(Hausa Novel) Naklat (Naughty Girl) By Walidation S. Mapi Part 1

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation



typing๐Ÿ“ฑ๐Ÿ’ป

๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒธ
*NAKLAT*
      (The naughty girl)

Page 1


 _*Labari/Rubutawa*_
_*Walidation s mapi*_

Dukannin yan uwa ina muku barka da sabuwar shekara.

*Dedicated my momy ladingo yar mutan niger wannan littafi tundaga farkonshi har karshenki sadaukarwa gareki ne.*

Tukwuici ga sister ta sanaz deeyah
____________________ZAMANI WRITERS ASSOCIATION________

*WASIKA ZUWA GA FANS NAWA*

_Wannan littafi nawa mesuna Naklat kagaggene kuma kir'kirarren banyishi don cin zarafin wata ko wani ba in yayi kama da taka labarin ka/ki yi hakuri labari ne wadda yake dauke da tausayawa,ilmantarwa,tareda fadakarwa kamar yadda kuka sani na kammala littafina mesuna HAKA SO YAKE? waya'anda suke tambayata document kada su damu soon zaku samu kuma ina fatan yadda kuka bani kwarin gwuiwar comment haka zaku bani anan Walidation tanayin fans nata over._

*GODIYA*
_______

_~Ina mika godiyata ga daukakin jama'ar kungiyarmu wato ZAMANI WRITERS ASSOCIATION bisa ga irin yadda suka dau hakuri dani gaskiya nagode da hakurinda kukeyi dani  kuma insha Allahu wannan littafin baza'a samu matsala daga gareni ba sunanku Aradu bazata lissafu ba.~_

Bismillahirrahmanirraheem
๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ

Yammatan ne guda biyu suna tsaye a bakin titi.

Suna sanye ne da tsukak'kkun wando baka'ke da kuma tops kanana sai kuma uwar gashin dokinda suka saka akansu.

dayar ce ta dubi dayar tace "Kawa da alama yaufa ba kasuwa"

Dayar ce ta juyo a fitsarance tace  "Haba kawata ya zakice haka sai kace bama kai karfe goma tsaye anan?"

tace "muna kaiwa mana amma yau duk nagaji kuma naga kamar ba kasuwa"

Suna cikin wannan maganarne sukaji tsayuwar mota a gefensu,nan suka gyara tsayuwarsu irin tsayuwar fine girls dinnan dayar kuma ta sauke gashin kantinda tasaka.

"Yammata sannunku"

Dayarce ta juyo cikin kissa da kashe idanu tace "yawwa sannu"

yace "mekukeyi haka har karfe tara kuna tsaye bazaku gida ba"

Dayarce ta juyo a fitsarance tace "Sana'a"

Mutuminko ya gane inda zancensu ya dosa amma kuma sai dake yace.

"Wace iriyar sana'a ce wannan cikin dare?"

Kyakkyawar cikinsu ce ta juyo a fusace tace.

"Malam da bakasan sana'armuba da bakazoba ni bana son iskanci da saka eyes akan abunda bai shafeka ba haba in zaka zaba ka zaba in kuma mu duka biyun mun maka to bismillah"

Yace "ok duka kunmin muje"

Dayarce ta juyo tana tauna cingam dinta tace "yafi maka"

Nan suka wuce suka shiga motar yajasu fuu suka tafi.

Washe gari da safe misalin karfe shida suka nema    yamayar dasu har gidajensu baiso hakan ba amma kawai sai ya kaisu.

Tana isa kofar gida ta sanya doguwar hijabinta tayi saurin shiga gida don dama tasan Babanta da ya fita sallar Asubahi baya dawowa sai karfe bakwai ko takwas don haka tashige daki tayiwa dakin key takunna tocin wayarta tafara waina kudi a hannu tana murmushi.

Dayarko tana isa gida tashige ko hijabin bata saka ba Mahaifinta na ganinta amma ko magana beyi mata ba don yanada dalili.

Mamarta ta tarar acikin gida tana girka tukunyar shayi.

tace "umma yau nayi naira nazama hajiya."

Cikin zumudi mahaifiyarta ta tashi.
tace "ke haba?"

tace "maza zokiga yau yarki tazama hajiya acikin hajiyoyi"

Mamarta tace "Ayyirirai yau kande ta zama Hajiya nawa kikayi? kawo na kidaya mana"

Bata mata gardama ba ta mika mata karba tayi tafara kidayawa Naira dubu hamsin ne cif ba ragi ba kari.

