π»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈ
π»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈ
*SUHAIMA* ( *Yar* *sarki* *ce* )
π»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈ
π»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈ
*NA*
*Shafa'atu* *Muhammad*
( *Beauty* *Beby*)
*Yar* *Mutan* *Kebbi* π³π¬
*ZAMANI* *WREITER'S* *ASSOCIATION* π€
________________________________________
We are here to educate motivate entertain our readers
___________________________________________
*2* / *1* / *2020*
I *na matukar godiya agareku my pan's da irin addu'o'in da kuke min bani da abinda zance muku face ina matukar kaunarku nima har cikin raina nima ina yinku irin sosai dinna wanna PJ nakune group na SUHAIMA (Yar sarki ce) kuyi ya da kuke so da shi* π₯°
Z *akujini kwana biyu banyi typ ba kumin uzuri muna bikine na sister's dina ina barar addu'arku a gare su my Pan's insha Allah zancigaba bayan bikin** π
*MANZON* *ALLAH* ( *S.A.W* ) *YA* *NACEWA* *KA* *TUNATAR* *DOMIN* *TUNATARWA* *TANA* *AMPANIN* *MUMINAI* , *ZAUNA* *DA* *JAMA'A* *LAFIYA* *DOMIN* *WATARANA* *SUNE* *ZASUYI* *RAKIYARKA* *IZUWA* *MAQABARTA* , *DAURE* *KARIKE* *SALLAH* *AKAN* *LOKACI* *DOMIN* *WATARANA* *ZATA* *TAYAKA* *KWANCIYAR* *QABARI* , *ALLAH* *YASA* *MUDACE* *AMEEN* π
*BISMILLAHI* *RAHAMANI* *RAHIM*
*5* & *6*
Ana isa asibiti aka wuce dasu emergency aka basu taimakon gagawa.. Aka ware matattu aka sakasu a mutuware, Allah sarki duniya sai dai muce Allah yajikan wadanda muka rasa ciki kuwa harda Malam, Suleiman, duniya kenan. A can bangaren masu rauni na hango abokin Malam Suleiman Ashe dama shi bai mutuba, ikon Allah kenan, kwanan sa daya yace a Sallame shi domin akwai dan uwansa a cikin matattu Dan haka zaije ya kai gawarsa gida a sallace shi..babu bata lokaci aka sallameshi ya wuce da gawar abokinsa garunsu.
A can bangaren iyalan Malam Suleiman kuwa Khadija da d'anta sun damu sosai inda Hajara kuwa ko ajikinta, dan har gidan abokin Malam Suleiman taje akace mata basu dawoba, ai kuwa tana shirin fita domin takoma gidanna abokin mijinta tayi kicibus da shi a cikin gida tare da wasu mutane."sannan ku da zuwa Khadija ce take magana cike da damuwa a fuskarta " yawwa Khadija ya gida, cewar abokin Mijin nata..
Yawwa ina uwargidan taki take ne??hmmm sai dai a duba dakin na ta ko tana nan.juyawar da zatayi sai gata nan ta taho.
Nasiha yayi musu mai ratsa zuciya inda ya basu hakuri sosai akan duk abinda ya sameka, sannan daga bisani ya fada musu cewar mijinsu ya rasu da abinda ya faru da su.
Tun kafin ya gama Khadija ta zube a gurin ta dinga kuka maitsuma zuciyar mai sauraro.
Da kyar aka bata hakuri tayi shiru, Hajara kuwa cewa tayi aranta shi kenan yanzu zanyi yadda nakeso a gidannan Dan wlh sai zaman gidannan ya gagareki ke da d'anki..a filikuwa kuka take hadda majina tana cewa shikenan gatana ya qare Malam ya tafi ya barni..hakuri aka bata tayi shuru sannan aka kaishi makwancin shi Allah sarki duniya.
Tun daga wannan rana Hajara ta takurawa Khadija da d'anta bata da sukuni ko kadan inba abokin Malam Suleiman ne yazo ba, shi ka dai ne yake taka mata burki takeji. Abinci da zasucima gagarar su yakeyi inba shine ya kawoba.
A haka rayuwa taci gaba da tafiya a gidan Malam Suleiman inda a halin yanzu Garba yana da shekara 26 Khadija kuwa kullum babu lafiya Garba yarasa yadda zaiyi ga shi babu abinci ga rashin kudi Ballan tana ya kaita asibiti.
Yau ta kama ranar Alhamis cikin dare Khadija ta dinga aman jini kafin gari ya waye Allah ya karbi abinda. (Allah sarki dukan mai rai mamacene Allah yasa mucika da kyau da imani Amin)
Garba ba Uwa ba Uba sai dai muce Allah ya jikan Khadija yakai rahama kabarinta.π
Da safe kuwa aka shirya ta aka kaita makwancin ta, Garba yasha kuka kamar karamin yaro.
Hajara kuwa murna ce cikin ranta yanzu burinta ya fara cika saura Garba shima ya mutu ta gaje dukiyar gaba daya,(Dama kafin Malam Suleiman ya mutu ya hada kaf dukiyar sa ya bawa Khadija sai wadda tayi saura a gurin abokinsa) da wannan farin ciki Hajara ta kwana a ranar, bayan mutuwar Khadija da kwana arba'in abokin Malam Suleiman yazo da maigari akan raba dukiya, inda Garba ya samu kaso mai tsoka..
Hajara kuwa kamar ta hadiya zuciya ta mutu dan bakin ciki.
Tun daga wannan rana Hajara (Innaro) take tarairayar Garba kamar d'anta na cikin ta.. Samun Garba tayi a dakin sa yanata tunani da Sallama ta Shiga, kai Garba meyasa meka kake kuka, la babu komai Innaro me kika gani, hawaye nagani a idonka.. kadai na kuka haka sannan ka cire damuwa "dama akwai maganar da nazo muyi da kai, " to Innaro inajinki cewar Garba dayake gyara zaman sa.
"Ya kamata ace kayi aure Garba da zama haka da kake yi " toh Innaro wacece zata soni bayan bana zuwa gurin kowace mace a garinna.
Hamdala Innaro tayi aranta tace faduwa tazo dai2 da zama a fili kuwa haka tace karka damu akwai yar qanwata na yaba da hankalinta sunan ta lami itama bata kula kowa cewar Innaro.
Garba dai shuru yayi domin bai San mezai ce mata ba sannan kuma bazai iya bijirewa maganarta ba.
Dago kansa yayi yace babu komai Innaro na amince da maganarki kije kiyi duk abinda ya dace ayi.(zo kuga murna gurin Innaro burinta ya cika Allah yarabamu da irin masu halin Innaro Amin)
Veto and share
Comment
*Mmn Beby ce* π₯°
0 Comments