[Hausa Novel] Lauratu Page 3 By Mrs H3RB33B

♥♥♥♥♥♥
      ♥♥♥♥
         *LAURATU*
     
       _(Love story)_


Story and written by
~Mrs H3RB33B~

*wattpad - Meerahman*


*©2019*


DEDICATED TO MY MENTOR
~BINTA UMAR ABBALE~



~Sadau'karwa ga~

*HASSAN 90k*
*HUSSAIN 80k*


🅿3

Junaid Abdullahi shine cikakken sunan mahaifinsu Maryam kuma sunan mahaifiyarsu, Junaid  asalinsu fulanin yola ne gaba da baya, Su uku ne a wajen mahaifinsu Junaid shine first born, sai Abubakar sai autarsu mai suna Aisha.


Suntaso cikin tarbiya da ingantaccen ilimi na addini dana zamani, Junaid ya kammala degree d'insa yayin da ya karanta Business Administration, Alokacin ne kuma 'kaninsa Abubakar yake level 3 A ABU zariya inda yake karantar Computer science a lokacin kuma Aisha tana SS 2.

Lokacin da Junaid ya tafi service d'insa a maiduguri ana ne ya had'u da Asma'u suka 'kulla soyayya, Asma'u dai shuwa ce mahaifinta Yana da rufin asiri. Asma'u su uku ne a wajen iyayensu dukansu mata ne Akawai Amina itace babba sai Khadija sai Asma'u itace autarsu suma akwai ilimi da tarbiya sossa, Yayun Asma'u duk sunyi aure inda suka auri manyan masu kud'i a Abuja.


Bayan wani d'an lokaci ne  iyaye suka shiga magana aka tsaida ranar auren Asma'u da Junaid, Ba'a wani d'auki lokaci mai tsayi ba akayi aure ta tare a yola yayinda Junaid yasamu aiki a wani company, bayan bikin ba'a dad'e ba ya jona master's d'insa.


Yanxu shekara d'aya da auren su amma Allah baibasu haihuwa ba, Alokacin Abubakar ya kammala degree d'insa yacewa mahaifinsa,"Aure zaiyi kafin ya fara service." Mahaifinasa bai musa ba ya tambayeshi wacce yarinyace nan ya sanar masa 'yar skull d'insu ce kuma a zaria take sunanta Zainab.

Bayan bincike da mahafinsa yasa aka masa akan Zainab nan bincike ya nuna sunada 'karancin ilimin addini, amma Abubakar yace,'Yaji ya gani ita yakeso."


Ba'a wani d'auki lokaci ba akayi bikin Zainab da Abubakar, suna zaune gida d'aya da yayanshi Junaid, Kamar had'in baki Asma'u da zainab suka samu ciki lokaci guda, sun shiga watan haihuwarsu kenan Allah yayiwa Baban su Junaid rasuwa.

Rasuwarda ta jijjiga kowa dayake unguwar da talakawa saboda shi mutum ne mai kyauta abin hannunsa bai tsolemasa ido ba. Bayan rasuwarsa da kwana 7 Zainab ta haifi santalelen d'anta namiji kyakkyawa dashi nan aka saka masa suna Abdullahi wato sunan mahaifinsu.
         After 2 weeks Asma'u ma ta haifo d'anta mai kama da ita sak, Ranar suna aka saka masa Asad.


After 3 years Zainab ta sake haihuwar namiji wadda yaci sunan Muhammad Naseer suna kiransa da naseer After 3 years tasake haihuwa inda ta haifi mace mai Kama da mahaifinta ranar suna aka sakamata Laurat.

Asma'u kuwa tun akan Asad Allah bai k'ara bata haihuwa ba tun suna damuwa itada mijinta harsuka daina suka barwa Allah komai suka rungumi tilon d'ansu.

Laurat uwarta ta sangarta ta sossai kasancewar ita kad'aice mace, Asma'u suna kiranta da Mamy Zainab kuma suna kiranta da Momy Junaid daddy suke cemasa Abubakar kuma Abba.

 Bayan an raba musu gado ne suka gina babban company ba abinda babu a wannan company d'in.


Allah yayiwa companyn Albarka yanxu state d'ad'd'aya ne babu branch d'insu a wajen, To yanxu kud'i ya zauna shiyasa suka dan'kara manyan gidaje a Abuja suka d'auki mahaifiyarsu suka koma can da zama anan Aisha tayi aure ta haifi yaranta biyu mace da namiji imran da Fatima.

After 25 years Asad da Abdullahi sun kammala degree d'insu a United kingdom (UK) Asad course d'in mahaifinsa ya karanta wato Business Administration yayinda Abdullahi kuma ya karanta ya karanta medicine.

 Lokacin da su Asad suka dawo Nigeria ne Asad yaga Laurat nan ya haukace akan  domin Laurat son kowane 'kin wadda ya rasa. Laurat farace sol tanada rown face, hancinta kamar biro, ga eyes d'inta medium ne shi ba babba ba kuma ba 'karami ba bakinta yanada d'an fad'i kad'an, tanada dogon gashi amma bashida cika.  Itama dai ta wajenta hakane tanason handsome injita da fad'a,  wannan kenan.


*Cigaban Labarin*

Laurat ce cikin friends d'inta suna hira kana ganinsu kasan yaran masu hannu da shuni ne ga skin d'insu yadda yake wani she'ki da laushi kasan naira tayi aiki.


Princess (haka skull mate d'inta suke kiranta dashi) gaskiya kinyi sa'ar mijin aure inama ace nice da handsome d'in ki da naji dad'i wallahi.


 Feenah kema dai kyafad'a.  And lastly Abinda zan fad'a shine wallahi princess ki nutsu kibar bin maza, Duk da ba wani ilimin addini gareniba amma naji anacewa,"Duk macen da take da aure tayi using  wani namiji wuta zatakishiga."


Sannu malama Fauzy feenah da Laurat suka fad'a atare suka kwashe da dariyar sha'kiyanci, Feenah Harda ri'ke ciki tsabar dariya.


Fauzy ta tashi ranta a b'ace tace musu....


Gaskiya comment yayi kad'an 😉



*Like*
*Vote*
*Share*
*Comment*
~Mrs H3RB33B~😘

Post a Comment

0 Comments