π»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈ
SUHAIMA (Yar Sarki ce )πΈπ»
π»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈ
*NA*
*Shafa'atu Muhammad*
( *Beauty Beby*)
*Yar Mutan Kebbi* π³π¬
*ZAMANI* *WREITER'S* *ASSOCIATION* π€
___________________________________
We are here to educate motivate entertain our readers
_____________________________________
**Gajeran* *Labari* *ne**
FARST ' JUNARY ' 2020
*BISMILLAHI* *RAHAMANI* *RAHIM*
1&2
Kuka naji yana tashi a gefen in da nakeyin ciyayi domin nasaida nasamu abinda zanci da iyalina, kasa kunne nayi da kyau najiyo kukan jariri, babu musu na isa inda kukan nan ke tashi, da isata na hango wani kwali wanda acikinsa kukan ke tashi da sassarfa na isa wurin, bude kwalin ke da wuya na hango wata kyakkyawar jiririya fara mai hanci gata da yalwa tacen gashi kayan jikinta kuwa kana gani kasan na yaran masu hannu da shunine addu'a nayi na dauke ta, gida na wuce da ita domin samar mata maganin kukanta, da isata gida na wuce dakin Asma'u amarya ta, da sallama na shiga na same ta a bakin gado tana kuka, dago idan da zatayi tayi tozali da jaririyar da take hannuna da sauri tazo kusa dani ta karbi yarinyar ta bata ruwa tana gama sha ta jijjigata tayi barci ta kwantar da ita akan gado, " Malam aina ka samo wannan jaririya haka Ma'u ce take tambayar shi cike da mamaki, kwashe labari yayi kaf ya fada mata, hawaye ya gani yana bin fuskarta cike da tausayi ya matso ya share mata " ki daina kuka haka yau Allah ya amshi addu'arki Ma'u, wannan yarinya insha Allahu sai ta zama abin alfahari agaremu.
"Insha Allahu Malam nayi maka alkawarin cewa zan riketa amana kamar Yar da na haifa aciki na.
Allah yayi miki albarka Asma'u Amin tace, cike da murmushi a fuskarta in da sabo ta saba shan addu'a a gurin mijin nata, " Malam wani han zari ba gudu ba kana ganin kuwa cikin gidan nan zasu yadda kuwa,"ki daina fadin haka zanyi musu bayani yadda zasu gane tau Ma'u tace takoma kusa da yarinyar, kosuwa suka miki haka Allah zai saka miki"Amin Malam yace ya fita, kallon yarinyar take cike da so da kaunar ta.
Tashi tayi ta fara gyaran daki, fitar Malam ke da wuya yayi kicibis da lami a kofar dakin Ma'u, "to annamimi munafuki kaje ka dauko shegiyar yarinya a bola to wallahi tun wuri ka maida ta gurin karuwar uwarta, dan bazan yadda cewa tsintota kayi ba, banza kawai daga hannu yayi da niyar marinta sai ya fasa, wani mahaukacin ashar ta zunduma masa da ka mareni mana wlh da ka gane kuranka, banza wanda baya iya ciyar da iyalansa sai yayi ciyawa ya siyar." Fita yayi domin bazai iya cigaba da jin munanan kalaman ta ba, ke kuma munafuka zaki fitone wlh na tsaneki shegiya mayya kin mallakemin miji, kuma wannan shegiyar yarinya bazata rayu a gidannan ba lami ce take fadar munanan kalamai ga Ma'u.
wucewa tayi ta shige daki gurin yaranta domin kitsamusu labarin da ta jiyo a cikin gidanna su, kwashe labari tayi kaf ta fada musu Rabi ce da Balki suka zunduma wata ashar "wlh ba'a isa akawo mana shegiya cikin gida ba, yanzu kuwa zamuje mu fadawa innaro ta dauki mataki a kai.
Da shigar su bangare innaro suka fada mata karya da gaskiya aikuwa ta hau ta zauna, tace " kubarni da shi sai na dauki mataki wlh a gidanna ne za'a kawoma shegiya, bara ya shigo gidan sai ya maida ita in da ya daukota.
Fitar Malam keda wuya ya wuce gurin Malam musa abokinsa ya fada mishi komai abinda ya faru shawarwari masu kyau ya bashi tare da nasihohi masushiga jiki sannan ya bashi hankurin rashin mutuncin da lami take masa, godiya yayi masa sannan ya koma gida.
Yana shiga lami ta galla masa wata uwar harara tace "kaje Innaro tana kiranka, bangaran ta ya nufa, Sallama yayi ya samu guri ya zauna, Innaro sannu da gida ya rana, mtsww "ban sani ba Innaro ce ke magana rai 6ace, inda sabo ya saba rashin amsa gaisuwarta, to naji abinda ya faru Garba wlh tun wuri ka maida ita gurin uwarta karka sake shegiyar yarinyar nan ta kwana a gidannan..✍
(Tirkashi fan's Innaro kuwa zata bari jaririyar na ta rayu a gidanna kuwu, ku biyoni dan jin yada wanna labarin zai kasance)
*Kadan* *kenan* *daga* *cikin* *labarin* *tsaraban* *sabuwan* *shekara* .
***Mmn Beby Ce***π₯°
0 Comments