Tace "kinga yau tukunyar shayinnan nafara daura shi,bara nakira kannenki suzo suje wurin danliti mai shayi yahado mana shayi mai kauri da indomie kai harma da kaji biyu in zan samu"

Yarinyarce tace "Mama! "ya za'yi inje in nemo kudi kuma kigama kashemin? ni gaski bazai yuwu ba ai wannan zalinci,ne da iskanci,da mugunta, dakuma Hauka"

Mamarce tace "a lallai NAKLAT kin girma tsawon mu yazo daya kin mallaki duk abinda nake dashi, an dana ki, dole kifadamin haka na yarda da duk irin zaginda zakimin indai akan kudi ne naji nagani kuma yau abinda na irga sai naci"
Ta shige daki kiran Salisu yazo ta aikeshi gurin dan liti mai shayi.

********
Kamilat,kamilat,kamilat, Mamarta ce ke kiranta kawai saita mike ta banko knfan nan tajishi da key.

Jin an banko kofa yasa tayi saurin tashiwa don ta bude,
innarta tagani tsaye "ta inna kiyi hakuri wallahi bacci nakeyi"

Innar tace "haba yar' kirki shine sai kin bani hakuri bakomai wallhahi yanzumma naga idonki kamarda alamun bacci jeki kwanta"

Batayi musu ba don gaskiya Baccin takeji.wannan kenan.

________Haba kande!"yaya za'yi son kudi yarufe miki ido kibar yar'ki tana aikata abinda bai dace ba? ki tuna fa ya'ya amanar Allah ne agaremu kada muci Amana"

Kande ta dago da bakinta ja hakanan hakoranta alama dai taci goro tace "kaga matsiyacin banza kayimin shiru ko intashi in zaneka"

Dayake yasan halinta kuma zata iyane yace "Allah yabaki hakuri kuma akara duba maganata"yabar wajen.

Itako tanata juya shayi ko kwah agefenta dakuma burodi tana murmushin mugunta sai kuma tace
"ka isa ka hanani cin dadinnan ne? Wallahi baka isa ba, kana bani ne? banza irinka talaka kawai matsiyaci to ni saidai kayi akan kudi ba abinda bazanyiba"

Naklat dake daki  tana danna wayarta dakuma jinjina son kudi irin na mamanta.

Dunduuut taji alamar sako yashigo ta duba taga a WhatsApp nata ne aka turo sakon sabuwar number tagani yacd mata "Slm"

Bata 6ata lokaci ba tace
 "wslm"
nan yakuma turowa
"ykk naki beb?"
tace "kalau nake wanene?"
yace "Wani bawan Allah ne me kaunarki"
tace "kauna kuma? to waya fada maka sunana?"
yace "canka nayi kuma ai naci ko?"
tace "nice naki beb amma da mamaki kodai dan harka ne nabashi layi na manta? "
yace "ni na kwarai ne aurenki nakeso nayi kuma"
nan tarike wajen Voice note nata tafara magana kamar haka:

"Kaga Malam nifa karuwa ce in kasan harka ne tafiyarka to bismillah inkuma    bashi bane nikam ba aure zanyi ba sai na kwale duniya na moreta"

Baifi minti daya ba shima yamayar mata kamar haka:

"Wallahi inasane ke karuwace amma naji nagani zan aureki kada kicuci kanki ga dama tazo miki wanda zai aureki kuma yana sane da halinki"
tagama ji game da jinjina dadin muryar wannan gayen bata bashi amsa ba tarufe datarta ta kwanta tama nazarta abin.
Ummanta ko tana gama kari tamike ta tafi kasuwa siyan zani,takalmi,da mayafi dakuma kayan abinci dana kwalam.

        **ASALINSU***
Malam Auwalu mutum ne me kima da daraja ga iimi Asalinshi dan garin Kaduna cikakken Bahaushe zanada auren kande aurensu na hadi ne, aikinshi ne yadawo nan garin Biu yana aikin soja ne,Basu ta6a samun haihuwa ba zamansu kuma na lafiya ne da karrama juna.
Bayan shekara biyu Allah ya azurtasu da Haihuwar ya' mace taci suna Naklat inda wata makociyarsu a barrack din take ce mata naki beb,yarinya ta taso cikin gata da kwanciyar hankali da tarbiyya don a lokacin Malam Auwalu yanaji da nairarsa.

Yarinyar na kaiwa shekara goma sha biyar labari ya sauya domin kudin malam Auwalu yagama karewa tas wulakanci awurin Kande sai wanda ba'a saniba kullum saita wulakantashi watarana ma har duka niko WALIDATION nace kaji wawan tsohon soja.


*SHARE PLS*
*COMMENT*

Post a Comment

0 Comments