(Hausa Novel) Juriya By Hafsat Usman Waziri, Page 1

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

~Typing...... ✍~




     *๐Ÿ’– JURIYAA! ๐Ÿ’–*



_*Written & Story*_

   *๐Ÿ’œHafsat Usuman Waziri๐Ÿ’œ*

      _๐Ÿ’Miss Hafsy๐Ÿ’–_




_________________________
ZAMANI WRITTERS ASSOCIAATION
_________________________

*We are here to educate, motivate, and entertain our readers*
______________________



            *๐Ÿ†• 2020*
_Happy New Year my Fans aduk inda kuke, Alherin Allah ya isa qq gareku_



_Bismillahir _ rahmanir rahim._


*ARASHI*

Wannan littafin ban rubutashi domin  wani ko wata ba, wanda rayuwar shi tayi kaman cece niya da labarin,asalima k'agagen labari ne wanda nakirkireshi domin ilmantarwa fadakarwa dakuma nishadantarwa.
_________________________


Y'a Allah kabani ikon kammalawa lafiya, ka nufeni da fad'an alkairi, kuma kasa a amfana dashi duniya da lahira, d'uk wani me buk'atar ganin wani b'atanci nawa kokuma wanda b'aya bukatar cigabana Allah kai ta nunamai duniya da lahira, kuskuren dazanyi allah ka yafeni Allah yasa na fadi Alkhair.



*Unforgetable one*

Anty Binta Umar Abbale
๐Ÿ’–Bintu batula ๐Ÿ’–
✍marubuciyar
*-Gimbiya balaraba*
*-Tsantsar butulci......*


*Allah yak'ara haske arayuwarki, yarabaki da sharin makiya, ya kara daga ki, yakara miki baseera da nusan kwana me albarka, ya raya miki y'ayanki cikin tafarki na garii.*




❤❤❤❤❤
_@real shaxee,  Allah yak'ara baseera ya rabaki da sharin makiya ya kawo miji na gari me albarka, da nisan kwana_ ๐Ÿ™๐Ÿป




*Zamani writters association members, i can't do without uu guys Alllah yak'ara mana hakuri da juna, ya tabatar da zumuncinmu duniya da lahiira ๐Ÿค๐Ÿฟ๐Ÿค๐Ÿฟ๐Ÿค๐Ÿฟ*




Dedicated to my beloved sister. ๐Ÿ’–
Khadeeja usman wazeer
      ( ummee)
Bride to be.... ๐Ÿ˜Ž



Page 1



 Gidan k'asa ne babba, wanda ya kunshi rukunan d'akuna da kuma bangarori da dama, wani b'angare ne d'aban wanda aka mishi ginin zamani, yasha tiles da fenti me shegen kyau.


Tana zaune a tsakar gidan nasu, tana tsintar shinkafa y'ar hausa, daga gefenta kuma dattijuwa ce zaune nesa da ita da y'ar redio dinta data sha tsuma tana sauraren labarai.

Sallama aka kwad'a a bakin kofar bangarensu "wa'alaika sallam " wata zazak'ar murya ta amsa  "wai zoya tazo...... "Kai kace batanan".  "Kai jeka kace gatanan zuwa"
Kallon ummanta tayi "Haba don Allah umma" "kar ki kuskura kimin magana, haka kikeson nasaka ku a gaba nai ta kallonku ga mazaje Allah ya kawo muku"  "Amma umma bafa asan waye ba, kuma kinsan y'aya garama ta hanani tsayawa da masu mota yanzu idan na fita tazo fa" ? A, a kinsan de Bukar me trader ne, yanzu dai kije ki dakko hijjabinki kije kinji Hadeeya?  Murmushi tayi wanda ya bayana point of beuty nata ( dimples) toh ummanah. "Yawwa y'ar kirki "

Bayan ta dakko hijjabinta, ta wuce waje, da sallama ta karasa, hadaden gaye ne a tsaye yasha shadar shi me kyau daga gani kasan d'an fulanine ziryan, murmushi yai mata, "mosoyitah ykk?
"Lafiya kalau ta amsa k'anta duk'e, nadawo kifadamin ansata domin gaskiya na gaji da ziryannan kuma haryanzu bansamu masauki ba cikin zuciyar ki yaka mata  zuwa yanzu nasan matsayina, dagowa tayi ta kalleshi "uhmm k'asan de zuciya tana son tasamu lokaci kuma tasamu nutsuwa ko, kayi hak'uri insha Allah gobe zan fada maka shawarar da na yanke......  "Wai kai bukar me ke damunka ne bana ce kar na kuma ganin wannan k'afar taka anan ba, toh ka kwantar da hankalinka rana itay'au za'a daura auren hadeeya....
Dummmm gabanta ya buga, innna lilahi wa'inna ilaihi rajiun shine abinda kawai take maimaitawa, Allah yasa mafarki take ba gaskiya bane abinda y'aya garama take fada...... Don haka d'aga yau idan ka kuma zuwa hukuma ce zata rabamu wallahi, idonshi ne yayi jajawur alamun bacin rai bece k'ala ba ya kama gabanshi saboda da yayi magana kukanshi ze iya fitowa.

