*BAMISIRIYA TA*
💞 💞 💞 💞 💞 💞 💞
👨🏻💻👩🏻💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
___________________________________
©2019
*🆙DATE*
*STORY BY*
*_DEEN_💘*
*TYPING BY*
*_Abubakar Saleh Al-Quyraemey_💘*
```Facebook.@Abubakar Saleh AlQuyraemey```
_Sadaukarwa Ga Zamani Writer's Association Allah Ya Kara Hade Kanmu Ameen Ya Hayyu Ya Qayyumu._
______________________________
_*My Fans* You Make Me Feel I'm The Most Precious. Your Reward's Coming From The Most Gracious. I Believe With You I Can Go Places And My Novel Are Gonna Last For Ages. Ni Kam Ba Zan Iya Biyan Ku ba, Sai Dai Addu'ar Allah Ya Cika Mana Burikan Mu._
______________________________
👉 *Page 5*
..........Bazan manta ba ina faɗa maku cewa: haka muka yi ta yi da su, sai da muka shafe kwanaki shida muna haka, daga k'arshe na had'u da wasu nayi mashu gardama suka rufeni da duka bayan nayi masu gardama.
Na kasance bayan wannan duka da nasha a hannun jami'ai, na kwanta jinya sbd ciwukan da suka ji mani, abokaina ba yanda basu yi ba akan na faɗa masu abunda ke faruwa Amman Sam naki faɗa masu sun kasa gane kaina. Ai ko Hizbullah ya fara magana ranshi a matuk'ar bace kamar haka "Gaskiya ban san wace irin abota muke ba, shin wannan wace irin abotace ace kana cikin matsala amman bamusan abunda ke damunka ba sai wasu abubuwa dasuke faruwa dakai yanzu gashinn kaje an dake ka kace jami'ai ne suka dake ka, to ba dole su dake ka ba, kullum kana fita suna dawo da kai an sa doka ka ki kabi, kuma mun rasa gane ina kake son zuwa haka." nan shima kamal ya dauka ya ce "kai kake damun kankama ni ai tuntuni na yakiceshi, cos naga abun nashi bana kare bane nikaga dan miko mani kazar can ma" yayi maganar yana nuna ma hixbullah take away din dake gefe na. Shi kuwa hixbullah ya kada baki yace "kai a na magana mai mahimmanci kana wani maganar kaza", aiko abun nema yasamu Kamal ya ce "kai kazar ce bata da mahimmanci to wlh tana da mahimmanci......"
Suka kaure da hayaniya kamar yanda suka sa ba, ni dai ina kwance ina jinya. Amman ba jikina yake jinya ba ni zuciyata ce take jinya sbd *bamisiriya ta* ko wane hali take ciki?. Tambaya da bani da amsar ta.
Ina cikin wannan jinya ne bayan an dauki *2 weeks* ana wannan hayaniya sai shugaba Husseni Mubarak da daddare ya sanar da cewa zai sauka daga kan mukaminsa, nan take wannan rikici ya tsaya cak tamkar daukewar ruwan sama.
A wannan lokaci duk da yake raunukan jiki na basu warke ba, sai naji na dawo garau. Washe gari da safe nai tsalle na sakko daga kan gadona ban zarce ko ina ba sai tashar jirgin kasa ta ramsis, na isa wannan Tasha ne da misalin karfe *8:00am* da sauri da sassarfa na k'arasa wajen da wannan baiwar Allah take sana'ar saida shayinta, amman saidai banyi dace ba domin kuwa babu ita babu tukunyar shayinta.
Haka na nemi guri na zauna dai-dai inda na zauna *2weeks* da suka wuce, ina tunowa da fuskarta da yanda ta rike littafi tana karatu, da irin shigarta ta kamala, da yanda take murmushi da kuma yanda fuskarta ta canza lokacin da muka shiga jirgi muka fara tafiya hawaye suna kwaranya a fuskarta, ina cikin wannan tunani ne sautin kiran Sallah ya farkaddani har karfe *12:00pm* tayi mani a nan, ba wannan yarinya ba asalinta nayi azahar nayi la'asar har sai da nayi magriba a nan da saran wani uzirine ya hanata zuwa, da saran zanga kawai ta bayyana da injin shayinta.
