♥♥♥♥♥♥
♥♥♥♥
*LAURATU*
_(Love story)_
Story and written by
~Mrs H3RB33B~
*wattpad - Meerahman*
*©2019*
DEDICATED TO MY MENTOR
~BINTA UMAR ABBALE~
~Sadau'karwa ga~
*HASSAN 90k*
*HUSSAIN 80k*
_YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI, MAI KOWA MAI KOMAI,ALLAH KABANI IKON RUBUTA DAI-DAI KURA KURAN CIKI KUMA ALLAH KA YAFEMIN ALLAH KASA YADDA NA FARA LAFIYA KABANI IKON GAMAWA LAFIYA._
~ABUJA~
Maitama street
Motacine guda goma masu tsadar gaske suke tafiya ahankali, basuyi wata tafiya mai nisa ba naga sun nufi wani tamfatsetsen gida suna isa bakin gate d'in mai tu'ka motar farko yayi hon, nan take mai gadi ya wangale gate d'in, nan motocin suka shiga d'aya bayan d'aya.
Murfin motan nafarko naga anbud'e wow! Masha Allah abinda na iya furtawa kenan lokacin danayi tozali da wasu kyawawan mata su biyu kana ganinsu kaga shuwa arab sunyi shiga irin na matan maiduguri, sunsha kwalliya ta alfarma kana ganinsu kasan naira ta zauna sosai a jikinsu.
Sauran motocin ne naga suma sun firfito amma mazane, nan da nan suka fara sauke akwatuna da alama dai na aure ne. To fa readers tun Ina 'kirgawa dai harna daina sun kusa 15mins kafin suka gama, akwatine na gani na fad'a, Akwatuna set biyar naga an jerasu ras, pink, purple, white, green, and golden.
Nan mazan nan suka nufi cikin gidan da akwatuna nan, cikin wani 'katon falo naga sun nufa aka fara jerasu nan cikin falon naga manyan mata sunkai su biyar kowacce cikinsu tayi shigar alfarma.
Mata biyun nan ne naga sunshigo cikin parlorn nan suna tafiya cikin isa da 'kasaita.
Bayan an basu wajen zamane cikin 'kan'kanin lokaci aka cikasu da kayan motsa baki, sosai anyimusu tarba ta karramawa nan dai suka gabatar da akwatunan dasuka kawo,sun yaba da kayan sossai yayin da dangin amarya suka bayarda 20mil wa dangin ango kud'in ganin kaya, Dazasu tafima aka cikasu da dangin su snacks drinks dadai sauran tarkace.
Laurat gaskiya kina da sakaci sai yaushe ne zakiyi hankali ne, ace Auren ki remain 3 weeks amma bazaki dena bin maza ba and now kina min maganar azubar miki da ciki gaskiya bazai yuwuba.
Nan take Laurat taciro masa bunch na 'yan 1 thousand guda goma ta jera masa kan table d'in dayake gabansa, ai nan take ya saki murmushi yace,"Angama big girl ko yanxu kike so za'ayi aiki,"
Laurat ta kalleshi da manyan idanuwanta up and down kafin tace masa,"Next tomorrow by 8:00am nakeso agama komai and idan naji labari ya fito kasan mezan aikata."
"Angama big girl yafad'a yana kwashe kud'in."
Knocking aketayi ba 'ka'k'kautawa yaja siririn tsaki kafin yace,"Come in."
Cikin cool voice d'insa
Wani matashi ne kyakkyawa ya shigo tare da rufe 'kofar tun kafin ya zauna yafara cewa,"Wannan ai iskanci ne kanajina kayi biris dani wallah nima saina fita harkarka tunda baka da mutunci, Ai ba aurena bane sai wahala nakesha amma ba sannu ba madalla enough please ya furta tare da juyowa subhanallah!!! Na furta lokacin da nayi tozali da kyakkyawar doguwar fuskarsa wadda ta wadatu da saje ga eyes balls d'insa manya farare tas amma wajen ba'kin blue ne, yanada dogon hanci ga 'karamin pink lips d'insa, ga kwanceccen gashin girarsa kamar wadda aka zanashi yayi kyau da fuskarsa, sai gashin kansa dayasha gyara sossai sai 'kamshi yakeyi.
Black suit ne ajikinsa ga hannun sa na hagu yasha zoben azurfa and right hand d'insa yasha agogon rolex kana ganinsa kaga asalin bafulatani wow yayi kyau sosai kamar my Habeeb d'ina lols.
Yacigaba da magana cikin golden voice d'insa Naseer kacika fitina wallahi, yanxu dan kamin hidima shine sai kayi shela kowa yaji gaskiya zan canza aboki ya 'karasa cikin shagwab'a.
Naseer yace,"So wat inka canzani, d'an iska kawai Albarkacin Mamy kaci da tuntuni nafita sha'anin aurenka."
Phone d'in ASAD ne ya fara ringing ganin mai kiransa ne yasashi yin wani tsadadden murmushi, d'aga kansa yayi ya kalli Naseer kafin yace,"My wife tana kirana d'an bani waje please."
Naseer sake baki da hanci yayi yana kallonsa kafin cikin masifa yace............
Inajiran comment🤪
*Like*
*Vote*
*Share*
*Comment*
~Mrs H3RB33B~ 😘
1 Comments
https://mynovels.com.ng/littafan-hausa-novel/
ReplyDelete