Ke kuma worning na k'arshe dazan miki ko k'are ne y'akuma aikowa kizo kika fito sede wata ba ke ba wallahi.
Fuuuu ta wuce tabarta a tsaye k'amar bishiya, jiki a sanyaye ta juya ta koma gida, koda tashiga ummanta b'tanan don haka tayi saurin kawar da damuwa aranta ta kirkiro murmushin dole "kina ina ke kuma munafuka annamimya toh ki shirya ranar Asabar za'a daura auren Y'arki wallahi babu kaffara, ummah dake cikin akurkin rumfarsu ta girki ta fito da gudu domin duk a zatonta f'ada akeyi da Hadeeya.... Turus tayi ganin zubaida.
"Lafiya zubaida meke faruwa?  "Dole zaki tambaya, toh ki bude kunnuwanki da kyau *ranar Asabar * za'a daura auren zoya..
K'amar saukar ruwan zafi ummah taji zancen zubaida, murmushi ta k'akalo "toh zubaida Allah ya nuna mana y'asa alkhairi " "Amin " ta juya ta fita tana ci gaba da masifa.

"Yanzu ummah haka zamu cigaba da zama agidannan bamu   y'ancin kanmu k'amar bayi?  Toh ai ko bayi sunada y'ancinsu, tun muna y'ara har yanzu jiya ya yau abinma se k'ara gaba yake "Ya Allah kabamu ikon k'arbar gaddarar nan.
Dafata ummah tayi cikeda da tausayi "Hadeeya nasanki da imani da kuma bin umarnin iyayenki wannan ma karkiyi watsi da ita bakisan alkhairan dake cikiga ki d'auki kadararki don allah, yazata yi tasan idan h'ar bata y'arda ba kiyayarce zata k'ara karuwa, gwara ma tayi auren ta huta, kuma tayi alkawarin ko almajiri suka bata zata karba hannu bibiyu.

Riko hannun ummanta tayi tace "ummah na y'arda da zabinsu, kuma zan k'arbi kaddarata Allah yasa hakan yafi alkhairi a ruyuwarmu gaba d'aya.
Hawayen farinciki ummah tashare "hakika kin faranta min rai Haddeya Allah ya faranta miki kema, yai miki albarka.


** k'alal lah subhanahu wata'ala ** khairikum man ta'alamal qur'an wa allamuhu li gairihi *

Mafi alkhairin gareku shine "wanda yasan alkur'ani yasanar da waninsa "


...  Kai tsaye zubaida ta wuce bangarensu tafara buga k'ofa, "ganunan ina zuwa, cewar wata mata aciki ajiye garin tuwon da take tankadewa tayi ta zo ta bude k'0far bangajeta tayi ta wuce "Oh! ni Maryamu Allah ka shiryamin yarannan "

Tana shiga d'akinsu ta saki fuska g'anin y'an uwanta, A, a batuu yaushe a gari zkedai bari nima ai nashiga layinku.. Zaro ido tayi ๐Ÿ™„ Banganeba, karde kicemin shima yayi halin?  "Eh mana ni gaba ta kaini y'anzu se muji dadin cin ubansu ai hajjo ta bani labari, tafawa sukayi " ke bakisan abinda hajjo tayi musu ba kinsan wa tahad'ata dashi?  A, a ina d'an gidan me abincinnan na b'akin titi?  K'ardai kice mun m......  Base kin k'arasa ba shi, a firgice ta kalli hajjo "haba hajjo gaskiya hukuncin yayi yawa kiyi hakuri ki janye don Allah " "kallon kin rainani tayi mata wallahi zan mareki batuu, ni sa, arki ce?  Haka nakeso don haka se nayi kuma da shawarar gwago ( mamansu kenan)  "nifa kina bani mamaki k'amar baki sha nonon gwago ba?  Tab dijan!



.. ... .. ✍✍✍✍✍


More comment more typing...... ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐Ÿป

Post a Comment

0 Comments