[Hausa Novel] Bamisriya Page 6 By Abubakar Saleh Al~Quyraemey

BAMISRIYA TA*
         💞 💞 💞 💞 💞 💞 💞

👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
___________________________________

©2019


*🆙DATE*



*STORY BY*

      *_DEEN_💘*


*TYPING BY*

      *_Abubakar Saleh Al-Quyraemey_💘*

 ```Facebook.@Abubakar Saleh AlQuyraemey```


_Sadaukarwa Ga Zamani Writer's Association Allah Ya Kara Hade Kanmu Ameen Ya Hayyu Ya Qayyumu._



*Special Gift To Hussain 80k Allah Ya Biyaka*


______________________________
_You have to find something thatz you love enough to be able to take risks, jump over the hurdles and break though the brick walls that are always going to be placed in front of you. If you don't have that kind of feeling for what it is you are doing, you'll stop at the first giant hurdle._
_______________________________


👉 *Page 6*



 ........Bazan manta ba ina fadamaku cewa: "When ever u meet this girl I will like to see her and I will help u".

Wai duk lokacin da na samu damar haɗuwa da wannan yarinyar lallai yana son ya ganta kuma zai taimakeni, Alhamdulillah haka na furta a zuciyata.

Gaskiya ban taɓa ganin ɗan sanda kuma  bamisre mai kirki kamar wannan bawan Allah ba, dan gaskiya yayi matukar fahimta ta daga karshe ya bani number wayarsa yace "Duk lokacin da nake neman taimako to kada nayi wata×2 kawai Na kirasa shikuma zai tsaya mani, kuma zai taimaka mani.

Sbd haka nan take ya miko mani hannu muka gaisa sannan ya sallameni, na tashi na fita naje ficewa yan sandan kan kanta suka bini da kallo niko ko kallan su banyi ba na fice abu na sakamakon zafinsu da nake ji cikin raina.

Na dauki hanyar gida ina ta tafiya ina ta sake×2 a cikin raina ban masan ta yaya zan ɓullo wa wannan lamari ba. Domin zuciyata tayi mani nauyi bana cikin jin dadi ko annushuwa gaba ɗaya raina a bace yake kuma ba nace ga wata mafita ba.

A daren wannan rana na tashi nai Sallah kana na roki Allah rokona ya tafi kamar haka _''Ya Allah ina rokonka ka fini sanin halin da nake ciki, ina neman a gazawa da tagazawa daga gareka, domin kai kadai ne zaka iya ya ye min wannan matsalar, ya Allah ka nuna mani mafita ta yarda zan samu in fita daga wannan k'angi, koda wannan mafita ta kasance sauwa'ke min zazzafa da kakkaifan yana yin da nake ciki na son wannan yarinya, ya Allah na ro'ke ka albarkacin sunayenka kyawawa da suffofinka tsarkaka ka amsa mani addua ta ameen_''.

Shikenan na kwanta da niyar bacci ya daukeni amman ina sai tunanin wannan yarinaya nake yi, na juya nan na juya can, naji abun bai gamsheni ba, na sake tashi na daura niyya sannan na karanta hasbinallahu wa ni'imalwakiI fiye da sau 1000 domin nasan falalar ta. Sannan na karanta salatin annabi {S.A.W}, shima na karantashi fiye da yadda zan iya tunawa kasancewa nasan falalar yiwa annanbi salati {S.A.W} da kuma tasirin sa wajen biyan bu'kata, sannan na haɗa da wasu addu'o'i waɗanda na sani, ai ko ina kammalawa wani bacci mai nauyin gaske yayi awon gaba dani.

Ban san inda nake ba sbd bacci, banyi aune ba sai ji nayi ana kiran as-salatu, kasancewa dukkanin baccin da na keyi da zaran ankira as-salatu sai kawai naga na farka, ina farkawa sai naji na tashi cikin wani irin farin ciki da annushuwa wanda ni kina bansan dalilinsa ba.

Bayan nayi sallar asuba na dawo na shigo falona na zauna na dauko Alqur'ani ina karantawa kamar yanda na saba kullum safiya, sai ji nayi wayata ta fara ringing na dauko wayar na duba fuskarta sai naga daya daga cikin abokaina ne waɗanda mukayi tafiya dasu mai suna Hixbullah yake kirana, na amsa kiran sannan na kara a kunnena nace:
