π»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈ
*SUHAIMA* ( *Yar* *sarki* *ce* )
π»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈ
*NA*
*Shafa'atu* *Muhammad*
( *Beauty* *beby* )
*ZAMANI* *WREITER'S* *ASSOCIATION*π€
_____________________________________
We are here to educate motivate entertain our readers
_____________________________________
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*A gaskya ina jindadi Comments dinku my Pan's bani da abin da zance muku Allah ya barmu tare much love u sosai dinna** π₯°
*A* *LOKACIN* *DA* *MALA'IKAN* *MUTUWA* *YAZO* *DOMIN* *KARB'AR* *RAN* *ANNABIN* *RAHAMA* *SAI* *YAJI* *ZAFI* *KWARAI* *YA* *TAMBAYI* *MALA'IKAN* *MUTUWA* *YACE* , " *DAMA* *HAKA* *AKE* *JIN* *ZAFI* *YAYIN* *FITAR* *RAI* *ALLAH* *YASA* *MUDACE* . *AMIN* π *BARKAMU* *DA* *SAFIYAR* *JUMA'A* *YAN* *UWANA*
*BISMILLAHI* *RAHAMANI* *RAHIM*
π
Ώ*7* & *8*
Albarka ta dinga samishi tace dashi bikin bazai wace nan da wata daya ba, ba komai Garba yace ya koma ya kwanta.
Innaro ta fita daga dakin domin ta kimtsa taje ta sanar da qanwar ta ta, tana isa gidan ta zayyane mata komai murna ce ta cikata. Ta dinga yiwa yayar tata godiya.
Rana bata qarya sai dai uwar diya taji kunya, haka masu karin magana ke cewaπ a yaune ake daura auren lami da Garba bakin innaro har kunne Dan murna saboda burinta ya kusa cika.
Da daddare aka shirya amarya lami aka kaita gidan mijinta, inda acikin gidan ya gyara wani guri inda zai zauna da iyalinsa.
Tun bayan biki da sati uku lami ta fara nunawa Garba halinta marasa kyau ko sau daya innaro bata taba yiwa lami fada ba.
I dan ma Garba yakai qarar ta sai innaro ta daura laifi akansa tun daga lokacin ya daina gaya mata komai nasa.
A haka lami ta sami ciki ta haifi danta namiji kamarsu daya da ita inda yaro yace suna Abdullahi..bayan shekara daya ta koma haifar diya mace mai suna Rabi'atu (Rabi). Sai kuma bayan shekara daya da wata tara ta haifi yarinyar ta mai suna Balkisu (Balki).kaf dukiyar Garba lami ta kwashe ta bawa innaro Ita, adalilin haka, Garba ya dawo matsiyaci.tun daga wanna lokaci Innaro ta sauyawa Garba masifar yau da ban ta gobe da ban.
Haka ake rayuwa gidan Malam Garba cikin qunci sai ya fita yayi faskare inyasamu yan kudi sannan yayi cefane yakawo gidan.
Randa kuwa ba'a samu ba sam babu zaman lafiya a gidan.
Tunda Garba yaga tsantsar halin Innaro da lami shine ya samu wata yarinya mai hankali a layinsu ya aura wato Asma'u Ma'u, shekara Ma'u daya a gidan lami ta haifi er ta inda tasaka mata sunan Innaro wato Hajara, (tunda Ma'u tazo gidan bata samun kwanciyar hankali lami da yaranta suyi mata rashin mutunci Innaro ma tayi mata, sai Malam Garba yana gida take samun kwanciyar hankali a gidan.
*Cigaban Labarin*
A haka rayuwa tacigaba da gudana a gidan Malam Garba, inda yanzu Suhaima take maida hankali a karatun ta, Dan takusa hadda ce izu goma, bangaren boko kuwa yanzu tana aji biyu saboda tanada kokari sosai Ma'u kuwa gwargwadon tana farantawa yarinyar tata rai, duk abinda takeso tana bata.
Wata rana SUHAIMA ta fita tsakar gida yin wanke2 sai ga Balki ta fito daga bayan gida, wani wawan mari ta dauketa da shi "ke shegiya Uban waye yace ki taba kayan masu Uba har huci takeyi saboda facin rai.
Da gudu Suhaima ta koma daki domin taji marin har Cikin ranta tana shiga ta fada kan ciyar Ummar ta kuka take kamar ranta zai fita Umma(Ma'u) ce take tambayar ta Mamana ke dawa tana shasheqa ta fada mata ummana ba Balki bace ta dukeni wai karna qara taba kayan masu Uba wai ni shegiya ce.
Daina kuka yarinyata keba shegiya bace ba domin nice na haifeki Malam kuma shine Baban ki yawwa Umma ta daman nasan Balki ba gsky ta keyiba rungume ta Umma ta tayi aranta kuwa cewa tayi oh ni naga ta kaina a ce wannan yarinyar karama da ita Balki ke cewa shegiya meta sani Allah ya kyauta. Juyowar da zatayi taga Suhaima har tayi bacci, kwantar da ita tayi ta fita tsakar gida domin qarasa wanke2 Sallama taji ana dokawa ta amsa shigowar da za'ayi tayi tozali da fuskar lami wata uwar harara ta doka mata da bakaken maganganu Balki ce ta fito daga uwar daki domin jin hayaniyar da akeyi a tsakar, gida fitowar ta keda wuya ta amshe da....yo ai ita ma idan aka bibiya ita ma shegiyar ce bata rufe baki ba taji mari a fuskar ta kafin ta dago taji an qarayi mata wani hagu da dama. Dagowa tayi da zummar ganin waye ya mareta sai taga....babanta "wlh kika qara zagin matata sai nayi miki dukan da babu Wanda ya taba yimiki shi. kai Malam akan wannan shegiyar matar taka ka dakar min y'a wlh yau sai anyi ta a gidannan.
Wucewa tayi fuuu sai a bangaren Innaro taja burki, kwashe labari tayi ta fadawa Innaro ai kuwa kamar ana tsungurar ta tace muje naci Ubansu su duka fita sukayi tsakar gida amma me sai sukaga babu kowa a gurin Balki ce tace da lami kina barin gurin nan suka shige daki suka kulle. Ashar suka dinga yi, sannan daga bisani da sukaga sun gaji shine kowa ya tafi dakin sa.
Akwana a tashi babu wuya gurin Allah SUHAIMA ta sauke Alqur'ani sannan tasan littafai da dama a bangaren hadda kuwa tana da Izu hamsin akanta, a boko kuwa tana ajin qarshe na garamar sakan dare wato aji Uku, kyawun ta sai fitowa yakeyi inda a yanzu SUHAIMA tana da shekara goma sha shida kuma a yaune Innaro ta bujuro da alqwarin da sukai lokacin da aka kawo SUHAIMA gidan inda ta fito tsakar gida tana ta banbami, ita ala dole sai SUHAIMA ta bar gidan a yau ba gobe ba wannan maganar ta tayar wa Ma'u da Malam Garba hankali ba qaramin kidime wa sukayi ba.. Da kyar ya bata hakuri cewa ta bari zuwa wani lokaci.
Sallamar SUHAIMA ce ta ankarar da su juyowa sukai gaba daya suna kallon ta, wani tsawa lami ta daka mata ke shegiya garama kidaina wannan farin cikin da kikeyi domin kuwa kin kusa barin gidannan, ko kulasu batayi ba ta shige daki domin inda sabo ta saba jin wannan bakaken kalaman daga bakin su.
(Allah yarabamu da bakin hali Irina Lami da Innaro Amin)
Vote and share
Comments
*Mmn beby ce* π₯°
0 Comments