar Mallam Mamman_
____________________
Na:
```Mubarak A Kamba```
____________________
*Zamani Writers Association*
```We Are Here To, Educate, Motivate And Entertain Our Readers```
*Sadaukarwa:*
```Na Sadaukarda Wannan Shafin Ga 'Yan Kungiyata Ta Amana Zamani writers ```
*Wacece Binta?*
*Binta* ~_wata yarinya ce wacce ta tashi cikin shagwaba da yanga. Babanta wani dattijo ne mai kirki mai daraja a idon mutane, aikinsa shine dinka rariya wacce mata ke yin aiki da ita cikin gida domin sarrafa wani abu mai ruwa. Mahaifiyarta kuma wata mata ce yar gidan mai kudi saidai bata da biyayya da mutunci a idon kowa musamman ma a idon mijinta (wato mahaifin Binta Mallam Mamman). Tashin Binta ba abin da ta iya sai walakanta mutane da tsangwama ga kuma uban cin mutunci domin ta koyi hakan ne a wurin mahaifiyarta._~
____________________
*Page 1 to 5*
____________________
_Tafiya na ke takona d'aya bayan d'aya kamar wata hawainiya, na hadu sosai ba kadan ba. Kai idan ka ganni dole ne ka maganta ko a cikin ran ka ne domin suturar da nasa tana nuna tsiraicina sosai, wata doguwar riga ce da kuma karamin dogon wando wanda ya kame jikina ne na sanya. Gayu fa kallo na su ke kamar su kamo ni domin na dauki hankalinsu. Wasu kuma tuntube suke yi wurin kallona kamar su fadi. Ina cikin tafiya ne kawai naga kowa na gudu, ta ko ina gudu su ke kamar tashin alkiyama, kafin na ankara tuni naji an yi cumu-cumu da ni har bana iya ko motsi domin masu karfi ne suka rikani suka jefa ni a mota fuskata a daure. Tafiya mu ke amma bansan a ina za mu je ba mun yi tafiya mai nisan gaske tsawon sa'o'i biyu mu na tafiya bansan a ina muke ba amma nasan cewa mun fita daga cikin garin da na ke. "Wayyo Allahna ni *Binta* yau na shiga uku, yau naga mugun abu ya zan yi da kaina wa'yannan mutane a ina za su kai ni". Abinda nake ta fadi kenan a cikin raina. Sai can daga baya naji motarsu cas ta tsaya._
_Aka kai ni cikin wani daki mai masifar duhun tsiya. Sannan aka kuncemin fuskata. aka kunna wata fitila mai haske sosai nan nagansu su biyar tsaye a gabana. Ganin bindigogi a hannuwansu ne ya sa na gigice na kasa yin ihu ko motsin kirki bana iya yi. Ogansu ne ya zo gabana da wata karamar bindiga a hannunsa ya na shan sigari, kai ko namiji yagansu sai ya rikice balle kuma ni macce. "Yan mata sannunki, gaskiya fa kin hadu". Ya fada yana busa hayakin sigari duk ya gigitani. Wasu maganganu kawai ya ke amma ni hankalina ya gushe ba na iya maida martanin abin da yake fada. Ganin haka ne ya sa duk su ka fita waje aka rufe dakin ana jiran hankalina ya dawo a yi magana da ni. An dauki tsawon lokoci mai yawa sannan hankalina ya soma dawowa gare ni. Su na waje ni kuma ina daga cikin dakin, can sai naji ogansu yace aje a siyo mu su kayan maye. D'aya daga cikin su ya ce " a gaskiya fa oga mun yi dace da irin yarinyar da muke so domin wannan da ganinta kasan cewa za ta iya aikin boko haram, kai ba boko haram ba ko islamiyya haram wannan ai za ta iya"._
_Dukansu su ka bushe da dariya. Sai wannan lokacin ne na gane manufarsu akaina. So su ke su samu yarinya wacce za ta iya tayasu aikinsu na tsiya. Hankalina ya kara tashi ashe yan boko haram ne shiyasa da su ka zo duk jama'a kowa dugu ya ke. Ina cikin wannan nazarin ne kawai naji shigowar wani a cikin dakin da na ke, zuciyata sai wani bugawa ta ke da karfi. Kafin kace me ji na yi an rungumo ni da karfi aka dafemin baki, sannan aka kunna fitilar nan mai hasken tsiya. D'aya daga cikinsu wanda tausayina ya kama shi ne yazo kunceni kafin ya kunce ni saida ya yimin wasu jawabai. " *Binta* zan kunce ki yanzu amma ki yi saurin barin dajin nan kuma ki bi a hankali yanzu abokan aikina duk sun yi maye ko wanne bacci ya kwasheshi. Saboda haka saidai ki bi a hankali domin kuwa shima wannan dajin abin tsoro ne". Ya fada cikin kashe murya domin bayaso a ji. Kamar na tambayeshi waye shi, amma tsoro ya hana ni. fita waje na yi cike da mamakin yadda akai ya san sunana._
*Tafdijam Akwai Sauran Rikici fa domin Binta batasanma a ina ta ke ba*
0 Comments