"Hello"
"Yace "Ya mutumin kana lpa"
"Lapia lau nake" na faɗa masa a takaice
Ya cigaba da magana kamar haka "Wai in tambayeka mana, batare da ya jira amsata ba ya cigaba da cewa "Wannan yarinyar nan mai saida shayin nan da ka ke boye mana ai munsani ka sake jin labarin ta kuwa?"
Cikin 'karfin hali, nai murmushi nace "A'a ban sake jin labarinta ba". Na cigaba da cewa "Ban gane kun gane ina son taba?".
Abokin nawa yace dani "Kai dai kawai ka saurareni kaji abinda zance maka kazo tashar yanzu yanzun nan ya kashe wayar". Kawai sai ya kashe wayar.

Ni kuma na cigaba gaba da hello! hello!..... amman ina ya riga ya kashe wayar.

Nan take naji mamaki ya cika mani zuciyata sannan nayi firgigit na ajiye Alk'ur'anin dake hannuna sannan na nufi kofar fita ai ko ina fitowa daga gidan na tsaida wani mai taxi nace ya kaini tashar jirgin kasa ta Ramsis.

Na shiga motar gashi gudu ake amman ni ji nake kamar ba tafiyar ake ba kamar na sauka na karasa da kafa da gudu, amman dai haka nayi hakuri inata faman adduar kawai na bude Idona na ganni a tashar jirgin kasa ta Ramsis.

Muna isa kuwa banyi wata-wata ba kuwa nayi hanzari na fito daga cikin motar da yar sassarfata, na isa wajen tun kafin na k'araso wajen na hango naurar dafa shayin wannan baiwar Allah. Wayyo daɗi!  Sai na ji wani irin daɗi ya lulluɓeni wanda tunda na ke bantaɓa jin irinsa ba zuciyata ta fara raira wata irin wak'a.

Nan take nayi firgigi na nutsu na dan gyagyara jikina kana na cigaba da tafiya ina mai doson wajen ta a duk lokacin da nayi taku daya sai naji annushuwa ta na daɗuwa, damuwata na raguwa bugun zuciyata na 'karuwa ga makeken murmushi a fuskata har dai na isa wajen.

Ina isa kuwa murnata ta fara komawa ciki kasancewar naga wani saurayi ne a wannan gurin ba yarinyar ba. Duk da haka sai zuciyata ta ce dani mai yiwuwa wannan ko yayanta ne, yake ta yata aiki ita kuma taje wani guri zata dawo.

Na riski wannan saurayi nayi masa sallama ya amsa ya tambayeni,
"kana bukatar shayi ne?"
"Wane iri ka ke so?" Duk a lokaci guda ya jero mani wad'anmam tagwajen tambayoyin. Na d'anyi Jim sannan nace masa "kafacino na ke so".

Sai ko ya tashi cikin zafin nama ya nufin in da na'urar dafa shayn take, ya matso mani irin wanda nake so ya dawo ya miko mani.

Na zauna ina sha amman hankalina yana kan ina zanga *Bamisriyata* wannan yarinya ina ta shiga ne zatazo ne?, yaushe zatazo? duk wannan tambayoyin ina juyasu ne a cikin zuciyata.

Da nayi kurɓa ɗaya, biyu, uku kamar wanda ake yi wa irga, na daga kai na tambayeshi ina yar uwarsa kuwa? cikin mamaki kuwa ya dago kai ya kalleni yace "wace 'yar uwar tawa?" sai nace "kanwarka mana wanda take aiki  a nan wurin itama tana saida shayi."

Sai yayi dariya yace "To ai shi baya da wata kanwa da zata zo ta tayashi aiki. Sai yace mani ai shi jiya-jiyan nan ya fara saida shayi a wurin." Na kalleshi naga ko wasa yake, amman a fuskarsa sai naga ba alamar wasa da gaske yake, kawai sai naji shayin ya fita daga raina, sai na 'kara tambayarsa "Shin bai san waɗanda suke yin amfani da wurin ba a da," sai ya nuna mani ai shi bai san abin da na ke nufi ba .

To na san halin Misrawa sai na d'auko kudisa na basa na bar masa ragowar shayin sa na tashi na rasa ya zanyi kawai sai na juya bayana ina zuyawa sai na ga...............






```Muje zuwa .......




✒Abubakar Saleh Al~Quyraemey

      ```{Young Writèr}

Post a Comment

0 Comments