[Hausa Novel] Yaro Da Kudi Page 4 By Binta Umar

*🐾YARO DA KUDI*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—



*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)



*πŸ…Ώ4*


Babu Abinda Abdul latif yace masa Dan inda sabo yariga yasaba da iskancin Nasir!

Ya kalli su Anwar da Abbas yace wallahi Ku lura da dunyar nan naga kwata kwata Ba kwa wannan lissafin duniya fa Ba matabbata ce kuma duk Abinda ka shuka shi zaka girba Ku dinga Sara kuna duba bakin gatari duk Abinda kayiwa Dan wani to tabbata sai an wa naka!!

Nunashi da hannu sukayi suna dariya Abbas yace Malam Alaramma wa'azi kake mana ne kome kai fa kafiye  Takawa nuna ma tsoron Allah zakayi kome?
Sunayi suna masa dariya tamkar sun samu mahaukaci sabon kamu!!

Girgiza kai kawai Abdul latif yayi yace ai duk kunyi Nisa bazaku ji kiran da nake yi muku!

Kai ya sayyadi A ramma ya isa haka Dan Allah cewar Anwar yaciga ba dacewa babu ruwanka damu ka wai ido ne naka Dan iska kawai munan dashi zai biyo sawunmu Amma yanzu yazo yanawa mutane wa'azi waishi mai tsoron Allah Mtssssssss!!

Mi kewa Abdul yayi domin fita yace Allah ya ki yayeni kuma da kukeyi Allah ya shirya minku babu India zan biku yawon iskanci Allah ya kiyaye hanya yayi ficewarsa daga falon!

Yana Fita Suka kyalkyale masa da dariya gami da tafawa Anwar yace dubeshi Dan Allah wai shi ustaz zaka biyo sawumu ne ai!

A haka Nasir yafito ya samesu suna tai wa Abdul iskanci!


Cikin wani irin taku Nasir din yakaro so inda suke  yana wani irin Abu irin nasu na birni !!
Da sauri Anwar ya dunqule hannusa suka dinga wani irin Abu da hannuwan nasu shi da Nass din suna Dariya hade da dukan kafadun su!!!

"Abbas yace  Kai Nass yaushe kahada wannan Wanka kwata kwata bansanka dasu bah!
Kaga yadda kayi kyau kuwa "Hande some "Lailai yau zaka hada go sulow mutumina!!


Yana Wani irin Abu irin nasu na nigogi gami da gyara wani tabkeken Agogo dake daure a hannusa mai bala'in tsada yace waddanan kayan ai sun Dade a ajiye ka wai banyi Amfani dasu bane!

"Kayi kyau sosai dole in kar6i kayannan nima in maqala "kasan Mutumi na ne 50 Cent na Lura shigarshi ka hada!!

Dariya Nasir yayi yace kwarai kuwa ni har yanzu duk mawaqr A  America bani da gwani kamarshi kasan ya'iya raff"hippo)

Abbas yace a ganinka Ba!


Wasu Riga da wando ne jikin Nasir wandon iya gwuwa ne wani burgujeje yasha a do ajikinshi birjik da Alji wuna gaba da baya rigar kuwa me kamar vest ce mai kauri da yankakken hannu itama burgujejiya da photon wani tsohon mawaqin kasar America 50cent a jikinta tafkeke sai wasu iyayen sarkoki a wuyanshi sai sheqi suke da Wata shigiyar hana sallah mai bala'in tsada da yasa a kansa!

Humm Fadin tsadar takalimin da'ike sanye a qafarsa bata lokaci ne totally in zaka lissafa kudin wannan  kwalliyar Nasir sun tassama dubbannin daruruwa domin shi kanshi takalmin ya kai dubu Dari da hamsin!!


"Cikin Nishadi suka Fita daga part din nsa ya sanya key ya kulle!!

Wata Shegiyar mota suka Nufa samanta a bude kalarta jace sosai  tayi masifar haduwa dagani sabuwar zuwace domin bata baza gari Ba gashi dagani sai an sanya kudade masu nauyi za'a mallaketaa!!

Zama sukayi ciki kana Nasir yatashi motar hade da sakin waqar Mawaqiyar nan (Rihanna) tuni Harabar gurin ya karade da dukan sifiqa ji kake duff Duff!


Da Sauri Malm Yau mai gadi yatashi domin bude get ganin yadda Nasir ya fafaro motar kamar zai tashi sama!

Tana Zaune kan bai n ci kamar ko da yaushe takan fito ta zauna kusa da mahaifinta ta Dan tayashi hira!

Tunda ga Fitowarsu Nasir har shigarsu mota bata dauke idonta daga Kansu Ba tanajin wani irin mugun bakinciki ganin yadda suka yi shiga kamar Ba "ya"yan musulmai Ba
Ran tane yabaci ganin yadda Mahaifinta ya mike yana rawar jiki domin bude musu kofaa"

Daga yau ta dauki Alkawarin mutukar tananan bata tafi  skull ba zata dingaa bude musu get din!!!


*MUJE ZUWA*πŸ’‹

Post a Comment

0 Comments