πΊπΊπΊ
*_SANADIN HIV!_*ππ»
πΊπΊπΊ
~_A Short & Fiction Story_~
*By*
*Jamaal Datti*
Wattpad@Jhermaal0809
~_Dedicated to my sis *Ummul~Khairi*_~
*1π2*
Bismillarihmanirrahim
Wani qaton gida na hango a second gate wato unguwar Jan bulo, wajen gidan ya qawatu da adon furanni gasu sunyi kore shar² dasu and flowers din so colorful. Sannan ga wasu dogayen bishiyoyi da suka kara qawata wajen gidan.
Fentin gidan white ne fes ² dashi tare da ratsin Abuja-brown, wow it look so beautiful, wae! Gate din gidan ma yakasnce Abuja-brown, hadadden gaske ne kuma design inshi ma abun kallo ne, ke daga ganinshi kinsan ba hadin gida 9ja bane sai dai abroad π€£
Tangamemen gate in a wangale yake so sai nasamu damar leken harabar gidan. Kai! πππ
Mata ne na gani sai karafniya suke tare da kai komo a cikin gidan hade da shewarsu da hayaniyarsu, alamu dai sun nuna biki bidiri ne za'ai ko kuma a ke kanyi a cikin wannan katafaren gidan wani mashahurin dan siyasa a cikin birnin kano ( _ta dabo tumbin giwa ko damai kaje an fika_) π
Ae ganin abinda ke wakana yasani juyo akalar sayyadata domin kwaso maku rahoto da dumi-dumin sa { _~kar dai a ce ko yar agwagwar nan ban hawa~_ ehe}
Laluba Aljifu nai nazaro layar zanata na matsata na bace bat sai gani a harabar gidan domin gidan buki ba'a rasa labariπ€«
" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" shine kawai abin da harshena ya furta sakamakon tozalin da wasu irin 4 different duplexes apartment masu azababben kyau, wato 2 a right handside sai kuma 2 left hand side dina, a opposite dina wani hadadden bungalow ne wanda ya fita daban daga sauran hudun sabida tsaruwarsa, da alama na Amrya sarautar mata ce π
Ko wanne flat consist of 3 bedroom with 2 fallow while na me gidan 3x3 ne shikuma, biyun duplex in dasuke makota dana tsakiyan are connected dana tsakiyan while sauran biyun kowane na can gefe, a end of my right hand side wani hadadden swimming pool ne sai kuma a can hannun haguna parking lot ne with veranda, daga bayan duplexes din wani makeken garden ne daya qawatu da different variety of trees π² π² π² da kuma flowers π π π masu fitarda daddaden kamshi.
Kai readers in na tsaya rubuto muku cikin duplex ne sai mu gama pejin nan ban gamaba.
Kowanne shashi dankam yake da mutane Yan biki da alama gobe ne daurin auran ko yau ne nidai bansaniba.ππ»♂
Shashin danafi jiyo hayaniyar 'yan mata na tashi can na nufa domin kwaso maku rahoto da zafi zafin shi
'Yan mata ne a part din 'yan kimanin shekaru sha takwas zuwa ashirin da biyu, kowacce ta ci gayunta na gani na fada domin fasawa a gidan bikin.
Wata budurwa 'yar kimanin shekaru ashirin na gani an zagayeta sai araha akeyi tare da janta da wasa, alamu dai sun nuna itace amaryar, gefenta wata official make-up π artist ce me tsantsara mata kwalliya ta kece raini a cikin taro,.
Juyowar da tayi ae kusan suma nai domin azatona deepika padukone ce, banbamci su dai she's not up to that tallness compared to Deepika, and kuma bata kaita tsinin hancin ba, fuskar nan ta tsaru sosai da sosai, said dai ita fair dark ce in complexion wato ba'a cemata fara tas ba kuma ba'a cemata chocolate ba, kyau dai masha-Allah.
Gama make up din keda wuya wata mai alamar masu shegen surutu tace "saike amarya a gidan *Fu'ad* sarki mai mulki a zuciyarki kasancewar shi zakaran gwajin dafi da yai nasarar kame zuciyarki, ya shige chiki yai kaka gida sannan ya hana kowa kowa shiga kuma yai nasarar kasa yayana gashi gobe iwar haka muna gidan Amrya munyi rakiya" man wata mai hanci a cikinsu da saki wata shegiyar guda kamar zata fasa dodon kunnuwa _ "Ayyyiriiriiiii"_, nan 'yan matan suka kwashe da dariya hadi da tafawa a tsakaninsu.
Sao wata cikin su tace niko wlh zanso inga wannan fuad din data boyewa mana shi gashi har an kusa dauresu! sai wata tai caraf tace wlh da gaskiyarta zamanin nan ne sai kinayi kina kaffa kaffa in bahaka a miki sakiyar da babu ruwa atoh π
Silent killer rabu da ita duk tsiya dai sai mun ganshi sai dai nikab zata bashi ya faso cikin taron, gabadaya wadanda ma badasu ake firar aka kwashe da dariya
_ya kuka jishi ne?_
JamaalDatti π
0 Comments