BAMISRIYA TA
💞 💞 💞 💞 💞 💞 💞
```Based On True Life Story```
```A Heart Touch Love Story```
👨🏻💻👩🏻💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
___________________________________
©2019
*🆙DATE*
*STORY BY*
*_DEEN_💘*
*TYPING BY*
*_Abubakar Saleh Al-Quyraemey_*
_@Facebook Abubakar Saleh AlQuyraemey_
_@What'sapp 08138873799_
_Sadaukarwa Ga Zamani Writer's Association Allah Ya 'kara Haɗe Kanmu Ameen Ya Hayyu Ya Qayyumu._
*Devoted To Mubarak A. Kamba {Mubson}*
_________________________________
_Winners are ordinary people with extraordinary heart._
_________________________________
👉 *Page 7*
..................Bazan manta ba ina faɗa maku cewa: sai na 'kara tambayarsa shin bai san waɗanda suka yin amfani da wurin ba a da, sai ya nuna Mani aishi sam bai san abunda nake nufi ba.
To, nasan halin misrawa sai na ɗauko kudinsa na bashi, na barmasa sauran shayinsa na tashi raina a ɓace na rasa ya zanyi, kawai sai na juya baya na ina juyawa sai na hangi dan sandan nan ya yi zuru yana kallona ko kiftawa baya yi, sai naga ya girgiza kai. Alamun yana jin-jina wa lamarina ya na kuna tausaya mani, haka zalika na ga mamaki 'karara a fuskarsa yayin da ya juya ya bar wajen.
A dai-dai wannan lokacin ne sai na fara tunanin anya lapiyata kuwa, kodai na fara taɓuwane? na kasa gane wannan al'amari kona mis'kala zarratun, amman duk da haka wani sashin na zuciyata yana sanar dani cewa "Wani abu tabbas ya afku kuma tabbas wannan yarinya a kwaita, haka zalika ina sa ran wata rana dole zamu sake haduwa sbd ni nasan iya adduar da nayi.
sannan ni nasan ubangiji maji ro'ko ne, nasan lokaci ne kawai baiyi ba na tabbatar karɓar addu'a ta. Daya daga cikin abunda ya 'kara mani ya'kinin san wannan yarinyar baiwuce Karin dadin son da nake ji yana daɗuwa a zuciyata ba.
A wannan rana sammako na yi ban samu na karya ba, a dalilin haka ne yasa na shiga gidan wani abinci wanda muka saba zuwa ni da abokaina a kusa da wannan tashar.
Su masu waje nma sun riga da sun gane mu, a duk lokacin da muka je cin abinci gidan ba abunda muke cewa a kawo mana sai shinkafa da gasashshiyar kaza, shi saurayi mai kawo abuncin da gani na sai yayi murmushi ya gyada kan shi alamar ya gane mai zai kawo mani.
Saboda haka, nan take yayi magana ga wad'anda suke had'a abincin ni kuma naci gaba da jira kafin a kawo min.
Kamar dai yadda kowa zaiyi tunani, banyi komai ba a wurin face tsunduma cikin zurfin tunani na wannan yarinyar Kyan fuskarta da lokacin da muka haɗu, dakuma abubuwan da suka waka na tsaka ni na da ita. Hakan ne ya sani nishaɗi a cikin zuciyata da kuma annushuwa naji daɗi sai dai kuma kash! na sameta na kuma rasata ya zanyi.
Kwakwalwata sai dai-daito mani dai-dai wajen da take murmushi.Take naji zuciyata ita kuma sai dariya take tana hmmhmmhmm.
Ina cikin wannan tunanin ne kawai sai naga giftawar wata daidai kofar gidan cin abincin, nan take na tashi a firgice aiko na bita da sauri, a dai-dai wannan lokacin ne shikuma mai kawo abinci yazo da abinci zai ɗora mani akan faranti, sai ganina ya yi cikin sauri ina fita daga wajen, yana ta 'kwala mani kira yana ga abincin an kawo amman ina ko kulashi banyi ba, yayin dana fice na bi bayan wannan baiwar Allah da naga ta wuce, tana tafiya nikuma ina binta a-baya-a-baya kasancewar bansan kowacece ba.
Jim kadan, sai ta lura da cewar bintafa nake domin duk kwanar da ta shiga sai taga nima na shiga, idan ta tsaya sai taga nima na tsaya daga nesa, idan taci gaba da tafiya sai taga nima na cigaba da tafiya. Nan take wannan matar ta tsargu sbd haka tafiyarta ta yan mata takoma sauri, daga sauri ta koma sassarfa, daga sassarfa ta kuma gudu, to a nan ne nima na fara binta a guje tana gudu nima ina gudu a bayan ta. Mun kasance mun d'auki lokaci a haka daga bisani ta tsallaka titi aiko banko duba titin ba nima na bita saura kad'an mota tayi awon gaba dani.
Nan take muka dauki hankalin jama'a, abun yana basu mamaki sbd mai bakar fata namiji yana bin mai farar fata *Bamisriya* a birnin Al'kahira. Wannan Abu lallai ko ba'a faɗaba an san lallai a kwai matsala, kawai banyi aune ba sai jin wani abu mai nauyi ya sauka a kaina. Nan take, abun ya kayar dani na dago ina duban wannan yariya, itama ta tsaya ta juyo ta kalleni sai kawai naga a shema ba ita bace. Wannan abun shikadai zan iya tunawa dagann kuma bansan inda kaina yake ba.
A saiɓance cikin dagiya, da kokawa da kyar na samu na bud'e idona biyu yayin dana ganni akan gadon asibiti a kwance, ga kuma wasu yan sanda guda biyu suna kallona da alamu tsarona suke saboda ko wanne a cikinsu yana sanye ne cikin kakin shi (Uniform).
Farkawata keda wuya naga daya daga cikin su ya dauko waya yayi kira, yayin da d'ayan kuma ya bini da idanu, daga cikin su biyun babu wanda yace dani uffan, hakazalika nima bance dashu komai ba.
Bayan kamar *15mints* sai ga wannan dan sanda da na taɓa zuwa office din sa ya shigo dakin, kuma shi sunan wannan dan sanda Magdi Jamal, wanda alamu sun nuna ko a tawa fahimtar gaba ɗaya wannan yanki a karkashinsa yake, a yayin shigowarsa dakin nabi fuskarsa da kallo inda na lura cewa wannan karan fuskarsa babu wasa, aiko sai na nutsu sbd ban san mai zai biyo baya ba.
Ai ko nan take ya fara yi mani faɗa, ya fara daga murya yana cewa "Nayi haukane bani da hankaline kodaima ni mahaukacine?" a zuciyata nace "Ni kaina ina da wannan tantamar," yake tambayata "Ina so nakashe kaina ne?"
Niko nayi shiru yayin da na siddar da kaina 'kasa ina sauraronsa, sai na dago kai na nace yayi hkr ni kaina nasan nayi kuskure.
Yana ta huci yayin daya samu kujera ya zauna ya harde hannuwa inda ya boye ko wane yan yatsu yayinda manta yan yatsunsa yaketa gaba da baya dani alamun yana tunanin cewa ya zaiyi dani nan take naji na shiga firgici ko wace matsalar na jefa kaina.
_Soyayya haka zata yimin haka zata maida ni?_
_Daman haka soyayyar take wayyo Allah na!?_
Sai naji kai na ya fara sarawa na lumshe idanuna........
_Muje zuwa ......._
*✒Abubakar Saleh Al~Quyraemey*
```{Young Writèr}```
0 Comments