Da naga dare yayi gashi abokaina sun kirani tafi sau 100 amman ban daga ba sbd kada na fad'a masu a inda nake, kuma nasan damuwa da nine yasa suke ta mani wannan kiran abunda basu sani ba shine damur da nake ciki ta dama damuwarsu ta shanye.
Haka dai na hakuri natashi na koma gida, washe gari ma na sake dawowa nai zaman dirshan ina jiran wannan yarinyar amman batazo ba, haka nayi tayi harna shafe tsawon *7days* kullum sai na je wannan wajen, amman Allah bai kaddara zamu sake haɗuwa da wannan yarinyar ba.
A kwana na bakwanne ina zaune gaf da lokacin sallar la'asar sai naji an dafani, nai sauri na juyo mezan gani? sai naga wani mulmulelen dan sanda yana tsaye a bayana, nan take naji wani bakin ciki ya rufeni na fara ce wa "wlh na zata itace ta zo gareni ta ganeni ta kusantoni" amman ina wani mulmulelen dan sanda ne.
Nan take yayi mani tambaya akan "me nakeyi anan?"
Nace masa "ba komai."
Yace "bakomai."
Yace masa 'eh."
Yace "wato tsawon *7days* zuwa nake nayi ba komai na koma gida kenan."
Nai shiru, kasancewar k'asar Masar akwai tsaro ashe duk lokacin danake zuwa wannan tashar jami'an tsaro na hankalce dani, ya kara zareni da ido yace bazaka fada mani ba?.
Nace masa wlh babu komai can daga bisani sai naga wasu yan sanda su biyu sun fito sun tsaya daga bayana, nan take yayi masu alama da hannuna akan su kamani abu kamar wasa, suka d'agani suka sa mani handcuffs aka shigar dani mota sai gamu a office.
Jim kadan sai ga wani babban dan sanda ya shigo akayi dace ya iya turanci ya dinga gaidani cikin mutunci da mutuntawa:
"Hello young man how are u"
Yace "dan matashi yakk"
Nace "ina nan lpa."
Sai kuma yace "where are you from."
"Wai daga ina nake"
Shine sai nace masa "I'm a Nigerian ma'ana ni dan Nigeria ne."
Nan kuma sai yayi mani wata tambaya wadda tabani mamaki kuma ta bani dariya yace: did you know Rashid yakini?"
Wai tambayata ya yi "Wai nasan dan kwallo Rashid Yakini" daman aikin su kenn duk sanda suka ga dan Nigeria sai su fara tambayarsa Wai yasan Rashid Yakini, abun yakan ban haushi, sannan kuma yakan ban mamaki kasancewar mu 'yan Nigeria bama godewa baiwar da Allah yayi mana, sai dai wasu su jinjina mana.
Sai na ba wannan dan sanda amsa da "eh" duk da ni ba ma'abocin kallon kwallon k'afa ne, haka dai yai ta jama da labarai har dai ya samu nasake dashi daga karshe na bashi labarin duk abunda ya faru, da dalilin dayasa nayi sati ina zuwa wannan tashar ta Ramsis.
Haka yayi shiru ya kuramin ido na dan lokaci bai ce komai ba can sai ya dago kai yace dani:
"I believe you but u have to promise me something."
"Wai ya yarda da maganata amman Wai yana so nayi masa alkawarin wani abu."
Sai nace dashi "mene ne?"
Sai yace "when ever u meet that girl, I will like to see her and I will help u."
Wai duk lokacin dana samu nasarar haduwa da wannan yarinyar Wai yanaso yaganta kuma zai taimakeni..............
_Alhamdulillah ............._
```Muje zuwa .......
✒Abubakar Saleh Al~Quyraemey
{Young Writèr}```
0 Comments